ukarofi

12641 Posts
Gwamnatin Kano ta sanar da ranar hutun Azumin Ramadan da ƙaramar Sallah

Gwamnatin Kano ta sanar da ranar hutun Azumin Ramadan da ƙaramar Sallah

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da ranar fara hutun Azumin Ramadan da na ƙaramar sallah ga dukkanin makarantun firamare da sakandare na gwamnati da masu zaman kansu a faɗin jihar. Sanarwar ta bayyana cewa, kamar yadda yake ƙunshe a cikin jadawalin shekarar karatu ta 2025/2026 da aka amince da shi, za a fara hutun ne a ranar Asabar 1 ga Maris, 2026, ga dukkan ɗalibai masu kwana a makaranta da na rana. An kuma buƙaci iyaye da masu kula da ɗaliban da ke makarantun kwana da su je su ɗauki ‘ya’yansu tun da safiyar Juma’a…
Read More
Gwamnatin Kano ta ƙaryata rahoton Amnesty International

Gwamnatin Kano ta ƙaryata rahoton Amnesty International

Daga RABIU SANUSI Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da zarge-zargen da Amnesty International ta gabatar, inda ta bayyana su a matsayin marasa tushe masu yaudara da kuma kauce wa gaskiya. A cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ya fitar, gwamnatin ta mayar da martani ga rahoton mai taken “Kano: Escalating Repression Endangers Freedom of Expression,” wanda ya zargi gwamnatin da amfani da jami’an tsaro wajen kama ko takura wa masu sukar Gwamna Abba Kabir Yusuf. Sanarwar ta jaddada cewa gwamnatin Kano na da cikakken ƙuduri wajen kare haƙƙin ɗan Adam ciki…
Read More
Cin zarafin ɗan jarida: SSR na Gwamnan Kano ya nemi afuwar ‘yan jarida

Cin zarafin ɗan jarida: SSR na Gwamnan Kano ya nemi afuwar ‘yan jarida

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Jihar Kano tare da SSR na Gwamna Abdullahi Rogo sun bai wa ƴan jarida hakuri kan zargin cin mutuncin ɗaya daga cikin mambobinsu, bayan wani zaman sulhu da aka gudanar domin warware rikicin. Sulhun ya biyo bayan zaman da kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya, ya kira a ranar Laraba domin daidaita al’amuran da suka lalace tsakanin ɓangarorin. Taron ya samu halartar shugabannin ƙungiyar Kano Online Media Chapel ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Kwamared Abubakar Abdulƙadir Dangambo, da daraktocin ma’aikatar yaɗa labarai, tare da ɗan jarida kuma tsohon shugaban ƙungiyar ƴan jaridu…
Read More
Ramadan: Mambobin Gidan Alheri sun ci gajiyar tallafin abinci da kuɗi

Ramadan: Mambobin Gidan Alheri sun ci gajiyar tallafin abinci da kuɗi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Ƙungiyar sada zumunta ta Gidan Alheri, reshen Dangin Juna Afirka Initiative (DJAI), ta raba kayan abinci da tallafin kuɗi ga mambobinta da sauran mabuƙata a Jihar Gombe domin sauƙaƙa raɗaɗin rayuwa a watan Ramadan. Tallafin ya ƙunshi gero, sukari, buhunan shinkafa masu nauyin kilo 10, taliya (spaghetti) da kuma kuɗi naira 5000 ga kowanne daga cikin waɗanda suka amfana. Mai taimaka wa Gwamnan Jihar Gombe kan harkokin tsaro da hulɗa da jama’a, Yusuf Musa Danbayo, ya bayar da tallafin gero da sukari ga mambobi 20, yana mai cewa hakan na daga cikin ƙoƙarin ƙarfafa ayyukan…
Read More
Hausa babbar harshe ce da ke da rinjayen masu amfani da ita a Afrika – Sadar Musa

Hausa babbar harshe ce da ke da rinjayen masu amfani da ita a Afrika – Sadar Musa

"Shekaru shida na kwashe Ina aikin samar da baƙaƙen Hausa da lambobi" Daga AISHA ASAS Idan ana zancen baiwa ta rubutu,  ba na jin a faɗin Nijeriya akwai inda ya kai Arewa yawaitar marubuta da za a iya buga ƙirji a kira su da gwanaye, watakila namijin ƙoƙarin da suke yi ne ya haifar da wanzuwa da kuma raya yaren Hausa ga masu tasowa duk da irin horo da ruɗin da yaren Ingilishi ke yi a ƙwaƙwalensu. A cikin irin wannan ƙoƙari, aka samu wani matashi da ya yi kishin ƙirƙirar baƙaƙe da kuma lambobi da malam bahaushe zai buge…
Read More
Gwamnatin Kano ta buƙaci faɗakar da jama’a kan nasarorin gwamna a manyan makarantu

Gwamnatin Kano ta buƙaci faɗakar da jama’a kan nasarorin gwamna a manyan makarantu

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada buƙatar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar yaɗa labarai da jami’an hulɗa da jama’a na manyan makarantu domin inganta isar da sahihan bayanai game da manufofi da nasarorin gwamnati ga al’umma. Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa inda ya bayyana cewa taron ya mayar da hankali kan muhimman batutuwa guda biyu. Ya ce batu na farko shi ne ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ma’aikatar yaɗa labarai da sassan hulɗa da jama’a na manyan makarantu domin…
Read More
Fashewar bam ya lalata tirelar siminti a titin Gusau zuwa Funtua

Fashewar bam ya lalata tirelar siminti a titin Gusau zuwa Funtua

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tirelar mai ɗauke da siminti mallakin kamfanin siminti na BUA Sokoto ta taka wani abu mai fashewa da ake zargin 'yan ta'adda suka binne wani Improvised Explosion Device (IED) da harshen turanci a safiyar Laraba a kan babbar hanyar Gusau zuwa Funtua a Jihar Zamfara. Lamarin ya haifar da tsaiko na ɗan lokaci a zirga-zirgar ababen hawa. Wakilinmu ya ruwaito cewa fashewar ta faru ne a Unguwar Chida dake ƙarƙashin ƙaramar hukumar Tsafe, yayin da babbar motar ke tafiya daga Sakkwato zuwa Kaduna. Ana kyautata zaton 'yan ta'adda ne suka dasa wannan na'urar, wadda ta…
Read More
UNICEF da Gwamnatin Sokoto sun haɗu don haɓaka Ilimin yara a Kebbi, Sokoto da Zamfara

UNICEF da Gwamnatin Sokoto sun haɗu don haɓaka Ilimin yara a Kebbi, Sokoto da Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Sokoto Asusun kula da yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) tare da haɗin gwiwar hukumar bada ilimi bai ɗaya ta jihar Sokoto sun gudanar da wani taron tattaunawa na kwana biyu kan wayar da kan jama'a da kafofin watsa labarai don ƙarfafa Ilimin ƙananan yara a matakin farko (ECCE) da kuma haɓaka samun ingantaccen ilimi a Jihohin Sokoto, Kebbi, da Zamfara. A cikin saƙonsa babban ofishin kula da UNICEF, reshen Jihar Sokoto, Dr. Michael Juma ya ce, tattaunawar da kafofin watsa labarai an shiyar shi ne don wayar da kan jama'a kan manufofi, don cigaban ilimin…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyar rasuwar Bello Musa Ɗankano

Gwamna Raɗɗa ya yi ta’aziyar rasuwar Bello Musa Ɗankano

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana alhinin sa kan rasuwar fitaccen marubuci kuma tsohon ma’aikacin gwamnati, Bello Musa Ɗankano. Ɗankano, mai shekaru 71, ya rasu ne a ranar Lahadi a Katsina. A cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin ɗa na gari wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar jama’a da kuma bunƙasa adabi. “Bello Musa Ɗankano ba kawai marubuci ba ne; mai bayar da labari ne wanda ya yi amfani da adabi a matsayin hanyar bayyana gaskiya, darussa na ɗabi’a da sauyin al’umma. Rasuwarsa babban rashi ne…
Read More
Bin doka: Muhimmancinsa da tasirinsa wajen gina al’umma ta gari

Bin doka: Muhimmancinsa da tasirinsa wajen gina al’umma ta gari

Tare da BILKISU YUSUF ALI Bindoka ginshiƙi ce ta zaman lafiya, adalci da daidaito a kowace al’umma. Doka ita ce ke tsara rayuwar jama’a, tana fayyace haƙƙoƙi da nauye-nauyen mutane, tare da samar da tsarin hukunci ga masu karya doka. A duk inda bindoka ta tsaya ƙafafunta, al’umma kan samu kwanciyar hankali, ci gaba da walwala. A gefe guda kuma, inda aka yi watsi da bindoka, rikice-rikice, zalunci da koma bayan tattalin arziƙi kan yawaita. A tarihi da zamani, masana siyasa, shari’a da zamantakewa sun jaddada cewa ba za a iya gina al’umma ta gari ba sai an gina bindoka…
Read More