27
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS ta sanar da cafke wani mutum da ake zargi yana da hannu a harin da aka kai cocin Katolika na St. Francis da ke Owo a Jihar Edo a shekarar 2022. Mutumin nan bayan nan wanda aka bayyana da suna Sani Yusuf, shi ne cikon na shida da ake zargi da kitsa harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar fiye da masu ibada 40 tare da jikkata wasu da dama. Tuni dai hukumar DSS ta riga ta kama mutum biyar waɗanda suke fuskantar shari’ar aikata laifukan ta’addanci. Gidan Talabijin…
