ukarofi

12738 Posts
Dangote ya yi alhinin rasuwar ’yar uwar Phyna ta Big Brothers, Ruth Otabor, wacce motar kamfanin ta kashe

Dangote ya yi alhinin rasuwar ’yar uwar Phyna ta Big Brothers, Ruth Otabor, wacce motar kamfanin ta kashe

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rukunin Kamfanin Dangote ya bayyana matuƙar alhinin rasuwar Ruth Otabor, ’yar shirin Big Brother Naija season 7, Phyna. Ruth ta rasu ne a ranar Lahadi, 31 ga Agusta, 2025, makonni bayan wani hatsarin mota da ya rutsa da ita tare da ɗaya daga cikin manyan motocin kamfanin Dangote a kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Auchi da ke Jihar Edo. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar jim kaɗan bayan sanar da rasuwarta, kamfanin ya ce: “Mun yi matuƙar baƙin ciki da rasuwar Ruth Otabor, wacce ta samu raunuka a wani hatsarin mota da ya…
Read More
Yadda Osinbajo ya yi arangama da DSS kan sakin Sowore

Yadda Osinbajo ya yi arangama da DSS kan sakin Sowore

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani sabon littafi ya yi ƙarin haske kan takun saka tsakanin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) dangane da ci gaba da tsare ɗan rajin kare haƙƙin ɗan Adam kuma ɗan siyasa, Omoyele Sowore, duk da umarnin da kotu ta bayar na a sake shi. Rubutun littafin na ƙunshe ne a cikin “Na rubuta abin da nake so”, wani sabon aikin da fitaccen ɗan jarida kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Richard Akinnola ya wallafa. Littafin mai shafuka 198, wanda ya ƙunshi babi ishirin, ya ƙunshi rubuce-rubucen da…
Read More
Birtaniya ta cire ayyuka 100 daga samun bizar ma’aikata ’yan ƙasashen waje

Birtaniya ta cire ayyuka 100 daga samun bizar ma’aikata ’yan ƙasashen waje

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Birtaniya ta sanar da tsawaita wasu sabbin takunkumi kan ɗaukar ma'aikatan ƙetare zuwa ƙasarta, tare da cire sama da guraben ayyuka 100 na 'yan ƙasashen waje ciki har da 'yan Nijeriya a wani ɓangare na yunƙurin da ta ke na daƙile ƙwararar baƙin haure. Ma'aikatar Cikin Gida ta Birtaniya ta bayyana canjin manufofin a cikin wata sanarwa a shafin X ranar Asabar da safe, tana mai cewa an mai da hankali ne kan buɗe dama ga ma'aikatan Birtaniyya yayin da suke sake fasalin tsarin biza. “Sabom tsarin zai kawo daidaiton abubuwan a ƙasar. "Sama da…
Read More
NRC za ta sake fasalin ayyukan jirgin ƙasa a Nijeriya

NRC za ta sake fasalin ayyukan jirgin ƙasa a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Zirga-zirgar Jiragen ƙasa ta Nijeriya (NRC) ta fara nazari tare da sauya fasalin ayyukanta don inganta ayyukan jiragen ƙasan Nijeriya. A cewar Manajan Darakta, Dokta Kayode Opeifa, kamfanin yana ƙoƙarin farfaɗo da ayyukansa da suka haɗa da Abuja-Kaduna, Legas-Ibadan, Warri-Itakpe, da kuma jiragen ƙasa na Fatakwal-Aba. Ya ce hukumar na ƙoƙarin sake farfaɗo da Layin Narrow Gauge na Legas-Kano-Baro. Hukumar, inji shi, tana da niyyar ƙara yawan zirga-zirgar kaya da jigilar kaya, da inganta zirga-zirgar ƙasa da ƙasa kan kayayyakin amfanin gona, da samar da hanyoyin jiragen ƙasa ga jihohi. NRC tana gyara…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta saka kamfanoninta 91 a kasuwa da nufi farfaɗo da ɓangaren lantarki

Gwamnatin Tarayya ta saka kamfanoninta 91 a kasuwa da nufi farfaɗo da ɓangaren lantarki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin sayar da kamfanoni 91 mallakinta a wani sabon yunƙuri na ƙarfafa tattalin arzikin Nijeriya, da samar da ƙarin kuɗaɗen shiga, da samar da ayyukan yi. Darakta Janar na Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Ayodeji A. Gbeleyi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, inda ya jaddada cewa sabon salon sayar da kamfanoni na da nufin tabbatar da ingantaccen aiki da kuma sake fasalin muhimman sassan tattalin arzikin ƙasar. A cikin waɗanda aka lissafa akwai – Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki guda biyu (DisCos) da kuma…
Read More
Badaƙalar Dala Miliyan 2.1: Kotun Amurka ta ɗaure tsohon babban jami’in NNPC

Badaƙalar Dala Miliyan 2.1: Kotun Amurka ta ɗaure tsohon babban jami’in NNPC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon babban ma’aikacin Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL), Paulinus Iheanacho Okoronkwo, na fuskantar ɗaurin shekaru 25 a gidan yari a ƙasar Amurka, bayan da aka same shi da laifin badaƙalar cin hanci na dala miliyan 2.1 da ke da alaƙa da cinikin mai na kamfanin Addaɗ, wani reshen Sinopec na ƙasar Switzerland. A cewar wata sanarwa daga ofishin lauyoyin Amurka da ke tsakiyar yankin California, Okoronkwo, wani lauya mai shekaru 58, an same shi da laifuka uku da suka haɗa da hada-hadar kuɗi, da ƙin biyan haraji, da kuma tuhume-tuhume ɗaya na kawo cikas ga…
Read More
Gwamnatin Kano za ta sake aurar da zawarawa da ’yan mata

Gwamnatin Kano za ta sake aurar da zawarawa da ’yan mata

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin Kano ta sanar da cewa tana shirye-shiryen gudanar da auren zawarawa da ’yan mata, wanda ya zarce na baya da ta yi. Babban Kwamanda Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne bayyana hakan a yayin ziyarar gaisuwa da ya kai wa Fadar Sarkin Rano a ranar Litinin. Sheikh Daurawa ya ce a wannan karon angwaye da amaren za su mori gwaggwaban tanadi na musamman daga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf. Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban 2023 ne Gwamnatin Kano ta ɗaura auren mata 1,800 da angwayensu 1,800 wanda ta ɗauki watanni…
Read More
’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi

’Yan sanda sun kama ɗan bindiga da shanu 10 a Kebbi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta cafke wani ɗan bindiga da ake zargin ɗan ƙungiyar Lukurawa ne tare da shanu goma da ya sato, a wani samame da aka kai kasuwar shanu ta Bachaka. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Nafi’u Abubakar, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata. A cewarsa, “bayan samun sahihan bayanan sirri, an kama wani Salihu Umar, mai shekaru 42, ɗan asalin Dogon Dutse a Jamhuriyar Nijar, wanda ya shiga kasuwar shanu ta Bachaka da shanu 10 da ya sace…
Read More
Dalilin da ya sa na kori dukkan kwamishinonina – Gwamnan Neja

Dalilin da ya sa na kori dukkan kwamishinonina – Gwamnan Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Neja Umar Mohammed Bago ya ce ya rushe kwamishinoninsa ne domin auna ƙoƙarin gwamnatinsa a rabin wa'adi. A ranar Litinin ne gwamnan ya sauke duka kwamishinoninsa bayan zaman majalisar zartaswar jihar da ya guda a fadar gwamnatinsa. To sai dai yayin tattaunawarsa da manema labarai, gwamnan ya ce akwai yiwuwar sake mayar da wasu cikin kwmaishinonin a wasu ma'aikatun na daban domin sake gwada sa'arsu. Gwamnan ya ce gwamnati tana da faɗi don haka wasu za su sake komawa wasu fannonin. “Wasu za su sake dawowa, yayin da wasu za su koma…
Read More
Wike da magoya bayansa sun gabatar da sharuɗɗa kafin amincewa da babban taron PDP

Wike da magoya bayansa sun gabatar da sharuɗɗa kafin amincewa da babban taron PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabannin Jam’iyyar PDP masu goyon bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike, sun gindaya sharuɗɗa kafin gudanar da taron gangamin ƙasa na jam’iyyar. A taron da suka gudanar a Abuja ƙarƙashin ƙungiyar Eminent Leaders and Concerned Stakeholders of PDP, sun dage cewa Shugaban PDP na ƙasa ya ci gaba da kasancewa daga Arewa ta Tsakiya, kamar yadda aka tsara a rabon muƙaman taron 2021. Haka kuma sun buƙaci a gudanar da sabbin tarurruka a jihohin Ebonyi da Anambra, da taron ƙananan hukumomi a Jihar Ekiti, tare da sake kiran sabon taron yankin Kudu maso Gabas.  Sun…
Read More