05
Sep
Gwamnatin soja ta Burkina Faso ta sanar da dokar da ta haramta luwaɗi, tare da kafa hukuncin ɗaurin kurkuku na tsawon shekaru biyu zuwa biyar ga duk wanda aka samu da aikata irin wannan hali. Wannan mataki ya zama ɗaya daga cikin sabbin tsare-tsaren da gwamnati ta ɗauka wajen gyaran tsarin iyali da dokokin ɗan ƙasa. Ministan Shari’a, Edasso Rodrigue Bayala, ne ya bayyana wannan doka a tashar talabijin ta ƙasa (RTB). A cewarsa, “Doka ta tanadi ɗaurin kurkuku daga shekara biyu zuwa biyar tare da tara mai tsoka. Idan wani ya aikata luwaɗi ko makamancinsa, ko wasu ɗabi’un da…
