ukarofi

12738 Posts
A lissafin da na yi, Tinubu na uku zai zo a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027 – El-Eufai

A lissafin da na yi, Tinubu na uku zai zo a zaɓen Shugaban ƙasa na 2027 – El-Eufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai zo na uku ne a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. El-Rufai jigo a jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa Tinubu zai sha kashi a zaɓen 2027 idan ya tsaya takara, inda ya ce mafi yawan abin da zai samu shi ne zuwa na uku a zagaye na farko wanda hakan zai kai ga sake zaɓe ba tare da shi ba. El-Rufai ya bayyana haka a tattaunawa da tashar Channels a ranar Lahadi, inda ya shawarci Tinubu da ya ɗauki darasi daga tsohon…
Read More
Mambobin APC sama da 200 sun sauya sheƙa zuwa PDP a Jigawa 

Mambobin APC sama da 200 sun sauya sheƙa zuwa PDP a Jigawa 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla mambobi 289 na Jam’iyyar APC mai mulki sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PDP a  mazaɓar Sakwaya, ƙaramar Hukumar Dutse, jihar Jigawa. Jaridar Manhaja ta rawaito cewa taron sauya sheƙar ya gudana ne a ranar Juma’a a ofishin PDP na mazaɓar, inda mataimakin shugaban jam’iyyar na jiha, Umar Danjani, ya wakilci shugaban jihar wajen tarbar sabbin mambobin. ɗanjani ya yaba wa fitattun ‘yan adawa da suka fito daga sassan jihar don halartar taron, yana mai bayyana sauya sheƙar a matsayin babban ƙarfafawa ga jam’iyyar wajen samun haɗin kai da ƙarfi gabanin zaɓe. Ya jaddada…
Read More
2027: PDP za ta iya samun kanta cikin matsala idan ta ba Jonathan takara – Keyamo

2027: PDP za ta iya samun kanta cikin matsala idan ta ba Jonathan takara – Keyamo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya Festus Keyamo a ranar Lahadi ya shawarci jam’iyyar PDP da kada ta tsayar da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takararta a 2027. Keyamo ya bayyana a ranar Lahadin da ta gabata cewa ‘yan adawa na fuskantar babban sakamako a zaɓe mai zuwa idan suka dogara da tsohon gwamnan Anambra Peter Obi a matsayin ɗan takararta. Ya ce jam’iyyar PDP ta ci gaba da kasancewa a cikin “matsalolin da ba za a yi hassada ba” bayan ta kasa tsayar da tikitin tsayawa takara a…
Read More
 NASFAT ta yi gargaɗi kan yin ɓatanci ga Annabi Muhammad

 NASFAT ta yi gargaɗi kan yin ɓatanci ga Annabi Muhammad

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Musulunci ta Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) ta yi kira ga malamai da mabiya addinin Islama a duniya da su guji yin kalaman ɓatanci ga sahabban Annabi Muhammad (SAW), tana mai cewa yin hakan zunubi ne mai girma kuma ya saɓa wa koyarwar addini. ƙungiyar ta yi kiran ne bayan rahotannin da ke nuna cewa wasu malamai a Jihar Kwara da wasu sassan Yammacin Nijeriya sun shiga cece-kuce saboda irin waɗannan kalamai a jan sahabban Annabi (RA). NASFAT ta ce addinin Musulunci ya umarci a yi biyayya ga Allah da Manzonsa (SAW) tare da girmamawa da ƙaunar sahabbai…
Read More
Rushe kasuwar Alaba Rago: Ya kamata shugabannin Arewa su sa baki – ABMPF

Rushe kasuwar Alaba Rago: Ya kamata shugabannin Arewa su sa baki – ABMPF

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Arewa ta ’Yan Jarida (ABMPF) ta roƙi Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da rushe Kasuwar Alaba Rago da Gwamnatin Jihar Legas ta fara, tana mai cewa matakin ya jawo asarar biliyoyin naira tare da barin dubban ’yan kasuwa cikin halin ƙaƙa-ni-ka-yi. Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abdullahi Yelwa, ya ce rusau ɗin ya haddasa wa ’yan kasuwar asarar kimanin Naira biliyan 20, tare da ruguza shaguna da wuraren ibada fiye da 40, abin da ya ce “bai dace ba kuma yana iya jawo rikicin ƙabilanci.” ƙungiyar ta roƙi gwamnonin Arewa, ’yan majalisa da sarakuna na gargajiya…
Read More
Zargin ɗaukar nauyin ’yan bindiga: Kungiyar Birnin-Gwari ta caccaki El-Rufa’i

Zargin ɗaukar nauyin ’yan bindiga: Kungiyar Birnin-Gwari ta caccaki El-Rufa’i

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD wata ƙungiyar ta masu goyon bayan shugabanci na gari a Birnin-Gwari, wato ‘Birnin-Gwari ɓanguard for Security and Good Goɓernance’, ta yi tir da abinda ta kira da kalaman ƙarairayi da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya ƙirƙira akan tsarin zaman lafiya na Ƙaramar Hukumar Birnin-Gwari a jihar. Ta bayyana kalaman nasa a matsayin ‘kare mai haushi ga wata’ duba da cewa sun ci karo da abinda ya bayyana a zahiri ga al’umma a yankin. A wata takarda da Shugaban ƙungiyar, Ibrahim Abubakar NaGwari ya fitar, ƙungiyar ta bayyana kalaman El-Rufa’i na cewa Gwmanatin jihar…
Read More
Kungiyar malamai da ma’aikatan kwalejojin ilimi sun yi taro a Kano

Kungiyar malamai da ma’aikatan kwalejojin ilimi sun yi taro a Kano

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Kungiyar Malaman Kwalejoji ta Nijeriya (COEASU), ƙarƙashin shugabancin reshan ta na makarantar sha re karatun jamia da karatu mai zirfi da aka fi sani da 'Kano State College of Education Preliminary Studies' ƙarƙashin shugabancin Dakta Sunusi Yakubu Ahmad Bichi da kwalejin da ya ke shugabanta ta karɓi taron ƙungiyar a wannan karan wanda kuma shugaban wannan ƙungiya na makarantar da akafi ta CAS kwamaret Aminu Hamisu Auwalu ya jogranci wannan gagarunmin taron na COEASU na Arewa Maso Yamma wanda ya gudana a birnin Kano wanda aka fara a ranar litinin da ta gabata. A jawabin…
Read More
Ba da igiyar auren wani na shigo harkar fim ba – Aisha Muhammad (Momi)

Ba da igiyar auren wani na shigo harkar fim ba – Aisha Muhammad (Momi)

Daga MUKHTAR YAKUBU An daɗe ana samun matsalar shigowar matan aure harkar fim ta hanyoyi da dama ba tare da an san da hakan ba sai kuma daga baya idan ta bayyana matar aure ce abin ya kan karewa da rigima ko kuma a dangana zuwa ga hukuma.  Akwai misalai da yawa da hakan ta faru, amma babban misalin da ya fi shahara shi ne na baƙuwar Rarara da aka yi a shekarun baya, lokacin da wata matar soja ta zo aka saka ta a fim sai bayan an zo an kwashi su Dauda Rarara da Usman Mu'azu a motar…
Read More
Kisan jaruma Laila Khan da iyalinta ya shiga tarihi a kotun Mumbai

Kisan jaruma Laila Khan da iyalinta ya shiga tarihi a kotun Mumbai

Daga AISHA ASAS  Al’umma sun sake tunawa da Laila Khan, wacce ta fito a fim ɗin Wafa: A Deadly Loɓe Story tare da Rajesh Khanna a shekarar 2008. Laila da iyalinta guda biyar sun gamu da ajalinsu a shekara ta 2011, a wani kisan gilla da ya girgiza Bollywood. A wannan mako, kotun Mumbai ta bayyana cewa, wannan kisan ya zama abin ban mataki wajen irin mummunan laifi, inda alƙalin ya bayyana shi a matsayin “rarest of rare”. Wannan kalma na nufin cewa laifin ya sha bamban ko in ce ya zama ɗaya cikin dubu na yadda aka saba gani…
Read More
Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Ɗandume

Yan bindiga sun kashe mutum bakwai a Ɗandume

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan bindiga ɗauke da manyan makamai sun kai mummunan hari a ƙauyen Magajin Wando da ke ƙaramar hukumar Ɗandume inda nan take suka kashe mutane bakwai. Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu'azu Ɗanmusa ya sanar da faruwar haka a wata takarda da ya fitar. Ya bayyana cewa jami'an tsaro na CWC suka kawo ɗauki a yayin da yan bindiga ke Kai hari a ƙauyen.Haka kuma bayan da jami'an tsaron suka ɗauki waɗanda suka samu raunuka zuwa asibitin Ɗandume nan ma waɗannan ƴan bindigan suka sake tare su. Sai dai bisa jajircewa, jami'an…
Read More