05
Dec
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Aƙalla mutum uku ne suka rasa rayukansu a daren Laraba bayan da ’yan bindiga suka kai hari a unguwar Danjibga da ke ƙaramar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara, sakamakon wata gardama da ta taso kan yoghurt ɗin Naira dubu uku da ɗari biyar. Bayanan harin sun fito ne ta hannun wani masani kan harkokin tsaro, Bakatsine, ta cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis. A cewarsa, rikicin ya fara ne lokacin da wasu ’yan bindiga suka shiga wani shago suka nemi ɗaukar yoghurt ɗin Rufaida ba tare da sun biya…
