ukarofi

12641 Posts
Yadda ya kamata ma’aurata su yi mu’amala ta zamantakewa a watan Ramadan

Yadda ya kamata ma’aurata su yi mu’amala ta zamantakewa a watan Ramadan

Daga SA'ADATU SAMINU KANKIA Ba wai kawai a wannan watan ake buƙatar ma'aurata su zama masu mu'amala mai kyau a tsakaninsu ba, a kullum, a kodayaushe ana buƙatar ganin cewa ma'aurata sun zama masu tafiyar da rayuwarsu ta zamantakewar aure cikin fahimta, mutuntawa da ganin girma da darajar junansu. Da yake wannan watan wata ne mai yawan darajoji da kuma albarka, yana da kyau musamman ga ma'auratan da ba su da ɗabi'ar daraja junansu da su yi amfani da wannan rubutu domin gyara zamantakewar zamansu na aure da niyar ci gaba da kyawawan ɗabi'un daga wannan lokaci har ya zuwa…
Read More
Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (4)

Muhimman hanyoyi 10 na kula da fata (4)

Daga AISHA ASAS Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Kwalliya na wannan makon. Sannunku da jimirin bibiyarmu.  A wannan satin da yardar mai kowa mai komai za mu kai ƙarshen wannan darasin da ya ɗauke mu tsawon sati huɗu. 8. Goge matattun ƙwayoyin fata cikin hikima: Akwai hanyar da ake bi wurin goge fata ta amfani da wasu amintattun kayan goge matattar fata cikin sauƙi. Saidai yana da kyau matuƙa lura da irin kayan da ya kamata a yi amfani da su. Za a goge a hankali sau ɗaya zuwa uku a mako (ya danganta da irin ƙarfin…
Read More
Ramadan: Jabiru Tsauri ya raba tallafin Azumi na Naira Miliyan 300 a Katsina

Ramadan: Jabiru Tsauri ya raba tallafin Azumi na Naira Miliyan 300 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban AUDA-NEPAD, Alhaji Jabiru Tsauri (Lamiɗon Katsina), ya ƙaddamar da rabon tallafin Azumi na kimanin Naira miliyan 300 ga al’ummar shiyyar Katsina da wasu sassan Jihar Katsina. An ƙaddamar da shirin rabon tallafin ne a gidansa da ke cikin garin Katsina, inda al’umma suka ci gaba da zuwa domin karɓar nasu kason na kayayyaki da kuma kuɗin cefane. Tallafin ya haɗa da kayan abinci irinsu shinkafa, sukari da gero, tare da kuɗin cefane domin tallafa wa masu amfana rage raɗaɗin tsadar rayuwa a wannan wata mai alfarma. Waɗanda suka amfana da tallafin sun haɗa da…
Read More
Majalisar Dokokin Katsina ta amince da gina dam a Kankiya

Majalisar Dokokin Katsina ta amince da gina dam a Kankiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakin majalisar Hon. Abduljalal Haruna Runka, ɗan majalisar mai wakiltar karamar hukumar kankiya Hon. Salisu Hamza Rimaye ya bayar da ƙuduri a gina dam ga al'ummar garin Dan-nayaki dake ƙaramar hukumar, duba da garin sun kasance manoma ne na kayan mar-mari. Haka zalika ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Kaita Hon. Surajo Abdu Kwaskwaro ya nemi majalisa da ta amince da samar da ruwan sha a garin Kuntu da kuma gyara hanyar shiga karkara a garin Gwanga a mazaɓar Dankama ƙaramar hukumar Kaita. Ƙudurorin sun samu cikakken goyon baya…
Read More
Gwamnatin Katsina ta rage lokutan aikin ma’aikata saboda Ramadan

Gwamnatin Katsina ta rage lokutan aikin ma’aikata saboda Ramadan

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rage lokutan aikin ma’aikatan gwamnati domin ba su damar gudanar da ibada cikin sauƙi a watan azumin Ramadan. Sanarwar ta fito ne daga ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin Jihar, inda sanarwar ta bayyana cewa gwamnan jihar, Dikko Umaru Raɗɗa, ya amince da sauyin domin bai wa ma’aikata damar halartar karatun tafsir da sauran ayyukan ibada a wannan wata mai albarka. A cewar sanarwar, sabon tsarin ya fara aiki daga ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026. Ƙarqashin tsarin, ma’aikata za su riƙa aiki daga ƙarfe 7:30 na safe zuwa 2:30 na…
Read More
Katsina: Ana jimamin shekara ɗaya bayan rasuwar gogaggen ɗan jarida Lawal Sa’idu Funtua

Katsina: Ana jimamin shekara ɗaya bayan rasuwar gogaggen ɗan jarida Lawal Sa’idu Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. Shekara ɗaya bayan rasuwar gogaggen ɗan jarida Lawal Sa'idu Funtua mai aiki da kafar yaɗa labarai na Peoples Daily abokan an aikin sa na cigaba da rasuwar sa. Lawal Sa'idu ya rasu ne bayan yayi fama da doguwar rashin lafiya inda akai jana'izar sa a Funtua. Shugaban 'yan jarida sashin kafofin yaɗa labarai (Correspondants chapel) Yusuf Ibrahim Jargaba ya zanta da jaridar Manhaja Hausa ya bayyana rasuwar Lawal Sa'idu a matsayin babban rashi ba wai ga 'yan jaridar jihar Katsina ba har da al'ummar jihar Katsina baki ɗaya. Ya ce marigayi Lawal Sa'idu mutum mai…
Read More
NDLEA za ta iya samar da zaman lafiya

NDLEA za ta iya samar da zaman lafiya

Masu azancin magana kan ce “zaman lafiya ya fi zama ɗan sarki.” Haƙiƙa, duk wani ci gaba da gwamnati ko masu hannu da shuni ko kuma ɗaidaikun mutane za su samar ba zai ɗore ba muddin babu zaman lafiya. Wannan ne ya sa duk wani ɗan ƙasa nagari ba ya da wata fata a ƙasarsa face samun zaman lafiya da kwanciyar hankali. A ƙoƙarin samar da wannan zaman lafiya, gwamnati ta kafa hukumomi daban-daban kamar ’yan sanda, sojoji, jami’an tsaro na farin kaya (DSS), Ciɓil Defence da sauransu domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Haka kuma, gwamnati ta kafa Hukumar…
Read More
Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Zuwa ga masu tuƙin ganganci

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuh. Wannan wasiƙa an rubuta ta ne da zuciya ɗaya, da damuwa mai tsanani, da kuma fatan alheri. Ba da ƙiyayya ba, ba da tsinuwa ba, ba da zagi ba. Sai dai da ƙauna, nasiha, tunatarwa da kuma roƙo na gaskiya daga ɗan uwa zuwa ‘yan uwansa. Ina magana ne kai tsaye zuwa gare ku masu tuƙin ganganci – masu karya doka, masu sa rayuwar kansu da ta jama’a cikin hatsari a kullum. Direbobin motoci masu zaman kansu, masu kabu-kabu, musamman ’yan J5, Golf da Hiace. Masu adaidaita sahu da masu babur, musamman matasa. Da…
Read More
Salafiyyanci na buƙatar gyara

Salafiyyanci na buƙatar gyara

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Ya mai karatu, ka sani cewa mai rubutun nan baya bin kowacce irin kungiya a Musulunci, walau Izala, Shi'a, Qur'aniyyun, Darika, Ahmadiyya dss, saboda yarda da na yi da abubuwa guda biyu: 1. Allah ya gargadi Annabi cikin ƙur'ani da cewa; Q6:159 "Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa." Kuma duk wanda ya san tarihin musulunci ya san cewa duk…
Read More
Babbar alamar tashin ƙiyama da ta bayyana

Babbar alamar tashin ƙiyama da ta bayyana

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Wato idan Duniya ta doso karshenta, lokacin da mutane suka shagala daga barin ubangiji, masu addinai sun maida addini fanko, ba sa aikata abinda su ke ta wa'azi da shi a masallatai da coci-coci. Sannan akasarin al'ummomin Duniya sun raja'a ga Mulhidanci (a yanzu kasashen yamma, Amurka da Turai, da Rasha da China duk suna ta karkata ga Mulhidanci da dakile addini kowane iri). To, a wannan lokaci da mulhidai su ka mamaye dukkan kafafen ci gaban Dan Adam, kama daga na Ilimi, sadarwa, yada labarai dss sannan kuma kaso 1% na al'ummar duniya su ka…
Read More