27
Feb
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jakadan ƙasar Saudiyya a Nijeriya, Yousef Albalawi, ya sanar da cewa kamfanin jiragen sama na Saudiyya zai dawo da zirga-zirga kai tsaye daga Jiddah zuwa Abuja nan da watan Yuni ko kuma a watan Janairun 2027. Jakadan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, a Abuja. A cewarsa, ziyarar na da nufin ƙara danƙon alaƙa tsakanin Saudiyya da Nijeriya tare da faɗaɗa damar haɗin gwiwa a fannoni daban-daban, musamman tattalin arziki, siyasa da tsaro. Albalawi ya jaddada cewa Saudiyya…
