ukarofi

12665 Posts
Katsina: Mai ciki ta rasu bisa ƙin karɓar ‘transfer’

Katsina: Mai ciki ta rasu bisa ƙin karɓar ‘transfer’

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata mata mai juna biyu, Aisha Najamu, ta rasa ranta a asibitin Turai Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina bayan ma’aikatan asibitin sun ƙi karɓar kuɗin iskar ‘oxygen’ ta hanyar tura kuɗi ta yanbar gizo (wato transfer), inda suka dage cewa sai an biya kuɗi a hannu (cash) kafin a ba ta agajin gaggawa. Hakan ya sa matar har ta mutu, bisa jinkirin saka mata iskar da asibitin ta ƙi yi, don ba su zo da kuɗi a hannu ba. Lamarin, wanda ya faru ne a ranar Laraba da daddare, shaidun gani da ido sun…
Read More
Matawalle ba tsararka ba ne – APC ga Gwamna Dauda

Matawalle ba tsararka ba ne – APC ga Gwamna Dauda

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar APC ta Jihar Zamfara ya yi Allah wadai da sanarwar da Gwamna Dauda Lawal ya yi a kafafen yaɗa labarai kwanan nan da ake zargin ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sharaɗin ya kori ƙaramin ministan tsaro, Hon. Bello Mohammed Matawalle kafin ya koma jam'iyyar ta APC. Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar Yusuf Idris ya yi wannan sanarwar a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a Gusau a yau Alhamis. Jam'iyyar ta yi Allah wadai da yadda Gwamna Dauda ya ya ɗauki Matawalle a matsayin babban abokin gabar sa da…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da hanyar Zobe mai tsawon kilomita 17

Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da hanyar Zobe mai tsawon kilomita 17

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da hanyar Zobe mai tsawon kilomita 17 da ta tashi daga Saubashi zuwa Shiye ta miƙa zuwa Munawa har Dan’aunai a ƙaramar hukumar Dutsi ta jihar Katsina. Gwamnan jihar ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin sa na da cikakken niyyar faɗaɗa ci gaban karkara, ƙarfafa ayyukan jin ƙai, da inganta walwalar al'ummomi a duk faɗin jihar. Ya bayyana haka ne a yayin ziyarar aiki da ya kai ƙaramar hukumar Dutsi, inda ya duba ayyukan ci gaban da ake gudanarwa tare da tattaunawa da masu ruwa da tsaki na ƙaramar hukumar. Gwamna…
Read More
Remi Tinubu ta bai wa nakasassu 250 tallafi a Zamfara

Remi Tinubu ta bai wa nakasassu 250 tallafi a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Uwargidan Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Sanata Oluremi Tinubu ta ƙaddamar da shirin ƙarfafa tattalin arziki ga nakasassu 250 a ƙarƙashin shirinta na inganta rayuwar alumma watau Renewed Hope Initiative, a jihar Zamfara. Da take jawabi a wajen ƙaddamar da shirin da aka gudanar a sakatariyar JB Yakubu da ke Gusau yau Laraba, Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa shirin zai samar da tallafin haɓaka kasuwanci da bayar da zunzurutun kuɗi Naira N200,000 ga kowane nakasashshe inda kowace jiha da kuma babban birnin tarayya za a baiwa nakassassu 250. Ta ƙara da cewa manufofin shirin shine…
Read More
2023: Ba zan ƙaurace wa Daura ba saboda Buhari – Dikko Raɗɗa

2023: Ba zan ƙaurace wa Daura ba saboda Buhari – Dikko Raɗɗa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya faɗi haka a garin Daura a cigaba da ziyarar aiki a ƙananan hukumomin jihar. Ya ce shi ba zai taɓa juya wa al'ummar ƙaramar hukumar Daura baya saboda tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari da ya taimaka masa a zaɓen 2023. Gwamnan ya bayyana ƙasar Daura a matsayin ƙasa mai ɗinbin tarihi ga shi ƙasa mai muhimmanci a siyasar Nijeriya. Malam Dikko Raɗɗa wanda ke cike da farin ciki ganin yadda ɗaruruwan mutane suka fito tarbar sa, ya sha alwashin cigaba da bin aƙidar tsohon shugaban ƙasar ta…
Read More
Zulaihat Dikko Raɗɗa ta jagoranci tattakin yaƙi da cin zarafin ’ya’ya mata

Zulaihat Dikko Raɗɗa ta jagoranci tattakin yaƙi da cin zarafin ’ya’ya mata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Uwar gidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Umar Raɗɗa, ta shiga sahun masu fafutukar yaƙi da cin zarafin ’ya’ya mata, yayin da ta halarci tattakin shekara–shekara na wayar da kan jama’a kan matsalolin fyaɗe, da sauran nau’ikan cin zarafi da mata ke fuskanta. Hajiya zulaihat ta sami wakilcin uwar gidan shugaban ma’aikatan fadar Gwamnatin Jihar Katsina, Hajiya Maijidda Abdulkadir Mamman Nasir. Tattakin, wanda ake gudanarwa kowace shekara daga 25 ga Nuwamba zuwa 10 ga watan Disamba, ya tara ƙungiyoyi da dama masu fafutuka a faɗin jihar domin mayar da hankali kan wannan batu mai…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta haɗa gwiwa da duk ƙungiyar da za ta tallafa wa harkokin ilimi

Gwamnatin Katsina za ta haɗa gwiwa da duk ƙungiyar da za ta tallafa wa harkokin ilimi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamishinan ma'aikatar ilimi a matakin farko da na sakandare Alhaji Yusuf Suleiman Jibiya ya bayyana haka, wanda ya samu wakilcin daraktan sashen kula da makarantun ƙaramar sakandare Alhaji Kabir Dodo a wajen taron kammala gasar Turanci, da ƙungiyar bunƙasa ilimin bai ɗaya ƙarƙashin Jolly Phonics ya shirya a Katsina. Kwamishinan ya bayyana gasar a matsayin wadda za ta ƙara ingiza ƙwazon ɗalibai, don haka ya yi kira ga sauran masu ruwa da tsaki da su cigaba da tallafawa shirin, domin bunƙasa harkokin ilimin jihar. A lokacin da shugaban hukumar ilimin bai ɗaya ta Jihar (SUBEB)…
Read More
Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nupe a Nijeriya (II)

Al’ummar Nufawa da kafuwar Masarautar Nupe a Nijeriya (II)

Kamar yadda jaridar Blueprint Manhaja ta fara kawo wa mai karatu tarihin asalin Nufawa a makon da ya gabata, a wannan makon za ta cigaba daga inda ta tsaya. Masarautar Bida ta zama ta farko a lokacin Turawan mulkin mallaka, a lokacin ’yancin kan Nijeriya sarakunan ƙasar Bida sun ba da gudunmawa wajen haskaka bikin ’yancin ƙasar nan. Har zuwa yau, masarautar Bida na shirya bikin gargajiya da ake wa laƙabi da ‘Nupe Cultural Day’ don tunawa da gudunmawar da sarakunan masarautar suka bayar da ake wa laƙabi da ‘Etsu’. Sarakunan ƙasar Nufe daga shekarar 1531 zuwa 1835: Tsoede, wanda…
Read More
Ƙiba da matakan guje mata – Kashi na biyu 

Ƙiba da matakan guje mata – Kashi na biyu 

Gabatarwa Ƙiba na nufin adadin kitse da ya wuce yadda ya kamata wanda ke haddasa illa ga lafiya. Mata da dama suna ɓata lokacinsu me tsada kan neman hanyoyi da za su rage ƙiba wanda wasu hanyoyin masu ɓullewa ne amma wasu kuma masu illa ne ga lafiya. Babban dalilin zaɓen wannan batu ana ganin kiba ba wai kawai lafiyar jiki ba, har ma tana shafar ƙwalliya (skin, fata), saurin tsufa, ƙwarewar rayuwa (self-esteem) da yanayin zamantakewa duka ta shafa, wanda mata su suka fi faɗawa wannan damuwar. Tsarin abinci (Sample Diet Plan) da hujjojin likitoci: Babban matakin rage ƙiba…
Read More
An yi kira ga al’ummar Funtua su guji zuba shara a magudanan ruwa

An yi kira ga al’ummar Funtua su guji zuba shara a magudanan ruwa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gidauniyar Musa Adamu Gwagware network ta yi wannan kira ta hannun shugaban ta kwamred Mannir Suleiman a Katsina. Ya ce wannan kira ya zama dole ganin yadda shara ya cunkushe a magudanan ruwa da ke cikin garin Funtua. Kwamred Suleiman ya ce wannan lamari ba ƙaramin illa bana ga lafiya al'ummar yankin. "Jibge shara a magudanan ruwa na iya kawo ambaliyar ruwa a lokacin damina dama cututtuka kamar su cutar Maleria da sauran su"Inji Mannir Suleiman. Sai ya yi kira ga al'ummar da su sa ido sosai domin kare magudanan ruwa da ke harabar su…
Read More