ukarofi

12738 Posts
Fadar Shugaban ƙasa ta yi Allah-wadai da “bayanan ƙarya” na jaridar Daily Trust kan Tinubu

Fadar Shugaban ƙasa ta yi Allah-wadai da “bayanan ƙarya” na jaridar Daily Trust kan Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban ƙasa ta buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wata jarida ta ƙasa mai suna “Daily Trust,” inda ta zarge ta da yin wasu rahotanni masu ɗaukar hankali kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu. Fadar shugaban ƙasar ta bayyana rahotannin a matsayin tatsuniyoyar gizo da ƙoƙi da aka shirya domin a zayyana gwamnati a cikin mummunan yanayi. A wani saƙon da ya wallafa a shafinsa na ɗ, @aonanuga1956, a ranar Lahadi, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya ce jaridar Daily Trust “wata tushe…
Read More
Zama cikin aminci da nake a yanzu ya isheni, ba zan sake komawa ‘Aso Rock’ ba, inji uwargidan Jonathan

Zama cikin aminci da nake a yanzu ya isheni, ba zan sake komawa ‘Aso Rock’ ba, inji uwargidan Jonathan

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Uwargidan tsohon shugaban ƙasa, Dame Patience Jonathan, ta yi kakkausar suka, inda ta yi watsi da duk wani yunƙuri na komawa Aso Rock, inda ta ce ta fi daraja zaman lafiyarta fiye da matsin rayuwar siyasa. Manhaja ta ruwaito cewa wani hoton bidiyon jawabin nata da aka sake naɗa a watan Mayun 2025 a wani taron Abuja inda aka karrama ta da lambar yabo ta shugabar mata ta Accolades Dynamics Limited, ya sake tayar da muhawara yayin da ake ci gaba da cece-kuce game da mijinta, tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, da kuma zaɓen…
Read More
Tinubu ya dawo da shugaban NTA da aka sauke

Tinubu ya dawo da shugaban NTA da aka sauke

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin mayar da tsohon Shugaban Gidan Talbijin na Nijeriya, NTA da aka sauke kwanan nan, Salihu Abdullahi Dembos. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, ya ce Dembos wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a watan Oktoban 2023, a yanzu zai dawo domin kammala wa’adin mulkinsa na shekara uku. Haka ma shugaban ƙasar ya bayar da umarnin maido da Mista Ayo Adewuyi a matsayin babban daraktan sashen labarai na NTA, domin shi ma ya ƙarasa wa’adinsa na shekara uku da zai ƙare…
Read More
Kotu a Finland ta yanke wa jagoran Biafara Simon Ekpa hukuncin shekara shida a gidan yari 

Kotu a Finland ta yanke wa jagoran Biafara Simon Ekpa hukuncin shekara shida a gidan yari 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kotu ta Päijät-Häme da ke Finland ta yanke wa Simon Ekpa, mai rajin kafa ƙasar Biyafara, hukuncin shekara shida a gidan yari kan laifukan ta’addanci. Kotun ta same shi da laifin tayar da zaune-tsaye da kuma shiga cikin ayyukan ƙungiyar ta’addanci. A cewar jaridar YLE ta Finland, kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi amfani da “yawan mabiyan da yake da su a kafafen sada zumunta” wajen hura tarzoma a yankin kudu maso gabashin Nijeriya tsakanin watan Agustan 2021 da Nuwamban 2024. Kotun ta kuma gano cewa Ekpa babban jigo ne a wata ƙungiyar…
Read More
Babu wani ƙorafi akan Kakakin Majalisa Abbas, Majalisar Wakilai ta ƙaryata rikici kan tallafin ayyukan mazaɓu

Babu wani ƙorafi akan Kakakin Majalisa Abbas, Majalisar Wakilai ta ƙaryata rikici kan tallafin ayyukan mazaɓu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta musanta rahotannin da ke cewa akwai rikicin da ya kunno kai kan kakakin majalisar Abbas Tajudeen, kan jinkirin da aka samu na kuɗaɗen ayyukan mazaɓu, inda ta dage cewa majalisar ta 10 ta ci gaba da kasancewa tare da mai da hankali kan ayyukanta na majalisa. A cikin wata kakkausar murya da ya fitar a yammacin ranar Lahadin da ta gabata ga jaridar Manhaja, mai magana da yawun majalisar, Akin Rotimi Jr, ya yi watsi da iƙirarin cewa ‘yan majalisar na shirin yin fito-na-fito da shugaban majalisar, yana mai bayyana rahoton…
Read More
Ta’addanci: Yadda yara da makarantu suka tagayyara a Nijeriya – UN

Ta’addanci: Yadda yara da makarantu suka tagayyara a Nijeriya – UN

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dinkin Duniya ta yi wani gargaɗi game da ƙaruwar ta'addanci a yammacin Afirka da yankin Sahel, inda ta bayyana cewa yara 1,364 ne ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai suka ɗauka aiki a shekarar 2024, yayin da sama da makarantu 14,000 aka tilastawa rufewa saboda rashin tsaro. An bayyana wannan mummunan ƙididdiga ne ta hannun mataimakin sakatare-janar na Majalisar ɗinkin Duniya kuma wakilin musamman a yammacin Afirka da yankin Sahel, Leonardo Simao, a taron yankin na yaƙi da ƙungiyoyin 'yan ta'adda da suka kunno kai da kuma ƙarfafa zaman lafiya mai ɗorewa a yankin ECOWAS da…
Read More
Tinubu zai tilasta saka ma’aikata a inshorar lafiya

Tinubu zai tilasta saka ma’aikata a inshorar lafiya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da inshorar lafiya a duk ma’aikatu da hukumomi (MDAs) daidai da dokar Hukumar Inshorar Lafiya ta ƙasa (NHIA) ta shekarar 2022. Wata sanarwa da mai ba Tinubu shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ta ce, hukumomi za su sanya ma’aikatansu cikin shirin Hukumar Inshorar Lafiya ta ƙasa (NHIA), tare da zaɓin ɗaukar ƙarin bayanan sirri daidai da dokar. Sanarwar ta ƙara da cewa "Dukkanin hukumomi dole ne su gabatar da takardar shaidar Inshorar lafiya ta NHIA da ta bayar a matsayin wani ɓangare…
Read More
Ina amfanin baɗi ba rai – Obi ya soki kuɗaɗen shiga da Nijeriya ke samu

Ina amfanin baɗi ba rai – Obi ya soki kuɗaɗen shiga da Nijeriya ke samu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Dan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Peter Obi, ya caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan iƙirarin cimma burin samun isassun kuɗaɗen shiga a Nijeriya a 2025, inda ya ce har yanzu ’yan Nijeriya na cikin ƙunci. A ranar Talata, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce Gwamnatin Tarayya ta cimma burinta na samun kuɗaɗen shiga a shekarar 2025 kafin lokacin da aka tsara, inda ya kawar da batun ci gaba da karɓar bashi. Shugaban ya ce, an samun kuɗin ne ba ta hanyar man fetur ba, inda ya ce gwamnatinsa ta samu…
Read More
Maulidin Nabiyyi: Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga Musulmi su gabatar da addu’o’in samun zaman lafiya

Maulidin Nabiyyi: Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga Musulmi su gabatar da addu’o’in samun zaman lafiya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A sanarwar da sakataren yaɗa labarai na gwamnan Muhammad kaula ya fitar,Gwamnan yayi wannan kalaman ne a saƙon taya musulmi murnar zagayowar tunawa da ranar haihuwar Annabi Muhammadu SAW ga al'ummar jihar. Gwamna Raɗɗa ya bayyana bikin Mauludi a matsayin wani lokaci na musamman domin gudanar da addu'o'i, da kuma ƙara jajircewa wajen bin koyarwa da kyawawan halayen Annabi Muhammad (SAW). Gwamnan ya jaddada cewa koyarwar Annabi Muhammad ta zaman lafiya, adalci, haƙuri, da ƙaunar juna, na da matuƙar muhimmanci wajen fuskantar ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta a halin yanzu. Gwamnan ya yi kira…
Read More
Jerry Damara ya fice daga PDP zuwa APC a Gombe ta Kudu

Jerry Damara ya fice daga PDP zuwa APC a Gombe ta Kudu

Daga ABUBAKAR A BOLARI a Gombe Fitaccen ɗan siyasa kuma attajiri na yankin Tangale-Waja, a Gombe ta kudu Hon. Jerry Joseph Damara, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Damara, wanda shi ne shugaban kamfanin Mesotho Group da Kugbo International Market, ya miƙa katin shaidar mambobinsa na APC ga gwamna Muhammad Inuwa Yahaya a gidan gwamnatin Gombe. Ya ce ya yanke shawarar hakan ne sakamakon ci gaban da gwamnatin Inuwa Yahaya ta samu da kuma salon shugabancin sa na haɗa kan al’umma. A nasa jawabin, Gwamna Yahaya ya bayyana wannan sauyi a matsayin babban ci gaba ga jam’iyyar APC,…
Read More