ukarofi

12641 Posts
Allah ya jiƙan Janar Murtala Ramat

Allah ya jiƙan Janar Murtala Ramat

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tun 1966 da su Chukwuman Nzeogwu su ka shekar da jini don ƙiyayyar bambancin addini da ƙabilanci, hakan bai zama darasi ga Buka Suka Dimka ba, cewa yin kisan gilla da kuma karawa da muguwar manufar ƙabilanci ba ya kawo nasara. Dimka ɗan Arewa amma maimakon ya nuna halin dattaku irin na Janar Theophilus Yakubu Danjuma, sai ya jagoranci mutanensa su ka yi kwantan bauna a hanya su ka buɗe wuta kan shugaba Janar Murtala Ramar Muhammad a ranar 13 ga Febrairu 1976 su ka yi ma sa kisan gilla. Na ji ƙanwar Janar wato Hajiya…
Read More
Su waye ke satar yaran mu na Arewa zuwa Kudu?

Su waye ke satar yaran mu na Arewa zuwa Kudu?

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Wannan batun ba sabo ba ne. An daɗe ana tattaunawa kan yadda ake satar yara ƙanana ko sayar da su kamar gyaɗa ga masu buƙatar yara a wasu jihohin Kudu. Rahotanni da dama sun tabbatar da yadda aka riƙa sace ƙananan yara masu wayo da marasa wayo, daga gidajen iyayensu, a cikin unguwanni, da kasuwanni, zuwa jihohin Anambra, Inugu, Imo, Riba, Kuros Ribas da kuma Delta, har ma da Jihar Legas. Waɗannan yara da shekarun su ba su wuce 18 ba, waɗanda suka haɗa maza da mata, sun fito ne daga jihohin, Filato, Bauchi, Kano, Gombe,…
Read More
Yadda wasu manyan ma’aikatu ke fama da ƙarancin kuɗi a Nijeriya

Yadda wasu manyan ma’aikatu ke fama da ƙarancin kuɗi a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sabbin alƙaluma daga Ofishin Kasafin Kuɗi na Tarayya sun nuna cewa manyan ma’aikatun da ke kula da muhimman ayyukan raya ƙasa na fuskantar matsananciyar matsalar kuɗi, bayan an gano cewa ƙasa da Naira tiriliyan ɗaya ne aka saki domin ayyukan gwamnati a watanni bakwai na farkon shekarar 2025. A wani rahoto da jaridar Newspoint ta wallafa, ta ce, binciken da aka yi kan bayanan kasafin kuɗi ya nuna cewa, duk da cewa an ware Naira tiriliyan 18.53 domin ayyukan jarin Ma’aikatun Tarayya da hukumomi a kasafin 2025, adadin da aka saki tsakanin Janairu zuwa Yuli bai…
Read More
Ƙorafe-ƙorafe guda shida aka gabatar wa kwamitin zaɓen shugabannin APC a Katsina, inji shugaba

Ƙorafe-ƙorafe guda shida aka gabatar wa kwamitin zaɓen shugabannin APC a Katsina, inji shugaba

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina An bayyana cewa, ƙorafe-ƙorafe guda shida aka shigar gaban kwamitin kula da ƙorafi na zaɓen sababbin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Katsina. Shugaban kwamitin sauraren ƙorafe ƙorafe na zaɓen da ya gudana na shugabannin jam'iyar APC a matakin gunduma a jihar Sadiq Mohammed Ali ya faɗawa manema labarai a Katsina. Wasu ya'yan jam'iyar ne suka gabatarwa kwamitin da waɗannan ƙorafe ƙorafe na nuna rashin gamsuwa da yadda a ka gudanar da zaɓen a yankunansu. Ya bayyana cewa kwamitin ya zauna da waɗannan mutane ya kuma saurari koken inda ya yace kwamiti ya zauna akan su…
Read More
Na fara tunanin kafa makaranta ne lokacin da zan sa ‘yata karatu – Jamila Mu’azu Abubakar 

Na fara tunanin kafa makaranta ne lokacin da zan sa ‘yata karatu – Jamila Mu’azu Abubakar 

"Nasarorin da na samu na da nasaba da jajircewar da mahaifinmu ya yi kan ilimi" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Jajirtattun mata masu ƙwazo da himma kan duk abin da suka sa a gaba, su ne ake kira da Kallabi Tsakanin Rawwuna. Ba domin komai ba kuwa, sai don ƙoƙarin su da rawar ganin da suke takawa, wanda ko a cikin maza ma sai an tona kafin a dace da mai jarumtarsu. Hajiya Jamila Mu’azu Abubakar ɗaya ce daga cikin irin waɗannan matan da ake yi wa laƙabi da Giwar Mata. ƙwararriya ce kuma jajirtacciya kan fagen da aka fi saninta…
Read More
Shugaban ADC na Karu ya yi kira da a ƙara haɗa kai da aiki tuƙuru a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya

Shugaban ADC na Karu ya yi kira da a ƙara haɗa kai da aiki tuƙuru a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya

Daga JOHN D WADA, Keffi Shugaban jam’iyyar adawa ta African Democratic Congress (ADC) na ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa Hon. John T. Teghtegh yace sakamakon zaɓen gundumomin babban birnin tarayya Abuja da aka kammala a ƙarshen mako da ya gabata inda jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ta yi nasara a kusan dukkanin gundumomin yankin bai zo masa da mamaki ba. Shugaban ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu jim kaɗan bayan bayyana sakamakon zaɓen da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta yi. A cewarsa, jam’iyyarsa ta ADC ta sha kaye a zaɓen ne…
Read More
Al’ummar Kunduro-Bakin kogi sun roƙi gwamnati ta kawo masu ɗauki kan zargin ƙwacen filaye

Al’ummar Kunduro-Bakin kogi sun roƙi gwamnati ta kawo masu ɗauki kan zargin ƙwacen filaye

Daga JOHN D. WADA a Lafia Wani mataimakin shugaban al'ummar Koro na shiyar Keffi da Karu a jihar Nasarawa mai suna Ɗanladi Adukwa ya yi kira na musamman ga gwamnatin jihar Nasarawa da ta tarayya da shugabanni da hukumomi da suka dace da masu fafutikar kare hakin ɗan Adam musamman fannin shari'a da su hanzarta kawo masu ɗauki sakamakon ƙwace masu dukiyoyinsu da ke ƙauyen Kunduro-Bakin kogi a yankin Rayawa na Pandam na ƙaramar hukumar Karu jihar Nasarawa. Inda suka ce wasu da suka fi ƙarfin su ke cigaba da ƙwace masu filaye a yankin. Ɗanladi Adukwa ya bayyana alhinin…
Read More
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya taya Musulmi murnar azumin Ramadana

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya taya Musulmi murnar azumin Ramadana

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya fitar da saƙo mai taɓa zuciya domin murnar fara watan Ramadan na Shekarar 2026 a inda ya yi kira ga duniya baki ɗaya da ta rungumi ruhin zaman lafiya, tausayi da haɗin kai da wannan wata mai tsarki ke ɗauke da shi. A cikin saƙon nasa, Guterres ya jaddada cewa Ramadan ba lokaci ne na ibada da tunani kawai ba, wata ne na ƙarfafa bege da zaman lafiya a tsakanin al’umma. Ya yi kira ga kowa da kowa da ya yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa haɗin kai da kuma…
Read More
Amurka na shirin bai wa jama’a damar kallon abubuwan da aka haramta

Amurka na shirin bai wa jama’a damar kallon abubuwan da aka haramta

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka na shirin ƙaddamar da wani sabon shafin intanet mai taken “Freedom.gov”, wanda manufarsa ita ce bai wa jama’a, musamman mazauna Turai damar shiga da kallon abubuwan da gwamnatocinsu suka takaita ko suka haramta. Rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya fitar ya nuna cewa shirin na ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Sakataren Hulɗa da Jama’a ta Amurka, Sarah Rogers, kuma an yi niyyar sanar da shi a wani taron tsaro da aka gudanar a birnin Munich na Jamus, sai dai aka dakatar ba tare da bayyana dalili ba. Majiyoyi sun ce an tattauna yiwuwar sanya wata fasaha…
Read More
Gwamnati Kanada ta fara shirin rage dogaro da Amurka a ɓangaren tsaro

Gwamnati Kanada ta fara shirin rage dogaro da Amurka a ɓangaren tsaro

Gwamnatin Kanada ta sanar da sabbin sauye-sauye a tsarin karɓar baƙin haure masu ƙwarewa, inda za a fara bai wa wasu rukunai na musamman fifiko domin cike giɓin ƙwararru a sassa masu muhimmanci. Ministar Shige da Fice ta ƙasar ta ce sauye-sauyen na shekarar 2026 za su jawo ƙwararru da za su iya fara ba da gudunmawa nan take, musamman a ɓangaren kiwon lafiya, bincike, sufuri da kuma tsaro. Firayim Minista Mark Carney ya jaddada cewa maƙasudin shirin shi ne rage yawan mazauna na dindindin da ake karɓa a ƙasar, tare da mayar da hankali kan hazikai da za su…
Read More