ukarofi

12641 Posts
Sabuwar dokar zaɓe: Majalisa ta tabbatar da ’yancin kuɗi ga INEC

Sabuwar dokar zaɓe: Majalisa ta tabbatar da ’yancin kuɗi ga INEC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dokokin ƙasa ta ƙaddamar da gagarumin sauyi a tsarin zaɓen Nijeriya bayan amincewa da sabuwar Dokar Zaɓe ta 2026, wadda ta tanadi ɗaurin shekara biyu ba tare da zaɓin tara ba ga duk wani Kwamishinan Zaɓe na Jiha (REC) da ya ƙi fitar da muhimman takardun zaɓe, tare da kafa asusun musamman domin tabbatar da cikakken ’yancin kuɗi ga INEC gabanin babban zaɓen 2027. Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ne ya bayyana muhimman tanade-tanaden dokar a Abuja, yana mai cewa an kwashe kusan shekaru biyu ana nazari da tattaunawa kafin a cimma…
Read More
Shugaban ƙaramar hukumar Bayo ya yaba wa Gwamna Zulum kan cigaban da ya samar a Borno

Shugaban ƙaramar hukumar Bayo ya yaba wa Gwamna Zulum kan cigaban da ya samar a Borno

Daga GAMBO ISA a Abuja Shugaban ƙaramar hukumar Bayo, Usman Balbaya Maidoki, ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, bisa jajircewarsa wajen kawo ci gaba da kuma tafiyar da gwamnati mai bai wa kowa dama a faɗin jihar. A cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a Abuja kuma aka bai wa jaridar Blueprint Manhaja, Hon. Usman Balbaya Maidoki ya bayyana muhimman nasarorin da gwamnan ya samu a fannoni da suka haɗa da bunƙasa jarin ɗan Adam, noma da kiwo, ilimi, kiwon lafiya, tsaro da kuma samar da kayayyakin more rayuwa.Shugaban ƙaramar Hukumar ya yaba…
Read More
An ci tarar Chelsea da West Ham kan hatsaniya tsakanin ’yan wasa

An ci tarar Chelsea da West Ham kan hatsaniya tsakanin ’yan wasa

An ci tarar Chelsea fam 325,000 da kuma West Ham fam 300,000, sakamakon wani rikici da ya ɓarke tsakanin ’yan wasa karawar da suka yi a Premier League a watan Janairu a Stamford Bridge. Lamarin ya faru ne a minti 95, inda ɗan wasan Chelsea, Joao Pedro ya ƙalubalanci Adama Traore na West Ham, saboda ture Marc Cucurella da ya yi. Bayan da aka duba VAR, sai alƙalin wasa Anthony Taylor ya bai wa Jean-Clair Todibo jan kati kai tsaye saboda shake wuyan Joao Pedro da ya yi. Hukumar ƙwallon ƙafa ta Ingila ta bayyana cewa Chelsea da West Ham…
Read More
Hakimi zai fuskanci shari’a saboda zargin fyaɗe

Hakimi zai fuskanci shari’a saboda zargin fyaɗe

Mai tsaron bayan Paris St-Germain, Achraf Hakimi ya ce zai fuskanci shari'a, bayan da wata mata ta zarge shi da yi mata fyaɗe. Matar ta zargi kyaftin ɗin Morocco da yi mata fyaɗe a gidansa da ke babban birnin Faransa a shekarar 2023, lokacin tana da shekaru 24. Sai dai ya musanta zargin. Ofishin mai gabatar da kara na Nanterre a yammacin birnin Paris, ya fara bincike a karon farko a watan Maris a 2023. “A wannan lokacin zargin fyaɗe kawai ya isa a kai mutum gaban kotu,” inji Hakimi a shafinsa na ɗ. “Wannan ba adalci ba ne ga…
Read More
Barcelona ta karɓe teburin La Liga daga hannun Real Madrid

Barcelona ta karɓe teburin La Liga daga hannun Real Madrid

Barcelona ta koma matakin farko a kan teburin La Liga, bayan doke Levente 3-0 a wasan mako na 25 da suka buga ranar Lahadi. Kungiyar Camp Nou ta ci ƙwallayen ta hannun Marc Bernal da De Jong da kuma Fermin Lopez. Da wannan sakamakon Barcelona tana ta ɗaya a kan teburi da maki 60, sai Real Madrid ta biyu da tazarar maki ɗaya tsakani. Real Madrid ta ci karo da komabaya, sakamakon da ta yi rashin nasara 2-1 a gidan Osasuna ranar Asabar. Ranar Laraba, Real Madrid za ta karɓi baƙuncin Benfica a wasa na biyu a neman cike gurbin…
Read More
Serie A na fuskantar tarihi mafi muni a gasar Zakarun Turai

Serie A na fuskantar tarihi mafi muni a gasar Zakarun Turai

Kungiyoyin ƙwallon ƙafar Italiya na cikin wani yanayi mai matuƙar muni a gasar Champions League, inda akwai yiwuwar babu ko ɗaya daga Serie A da za ta kai zagayen na biyu wato na ’yan 16 a bana. Tun bayan dawo da tsarin zagayen ’yan 16 a kakar 2003-04, a ko da yaushe akwai aƙalla wakili guda daga Italiya. A lokuta 12 cikin shekaru 22 da suka wuce ma har ƙungiya uku ne suka kai wa wannan mataki. Ba a taɓa samun kakar da babu ko ɗaya ba daga mai buga Serie A tun 1987-88, lokacin da Napoli ta fita a…
Read More
Daraktan hukumar samar da ruwan sha a Katsina, Injiya Tingilin ya rasu

Daraktan hukumar samar da ruwan sha a Katsina, Injiya Tingilin ya rasu

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Injiniya Tukur Tingilin Malumfashi, ya rasu sakamakon mummunar hatsarin mota a tsakanin mararrabar Musawa zuwa Musawa a Alhamis da ta wuce. Mutane da dama sun bayyana marigayi Tukur Tingilin a matsayin mutum mai kirki, mai sauƙin kai da kyakkyawar mu’amala. Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa, ya bayyana matuƙar alhini da jimaminsa kan rasuwar daraktan hukumar. A cikin wata sanarwar ta’aziyya da babban sakataren yaɗa labarai na gwamna, Ibrahim Kaula Mohammad, ya fitar, gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga jihar, musamman a daidai lokacin da gwamnati ke ƙara ƙaimi wajen inganta samar…
Read More
Ma’aikatar al’amuran addini a Yobe na bibiyar ciyarwar watan Ramadan

Ma’aikatar al’amuran addini a Yobe na bibiyar ciyarwar watan Ramadan

Daga MUHAMMAD AL-AMIN, Damaturu Tun a farkon watan Ramadan ne Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, ya amince da kashe kimanin Naira miliyan 398 a shirin ciyarwa a watan Ramadan na wannan shekara ta 2026, tare da tallafa wa tafsirin da malamai ke gudanarwa a faɗin jihar. Yayin da yake ƙaddamar da shirin ciyarwa, Kwamishina a ma'aikatar al'ammuran addini da ɗa'a da wayar da kan jama'a, Alhaji Yusuf Umar, ya yaba wa Gwamna Buni da ci gaba da faɗaɗa shirin. Haka kuma, Kwamishinan ya bayyana shirin a matsayin yar manuniya dangane da sadaukarwar gwamnati wajen kula da jin daɗin…
Read More
Ba mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba – Gwamnatin Nijeriya

Ba mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba – Gwamnatin Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa ba ta taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba ko nuna wariyar addini ba, bayan rahoton bincike kan zargin muzgunawa da kashe Kiristoci da Majalisar Wakilan Amurka ta fitar. Gwamnatin ta ce "duk da ƙalubalen tsaro da wasu yankuna ke fuskanta, matsalolin sun samo asali ne daga ta’addanci da fashi da makami, da rikice-rikicen al’umma." Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanadi ‘yancin addini…
Read More
Kotu ta ɗage shari’ar El-Rufai zuwa watan Afrilu

Kotu ta ɗage shari’ar El-Rufai zuwa watan Afrilu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Mai bai wa tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa kotu ta ɗage shari’ar da ake yi da tsohon gwamnan zuwa ranar 23 ga Afrilu, 2026, bayan da aka kasa gabatar da shi a gaban babban kotun tarayya da ke Abuja. Sanarwar da ya fitar ya ce mai gabatar da ƙara ya buƙaci kotu ta ba da wa’adin makonni biyu domin bai wa jami’an DSS damar gabatar da El-Rufai wanda ke hannu hukumar ICPC. Sai dai lauyan El-Rufai, Wole Iyamu, ya shaida wa kotu cewa babu…
Read More