21
Feb
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Kula da Asusun Jama’a na Majalisar Wakilai ya umarci Ofishin Akanta-Janar na Tarayya da Ofishin Mai Binciken Kuɗi na Tarayya da su tattara tare da gabatar da cikakken rahoton haɗaɗɗen asusun Gwamnatin Tarayya da kuma rahoton binciken kuɗi na shekarun 2023, 2024 da 2025 kafin watan Oktoban 2026. Umarnin ya fito ne a yayin zaman sauraron bahasi na bincike da aka gudanar a zauren Majalisar ƙasa, inda ‘yan majalisa suka nuna damuwa kan jinkirin da ake samu wajen gabatar da rahotannin kuɗin gwamnati da aka tantance, tare da duba ingancin tsarin sarrafa kuɗaɗen jama’a a…
