ukarofi

12641 Posts
Shugaban Jamus na goyon bayan taƙaita wa yara amfani da kafofin sadarwa 

Shugaban Jamus na goyon bayan taƙaita wa yara amfani da kafofin sadarwa 

Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya bayyana goyon bayansa ga matakan da za su taƙaita damar yara shiga kafafen sada zumunta, yana mai cewa illar bayanan ƙarya da ake kirkira ta hanyar fasahar zamani ta sa ya sake duba matsayinsa. Ya ce ba za a bar al’umma ta rushe sakamakon yaɗuwar bayanan bogi da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a ba, musamman idan yara ne ke yawan shafe sa’o’i masu yawa a kan intanet. Jam’iyyarsa ta nemi a hana yara ƙasa da shekara 16 shiga wasu manhajoji, yayin da ake sa ran jihohin ƙasar za su tattauna yadda za a kafa…
Read More
Iran na ci gaba da gyara da ƙarfafa wasu muhimman wuraren soja da aka kai wa hari a shekarar baya

Iran na ci gaba da gyara da ƙarfafa wasu muhimman wuraren soja da aka kai wa hari a shekarar baya

An gina garkuwar kankare a wani muhimmin sansani An rufe hanyoyin shiga ramuka a wuraren nukiliya Matakin na zuwa ne yayin da rikici da Amurka ke ci gaba Sabbin hotunan tauraron dan adam da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani sun nuna cewa Iran na ci gaba da gyara da ƙarfafa wasu muhimman wuraren soja da aka kai wa hari a shekarar da ta gabata. Masana sun ce an gina garkuwar kankare mai kauri tare da lullube ta da ƙasa domin kare wani sabon gini a wani sansanin soja, tare da rufe mashiga zuwa wasu ramuka a wuraren da…
Read More
Legas na bada kaso 22 ga tattalin arzikin Nijeriya, inji Sanwo-Olu

Legas na bada kaso 22 ga tattalin arzikin Nijeriya, inji Sanwo-Olu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana cewa, jihar tana ci gaba da kasancewa babbar matattarar ci gaban tattalin arziki a Nijeriya, inda take bayar da kaso 22 cikin ɗari ga jimillar samun arzikin cikin gida (GDP) na ƙasa bakiɗaya. Sanwo-Olu ya yi wannan bayani ne yayin zaman Majalisar Kasuwanci a taron Oniru Business and Cultural Day da aka gudanar a daren Asabar a Legas, inda ya ce jihar ta ba da kusan ɗaya cikin biyar na jimillar GDP na ƙasa. Gwamnan ya ce, wannan ci gaba ya samo asali ne daga zaɓuka na shugabanci…
Read More
Hauhawar farashin kaya ya ragu da kashi 15 a Nijeriya – NBS

Hauhawar farashin kaya ya ragu da kashi 15 a Nijeriya – NBS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta sanar da cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya ragu da kashi 15.10 a watan Janairun bana, lamarin da ke nuna alamun samun sauƙi daga tsadar rayuwa da aka daɗe ana fama da ita. Wannan sauyin ya faru ne sakamakon daidaita tsarin lissafin da hukumar ke amfani da shi domin ya dace da yanayin kasuwanci a ƙasar. Hakan ya sa farashin kayayyakin ya ragu idan aka kwatanta da kashi 27.61% a bara. Shugaban hukumar, Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa wannan raguwa ta faru ne sakamakon sabon tsarin lissafi daga…
Read More
Dole a zamanantar da tsarin haraji – Shugaban NRS

Dole a zamanantar da tsarin haraji – Shugaban NRS

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (NRS), Zacch Adedeji, ya bayyana cewa nasarar aiwatar da sabbin dokokin sauya fasalin haraji a Nijeriya za ta ta’allaƙa ne kacokan kan rungumar tsarin fasahar zamani mai dogaro da bayanai da na’urori masu aiki kai tsaye. Adedeji ya yi wannan jawabi ne a wani taro mai taken “Daidaita Tsarin Tara Haraji da Aiwatar da Sabbin Dokokin Haraji,” wanda FCT Internal Revenue Service (FCT-IRS) ta shirya a Abuja. Ya jaddada cewa duk da cewa dokokin sauya fasalin haraji na 2025, da suka fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026, sun samar…
Read More
NLC ta yi tir da sayar da kamfanonin lantarki

NLC ta yi tir da sayar da kamfanonin lantarki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) ta bayyana cewa tsarin sayar da kamfanonin wutar lantarki a Nijeriya ya kasance “babban zamba”. A yayin wani taron shekara-shekara na mata da matasa na ƙungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta ƙasa (NUEE) da aka gudanar a Abuja a ƙarshen mako, Shugaban NLC, Kwame Joe Ajaero, ya bayyana cewa fiye da shekaru goma bayan rarraba sashen wutar lantarki, samar da lantarki ya tsaya ne tsakanin megawatt 4,000 zuwa 5,000, wato daidai matakin da ake da shi kafin tsarin sayarwar. Ajaero ya ce: “Shekaru goma bayan sayarwar da aka yi wa duniya tamkar…
Read More
Tinubu da shugaban UBA sun tattauna sauye-sauyen haraji da ƙarfafa ƙananan sana’o’i

Tinubu da shugaban UBA sun tattauna sauye-sauyen haraji da ƙarfafa ƙananan sana’o’i

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban rukunin bankin United Bank for Africa (UBA), Tony Elumelu, domin tattauna hanyoyin bunƙasa tattalin arziki, sauye-sauyen haraji da kuma ƙarfafa ƙanana da matsakaitan sana’o’i (SME) a Nijeriya. Ganawar ta gudana ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, inda Elumelu ya bayyana wa manema labarai cewa tattaunawar ta fi mayar da hankali kan yadda za a ƙara tallafa wa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, waɗanda ya bayyana a matsayin “injin ci gaban tattalin arziki.” A cewarsa, Shugaba Tinubu na da matuƙar sha’awa wajen ƙarfafa gwiwa da bai…
Read More
 Makwabta sun hallaka matashi bayan zargin afka wa mahaifiyarsa da adda

 Makwabta sun hallaka matashi bayan zargin afka wa mahaifiyarsa da adda

Wani matashi mai shekara 16 ya rasa ransa a Abuja bayan da ake zargin wasu makwabta sun doke shi har lahira, bayan ya far wa mahaifiyarsa da adda yayin wata taƙaddama ta cikin gida. Lamarin ya faru ne a ranar 12 ga Fabrairu, 2026, a unguwar Byazhin, Kubwa, cikin ƙaramar Hukumar Bwari ta Babban Birnin Tarayya Abuja. Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya fara ne a matsayin saɓani tsakanin matashin da mahaifiyarsa kafin daga bisani ya rikiɗe zuwa ramuwar gayya daga wasu mazauna unguwar. A cewar rundunar ’yan sanda, Hedikwatar ’Yan Sanda ta Byazhin ta samu kiran gaggawa da misalin…
Read More
An bankaɗo shirin wani ɗan Rasha da ya zo Afrika domin yaɗa cutar ƙanjamau

An bankaɗo shirin wani ɗan Rasha da ya zo Afrika domin yaɗa cutar ƙanjamau

Wani faifan bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta ya haddasa muhawara mai zafi, bayan an yi iƙirarin cewa wani mutum ɗan ƙasar Rasha ya yi tattaki zuwa Afirka da nufin yaɗa cutar ƙanjamau, wato HIɓ. Sai dai har yanzu babu wata hujja ta hukuma da ta tabbatar da wannan zargi. Wata mai amfani da dandalin Instagram mai suna Jullie Cassie ce ta wallafa labarin a shafinta, inda ta yi zargin cewa mutumin, wanda ta ce yana ɗauke da cutar HIɓ, ya kwanta da mata masu yawa ba tare da kororon roba ba bayan isowarsa Afirka. A cewar rubutunta,…
Read More
An kammala zangon farko na ɗaukar fim ɗin ‘Five Winners’  

An kammala zangon farko na ɗaukar fim ɗin ‘Five Winners’  

Daga MUKHTAR YAKUBU  A yanzu haka dai an kammala zangon farko na ɗaukar wani gawurtaccen fim mai dogon zango wanda Kamfanin Jammaje Production ya ɗauki nauyin shiryawa inda aka shafe kusan kwanaki ashirin ana gudanar da aikin. Fim ɗin mai suna 'Five Winners' dai tun kafin fara aikin sai da aka yi masa shiri na musamman ganin yadda aikin fim ɗin zai ɗauki tsawon lokaci da kuma maƙudan kuɗaɗe. A tsawon kwanakin da aka yi dai ana aikin abubuwa sun faru da dama wanda hakan ya mayar da fim ɗin na daban a cikin ayyukan fim da aka daɗe ba…
Read More