21
Feb
Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta ƙaddamar da mataki na takwas na shirin bibiyar ayyukan mazaɓu da na sashen zartarwa a Jihar Katsina, inda ake sa ido kan jimillar ayyuka 39 da kuɗin su ya kai naira biliyan 13.5 a yankunan sanatoci da mazaɓun tarayya na jihar. A cewar hukumar, tawagar bibiyar ayyukan ta haɗa da manyan jami’ai daga hedikwata da ofishin Katsina. Hukumar ta ce ana gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar Nigerian Institute of Quantity Surveyors da kafafen yaɗa labarai domin tabbatar da inganci, amfani…
