ukarofi

12664 Posts
An yi wa Sanata Yar’Adua ihu a Safana

An yi wa Sanata Yar’Adua ihu a Safana

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina  Mutane a Safana sun yi wa Sanatan Arewa ta Tsakiya ihun 'ba ma yi'. Wannan lamari ya faru ne a garin Safana a Jihar Katsina, inda Gwamna Dikko Raɗɗa yake kai ziyarar aiki a ƙananan hukumomi da ke jihar. Yayin da yake jawabi a wajan taron ƙaddamar da wasu kayayyaki ya sanar da kyautar littafin rubutu guda 3,000 da Sanata Abdul'aziz Musa Yar'Adua, wanda yake wakiltar Katsina ta Tsakiya, sai dai nan take mutanen da ke wajen suka kama ihun “ba ma yi! Ba ma yi”. Wasu daga cikin waɗanda Wakilin Blueprint Manhaja ya tattauna…
Read More
Yanzu ƙananan hukumomin Katsina sun samu cikakken ’yanci – Gwamnan Radda

Yanzu ƙananan hukumomin Katsina sun samu cikakken ’yanci – Gwamnan Radda

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayyana cewa batun cikakken ‘yancin kai ga ƙananan hukumomi ya zama gaskiya a faɗin jihar, yana mai cewa wannan ci gaba ne mai matuƙar muhimmanci ga bunƙasar ci gaban karkara. Gwamnan ya sanar da hakan ne a yayin wani shirin tallafa wa al’umma da ƙaramar Hukumar Daura ta shirya, wanda aka gudanar a garin Daura a ranar Laraba. A cewarsa, wannan mataki wani juyin-juya-hali ne da zai buɗe sabon babi a harkokin mulki da ci gaban al’umma a matakin ƙasa. Ya ƙara da cewa, tun daga ranar 24 ga watan…
Read More
Majalisar Tattalin Arziki ta amince da biliyan N100 don gyaran cibiyoyin horar da jami’an tsaro

Majalisar Tattalin Arziki ta amince da biliyan N100 don gyaran cibiyoyin horar da jami’an tsaro

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Tattalin Arziki ta ƙasa (NEC), ta amince da ware Naira Biliyan 100, bisa jiran sahalewar Shugaban ƙasa Bola Tinubu, domin gudanar da cikakken aikin gyara da farfaɗo da cibiyoyin horas da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a faɗin Nijeriya. Matakin ya biyo bayan shawarwarin kwamitin wucin-gadi da aka kafa domin duba halin da cibiyoyin horas da jami’an tsaro ke ciki a ƙasa.  Haka kuma, a taron ta na 154 da aka gudanar ta hanyar zamani, wanda Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta, majalisar ta kuma amince da Naira Biliyan 2.6 domin kuɗin ayyukan…
Read More
Na gana da Tinubu ne kan Nnamdi Kanu, ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia

Na gana da Tinubu ne kan Nnamdi Kanu, ba batun sauya sheƙa ba — Gwamnan Abia

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai wa Shugaba Bola Tinubu, ba ta shafi batun sauya sheƙarsa zuwa jam’iyyar APC ba, sai dai a kan shugaban ’yan awaren ƙungiyar Biyafara, Nnamdi Kanu. Mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ferdinand Ekeoma, ya fayyace cewa ziyarar ta biyo bayan iƙirarin tsohon Kwamishinan jihar Charles Ogbonnaya. Tsohon Kwamishinan, ya ce Gwamna Otti ya gana da Tinubu ne don tattaunawa shirin sauya sheƙarsa zuwa APC kafin zaɓen 2027. “Gwamnan ya gana da Shugaban ƙasa bayan ziyartar Kanu a gidan yarin…
Read More
Saudiyya ta sako ’yan Nijeriya da aka maƙala wa ƙwayoyi a jaka

Saudiyya ta sako ’yan Nijeriya da aka maƙala wa ƙwayoyi a jaka

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta tabbatar da sakin ’yan Nijeriya uku da aka tsare a ƙasar Saudiyya bayan da aka kama su a filin jirgin sama na Sarki Abdul Aziz da ke Jeddah a watan Agustan 2025 bisa zargin shigo da haramtattun abubuwa. Sanarwar ta fito ne a wani saƙo da Fadar Shugaban ƙasa ta wallafa a shafinta na ɗ a ranar Alhamis. Waɗanda aka saki sun haɗa da Sadiya AbdulHamid, Hajiya Maryam Hussein Abdullahi da kuma Hajiya Bahijah Aminu Abdullahi. Bayanin ya nuna cewa an kama su ne bayan gano wasu haramtattun abubuwa a cikin kayan…
Read More
Tinubu ya naɗa Dambazau da tsohon kantoman Ribas a matsayin jakadun Nijeriya

Tinubu ya naɗa Dambazau da tsohon kantoman Ribas a matsayin jakadun Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon shugaban rundunar sojin ruwa kuma tsohon Kantoman jihar Ribas, Ibok-Ete Ekwe Ibas a matsayin Jakadan Nijeriya. Tinubu ya kuma naɗa Ita Enang, tsohon sanata da uwargidan tsohon gwamnan jihar Imo Chioma Ohakim da tsohon ministan cikin gida kuma tsohon shugaban rundunar sojin ƙasa Abdulrahman Dambazau, a matsayin jakadun. Sunayensu nasu na zuwa ne ’yan kwanaki bayan Tinubu ya aike wa Majalisar Dattijai jerin farko na waɗanda yake son nadawa a matsayin jakadun. Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar sabbin naɗe-naɗen a gaban majalisar a…
Read More
’Yan bindiga sun sace ’yan Chana biyu masu aikin titi a Kwara

’Yan bindiga sun sace ’yan Chana biyu masu aikin titi a Kwara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace ’yan ƙasar Chana biyu da ke aiki a Jihar Kwara, a wani sabon hari da ya ƙara tada hankula a yankin. Rahoton ya bayyana ne ta kafar SaharaReporters, inda majiyoyi suka tabbatar da cewa mutanen biyun ma’aikata ne a wani aikin gina hanya na kamfanin BUA a jihar. An ce an sace su ne yayin da suke bakin aiki a kan aikin titin Bode Sa’adu–Kaiama–Kosubosu, inda ’yan bindigar suka mamaye wajen da daddare suka kwashe su zuwa wani wuri da ba a sani…
Read More
’Yan bindiga sun kashe mutum uku saboda ‘yoghurt’ a Zamfara

’Yan bindiga sun kashe mutum uku saboda ‘yoghurt’ a Zamfara

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu a daren Laraba bayan da ’yan bindiga suka kai hari a unguwar Danjibga da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, sakamakon wata gardama da ta taso kan yoghurt ɗin Naira dubu uku da ɗari biyar. Bayanan harin sun fito ne ta hannun wani masani kan harkokin tsaro, Bakatsine, ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis. A cewarsa, rikicin ya fara ne lokacin da wasu ’yan bindiga suka shiga wani shago suka nemi ɗaukar yoghurt ɗin Rufaida ba tare da sun biya…
Read More
Nasarorin da na samu a harkar rubutu ba irin waɗanda sauran marubuta ke lissafawa ba ne – Tijjani Muhammad Musa

Nasarorin da na samu a harkar rubutu ba irin waɗanda sauran marubuta ke lissafawa ba ne – Tijjani Muhammad Musa

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU MANHAJA: Mu fara da jin cikakken sunanka? ARC. TLIJANI: Cikakken sunana shi ne Arc. Tijjani Muhammad Tajuddin Musa. Ina yi wa kaina laƙabi da Muhammad Tajajjini. Wasu kuma da suka sanni tun muna yara ƙanana su kan kira ni da Tajo kai tsaye. Ni marubucin adabi ne kuma ina rubuce-rubucena cikin harsuna biyu wato Hausa da Turanci. Ina rubuta rubutattun waƙoƙi na Turanci da na Hausa da kuma rubutun zube. Har ila yau ni gogaggen ɗan Jarida ne, kuma cikakken mamba na Ƙungiyar Ƙwararrun 'Yan Jarida a fannin rediyo da talabijin wato SNB. Sannan na samo…
Read More
Katsina: Mai ciki ta rasu bisa ƙin karɓar ‘transfer’

Katsina: Mai ciki ta rasu bisa ƙin karɓar ‘transfer’

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata mata mai juna biyu, Aisha Najamu, ta rasa ranta a asibitin Turai Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina bayan ma’aikatan asibitin sun ƙi karɓar kuɗin iskar ‘oxygen’ ta hanyar tura kuɗi ta yanbar gizo (wato transfer), inda suka dage cewa sai an biya kuɗi a hannu (cash) kafin a ba ta agajin gaggawa. Hakan ya sa matar har ta mutu, bisa jinkirin saka mata iskar da asibitin ta ƙi yi, don ba su zo da kuɗi a hannu ba. Lamarin, wanda ya faru ne a ranar Laraba da daddare, shaidun gani da ido sun…
Read More