05
Dec
Daga UMAR GARBA a Katsina Wata mata mai juna biyu, Aisha Najamu, ta rasa ranta a asibitin Turai Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina bayan ma’aikatan asibitin sun ƙi karɓar kuɗin iskar ‘oxygen’ ta hanyar tura kuɗi ta yanbar gizo (wato transfer), inda suka dage cewa sai an biya kuɗi a hannu (cash) kafin a ba ta agajin gaggawa. Hakan ya sa matar har ta mutu, bisa jinkirin saka mata iskar da asibitin ta ƙi yi, don ba su zo da kuɗi a hannu ba. Lamarin, wanda ya faru ne a ranar Laraba da daddare, shaidun gani da ido sun…
