ukarofi

12664 Posts
Gwamnatin Nasarawa za ta kafa ‘yan sandan jiha

Gwamnatin Nasarawa za ta kafa ‘yan sandan jiha

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana shirinta na kafa rundunar ‘yan sandan jiha idan kundin tsarin mulkin ƙasar ya amince da hakan. Kalaman sun fito ne daga kwamishinan tsaro da harkokin sauran al’amura, CP Usman Baba yayin wani taron manema labarai a Lafia, babban birnin jihar. Kwamishinan ya ce tun daga zuwan gwamnatin jihar a 2019, an fifita harkar tsaro, tare da ba rundunonin tsaro tallafi na ababen hawa da kayan aiki da sauran kayan aikace-aikace. Ya jaddada cewa gwamna Abdullahi Sule ya ƙuduri aniyar tabbatar da cewa jihar ta kasance amintacciya ga masu zuba…
Read More
Zargin kisan Kiristocin Nijeriya: Abin da rahoton Majalisar Dokokin Amurka ya ƙunsa

Zargin kisan Kiristocin Nijeriya: Abin da rahoton Majalisar Dokokin Amurka ya ƙunsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Majalisar dokokin Amurka ta tsoma baki kan zargin da ake yi na yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya. Shugaban Amurka Donald Trump ne ya umarci kwamitin majalisar wakilan ƙasar kan kasafin kuɗi ya yi bincike kan zargin kisan Kiristocin a Nijeriya. Hakan na zuwa ne bayan shugaban na Amurka ya yi barzanar far wa Nijeriya bayan ya bayyana ƙasar a matsayin 'abin kunya', inda ya ce Amurka za ta 'kawar da 'yan ta'adda' a ƙasar. Kafin ganawar da 'yan majalisar wakilan Amurkar suka yi, wata tawagar gwamnatin Nijeriya ta ziyarci Amurka domin tattaunawa…
Read More
Lakurawa sun sun kashe maƙerin  bindiga a Kebbi 

Lakurawa sun sun kashe maƙerin  bindiga a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Waɗansu mutane da ake kyautata zaton Lakurawa ne sun kai samame a kasuwar wani gari da a ke kira Amagwaro da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a ƙaramar Hukumar Arewa da ke jihar Kebbi. Wani ganau ya bayyanawa wakilin Blueprint Manhaja da cewa waɗannan Lakurawan sun shiga kasuwar ne inda suka rinka tambayar mutane suna neman wannan mutumin ne har suka gano rumfarsa, bayan da suka tambaye shi ko shi ne ke ƙera wata bindiga (Wagila), bayan amsa daga nan sai daya daga cikin su ya zaro bindiga ya harbe shi nan take…
Read More
Ranar masu buƙata ta musamman: Nakasassu 1000 ne suka amfana da tallafi a Kebbi 

Ranar masu buƙata ta musamman: Nakasassu 1000 ne suka amfana da tallafi a Kebbi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Ranar 3 ga watan Disamba ita ce ranar da aka ƙayyade a matsayin ranar nakasassu ko kuma masu buƙata ta musamman ta duniya. Jihar Kebbi ita ma ta bi sahun sauran duniya wajen bikin wannan ranar inda ta yi amfani da wannan ranar don tallafawa mutane dubu ɗaya da babura da sauran kaya na buƙatar yau da kullum a ƙarƙashin ma'aikatar ayyuka na musamman. Kwamishina a ma'aikatar Honarabul Zayyanu Umar Aliero ya bayyana cewa ma'aikatar a cikin wani akin haɗin gwiwa da ofishin Uwargidan shugaban ƙasa suka shirya wannan tallafin ga masu buƙata ta musamman.…
Read More
Kutsen ’yan bindiga a Kano na barazana ga Arewa, inji CPACI

Kutsen ’yan bindiga a Kano na barazana ga Arewa, inji CPACI

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata ƙungiya mai zaman kanta ta 'Citizens Participation Against Corruption Initiative' (CPACI), ta bayyana damuwa kan kutsen ‘yan bindiga a wasu sassan Jihar Kano, tana mai cewa lamarin na barazana mai tsanani ga zaman lafiyar Arewa baki ɗaya da ginshiƙin tattalin arziƙinta. Babban darektan ƙungiyar, Bishir Dauda Sabuwar-Unguwa Katsina, ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abuja. Ya ce, samun kutsen ‘yan bindiga zuwa yankunan wasu ƙananan hukumomi da ke jihar Kano — musamman a Shanono, Bagwai da Tsanyawa — wuri da ya kira “kagarar ƙarshe da ba a iya…
Read More
’Yan Nijeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro

’Yan Nijeriya suna da ƙwarin guiwa a kaina, ba zan ba su kunya ba — Ministan Tsaro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce ba zai bai wa ’yan Nijeriya kunya ba, saboda ƙwarin guiwar da suke da shi a kansa. Musa, wanda Shugaba Bola Tinubu ya naɗa ministan tsaro, ya bayyana haka ne a ranar Laraba lokacin da aka tantance shi a Majalisar Dattawa. Ya gode wa Shugaban ƙasa saboda zaɓarsa da ya yi a matsayin minista, sannan ya gode wa ’yan Nijeriya saboda amincewa da suka yi da shi. Ya yi alƙawarin yin iya bakin ƙoƙarinsa domin tabbatar da zaman lafiya a ƙasar nan. Ya ce: “Da…
Read More
Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin minista — Badaru

Tinubu ya san dalilin da ya sa na yi murabus daga muƙamin minista — Badaru

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, ya ce Shugaba Bola Tinubu ya san dalilin da ya sa ya yi murabus. Badaru, ya ajiye aiki ne a ranar Litinin, inda ya ce matsar rashin lafiya ce ta sa ya yi murabus. Shugaban ƙasa ya amince da murabus ɗinsa kuma ya naɗa Janar Chris Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro. Badaru, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa ya yi murabus ne saboda barazanar da Amurka ta yi na ɗaukar matakin soji kan Nijeriya game da zargin kisan Kiristoci. “Ina so na bayyana a fili cewa wannan labari…
Read More
Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai

Tsaro: Gwamnonin Arewa na shirin dakatar da haƙar ma’adinai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnonin Arewaci, na shirin dakatar da haƙar ma’adinai a wasu yankuna da ake fama da matsalar tsaro, domin daƙile ayyukan ’yan bindiga da sauran ƙungiyoyin ta’addanci. Wannan batu ya fito ne daga taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya da aka yi a Kaduna daga 1 zuwa 2 ga watan Disamba, 2025. Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na Jihar Gombe, ya ce lamarin tsaro ya kai wani mataki da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa. Ya bayyana cewa wuraren haƙar ma’adinai sun zama mafakar ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane…
Read More
Kungiyar Alƙalai ta Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa

Kungiyar Alƙalai ta Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Kungiyar Alƙalai ta Nijeriya ta karrama Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, da lambar yabo a matsayin uban ƙungiyar na ƙasa, saboda ƙoƙarinsa na tallafa wa addinin Musulunci da kuma inganta harkokin shari’a a jihar. Shugaban ƙungiyar, Alƙali Mudassir Hassan, wanda ya jagoranci tawagar zuwa gidan gwamnatin jihar, ya bayyana cewa sun ziyarci gwamnan ne domin jaddada goyon bayansu gare shi, tare da miƙa masa lambar girmamawa bisa namijin ƙoƙarin da yake yi wajen bunƙasa shari’a, da kuma inganta walwalar alƙalai. Ya nuna gamsuwarsa da salon mulkin Gwamna Namadi, yana mai cewa gwamnatin ta…
Read More
Tinubu ya rantsar da Janar Musa a matsayin Ministan Tsaro

Tinubu ya rantsar da Janar Musa a matsayin Ministan Tsaro

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da tsohon Babban Hafsan Tsaron Rundunar Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa, a matsayin sabon Ministan Tsaro na ƙasa. An gudanar da rantsarwar ne a ranar Alhamis a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, bayan Majalisar Dattawa ta amince da naɗinsa a hukumance a ranar Laraba, sakamakon tantancewar da ta ɗauki kusan awanni biyar ana yi masa. A yayin tantancewar da ‘yan majalisar suka yi masa, Janar Musa ya fuskanci tambayoyi masu tsauri kan taɓarɓarewar tsaro a wasu sassan ƙasar nan, ciki har da janyewar sojoji daga makarantar ‘yan mata…
Read More