06
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamitin masallacin juma'a na kungiyar Jama'atul Izalatul Bidi'a Wa Ikamatul Sunnah ta sanar da rufe masallacin da ke garin Kankiya sakamakon ambaliyar ruwa da ya mamaye masallacin. Masallacin da ke unguwar Layi quaters ya kai shekara 40 da tubawa,kuma wannan shine karo na farko ya fuskanci wannan iftala'i. Mai magana da yawun kwamitin Sheikh Khalid Kashim ya bayyana cewa yanzu za a rinƙa gudanar da sallar juma'a a Masallacin Masjid ibn Taymayya a unguwar Gurara. Ya ce sakamakon ambaliyar ruwa an dakatar da gudanar da salla a masallacin har sai wani lokaci. Sheikh Kashim ya…
