ukarofi

12641 Posts
Haɗa fim da wata sana’a ce mafita ga ‘yan fim don guje wa ɓacin rana – Musa Maisana’a 

Haɗa fim da wata sana’a ce mafita ga ‘yan fim don guje wa ɓacin rana – Musa Maisana’a 

Daga MUKHTAR YAKUBU  Fitaccen jarumi a masana'antar finafinai ta Kannywood Musa Abdullahi wanda aka fi sani da Musa Maisana'a, ya yi kira ga masu gudanar da harkokin su a masana'antar da su rungumi wasu sana'o'in da kasuwanci kada su tsaya a fim kaɗai.  Jarumin ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da wakilin mu dangane da yadda masana'antar take a yanzu inda yake cewa  "A yanzu ko siyasa kake yi to ka haɗa da wata sana'ar, duk abin da ka san za ka samu ɗari da kwabo ka yi, kada ka dogara da fim kaɗai. Domin idan ka dogara…
Read More
An yaba wa matan ƙaramar Hukumar Bichi bisa nuna ƙwazo a harkar sana’o’i

An yaba wa matan ƙaramar Hukumar Bichi bisa nuna ƙwazo a harkar sana’o’i

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An yaba wa matan ƙaramar Hukumar Bichi bisa jajircewa da haɗin kan da suke nunawa wajen koyon sana’o’in dogaro da kai domin inganta rayuwarsu da ta iyalansu. Daraktan Mulki na ƙaramar Hukumar Bichi, Alhaji Abba Muhammad ɗiso, ne ya bayyana hakan yayin da ƙaramar hukumar ta karɓi baƙuncin Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara kan Ayyukan Gayya da Sa-kai, Alhaji Isma’il Shehu Gurjiya. Alhaji Abba Muhammad ɗiso ya jaddada cewa matan yankin na da burin inganta zamantakewar aure da tarbiyyar yara, kasancewar su ne ginshiƙan iyali da al’umma. Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Kano bisa…
Read More
JNC a Kano ta horar da ma’aikata da suka kusa ritaya sana’o’in dogaro da kai

JNC a Kano ta horar da ma’aikata da suka kusa ritaya sana’o’in dogaro da kai

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Kungiyar Majalisar Sasanta Matsalolin Ma’aikata ta ƙasa (JNC), reshen jihar Kano, da haɗin gwiwa da ofishin shugaban ma’aikata na jihar Kano, ta shirya bitar kwana biyu ga ma’aikata da suka kusa yin ritaya domin koya musu hanyoyin sana’o’i da za su iya dogaro da kansu bayan sun bar aiki. Shugaban ƙungiyar Majalisar Sasanta Matsalolin Ma’aikata ta ƙasa, reshen jihar Kano, Kwamared Hashim A. Saleh, ya ce a shekarar 2024 suka nemi gwamnatin jihar Kano ta ba su taimakon kuɗi ta ƙarƙashin ofishin ma’aikata. Suka haɗa kai da masana da suka bar aiki da waɗanda suke…
Read More
Ana samun ɓaraka a Jam’iyyar APC a Kano

Ana samun ɓaraka a Jam’iyyar APC a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wani taron haɗa kan Jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Kano ranar Talata ya bar baya da ƙura. An gudanar da taron ne da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da kuma manyan jiga-jigar jam’iyyar na jihar, inda aka tattauna abubuwa da dama. A wajen taron ne shugaban jam’iyyar na ƙasa ya tabbatar da cewa, “za a yi aiki da tsarin rabon shugabanci kashi 60 da kashi 40,” inda ya ce rabon zai kasance tsakanin sababbin masu shigowa jam’iyyar da kuma waɗanda aka tarar tun farko.…
Read More
Karfa-ƙarfa aka mana wajen amincewa da sassan dokar zaɓe – Tambuwal

Karfa-ƙarfa aka mana wajen amincewa da sassan dokar zaɓe – Tambuwal

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya zargi shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya da yin ƙarfa-ƙarfa wajen amincewa da wani sashe na dokar zaɓe ba tare da yin gyara ba, yana mai cewa an yi hakan ne duk da adawar ɓangaren marasa rinjaye. A hirarsa da BBC, Tambuwal ya ce hatsaniya ta ɓarke ne a zauren majalisa sakamakon yadda aka ƙi amincewa da buƙatar ‘yan adawa na a sake duba sashen dokar. A cewarsa, abin da aka fara gabatarwa shi ne buƙatar hukumar zaɓe ta sauya kwanakin bayar da sanarwa daga kwana 360 zuwa 300 domin daidaita…
Read More
Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da raba tallafin azumi

Uwargidan Gwamnan Zamfara ta ƙaddamar da raba tallafin azumi

Gaga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta ƙaddamar da shirin raba tallafin azumin watan Ramadana da bukukuwan Sallah a faɗin jihar a ranar Asabar, wanda hukumar zakkat da waƙafi ta samar. Shirin ya mayar da hankali ne kan marayu 16,000 da marasa galihu a faɗin majalisun masarautu 19 na jihar. Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta bayyana cewa an tantance waɗanda suka ci gajiyar shirin kuma za a ba su buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 25, tallafin kuɗi ₦20,000, kayan sutura ga kowanne. "Muna ƙaunarku, muna ɗaukar ku da daraja, za a cigaba da…
Read More
Jami’an tsaro sun ƙubutar da mutane 21 da ‘yan bindiga su kai garkuwa da su a Katsina

Jami’an tsaro sun ƙubutar da mutane 21 da ‘yan bindiga su kai garkuwa da su a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wannan kuwa ya faru ne a wani samame na haɗin gwiwar jami’an tsaro da aka kai a Tuddan Dargaza da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa. Aikin na sirri ya samu jagoranci daga hukumar DSS tare da haɗin gwiwar sojoji ’yan sanda da kuma Community Watch Corps, lamarin da ya kai ga kama mutane huɗu da ake zargi, waɗanda a yanzu haka ake ci gaba da bincike a kansu. Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata 16, maza biyu da jarirai uku, waɗanda aka yi garkuwa da su daga Kauyen Gidan Sarkin Bayero a ƙaramar hukumar Musawa…
Read More
Ramadan: Jaji ya raba buhunan hatsi 52,000 ga mabuƙata a Zamfara

Ramadan: Jaji ya raba buhunan hatsi 52,000 ga mabuƙata a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ƙaura Namoda da Birnin Magaji, a Jihar Zamfara, Hon. Aminu Sani Jaji, ya raba buhunan hatsi iri-iri har 52,000 ga mazauna Jihar Zamfara domin rage wahalhalun tattalin arziki a lokacin azumin Watan Ramadana da muke ciki. Da ya ke jawabi a wajen ƙaddamar da rabon a Gusau yau Asabar, Hon. Sani Jaji ya ce, hatsi iri-iri da ya bai wa mutane sun ƙunshi buhunan gero, masara, dawa da shinkafa. Hakazalika ya bayyana cewar waɗanda za su amfana da tallafin sun haɗa da marayu, 'yan gudun hijira, mata…
Read More
Zaɓen gundumomi na APC a Katsina alamun nasara ne a zaɓen 2027 – Uwais

Zaɓen gundumomi na APC a Katsina alamun nasara ne a zaɓen 2027 – Uwais

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin sauraren ƙorafe ƙorafe na jam'iyar APC a zaɓen gundumomin ƙananan hukumomin jihar da ya gudana Malam Jamilu Uwais Zaki ya faɗawa manema labarai haka, wanda ya ce gudanar da zaɓen ba tare da ƙorafi ba na nuna alamun nasarar jam'iyar a zaɓen 2027. Uwais ya bayyana cewa sakamakon zaɓen shugabannin jam'iyar a waɗannan matakai ya nuna gaskiya da adalci da kuma ba duk wani ɗan jami'ya damar ayi da shi. Ya yaba wa 'yan takarar kan yadda suka nuna halin manyantaka wajen gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali. Shugaban kwamitin ya bayyana cewa…
Read More
Sule Lamiɗo – Jagora na gaskiya da ake jira

Sule Lamiɗo – Jagora na gaskiya da ake jira

“Sule Lamido mutum ne mai muhimmanci a sabon tsarin gina Nijeriya,” inji Fasto Nnamdi Orji na God’s Glorious Time Redemption Ministry da ke Abuja. Fasto Orji ya bayyana wannan a makon nan yayin tattaunawa da wasu mambobin coci kan abin da Allah ya nuna masa a matsayin wani ɓangare na abubuwan da za su haifar da sabuwar rayuwar ƙasa. Ya ce Allah ya nuna masa yadda tsohon minista kuma gwamna zai taka muhimmiyar rawa a babban aikin taimaka wa ƙasa. A halin yanzu, tsohon gwamna Sule Lamiɗo yana kallon yadda abubuwa ke gudana a ƙasar, musamman yadda jam’iyyun siyasa ke…
Read More