ukarofi

12738 Posts
2027: Da yiwuwar Kwankwaso ya shiga APC – Kofa

2027: Da yiwuwar Kwankwaso ya shiga APC – Kofa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Dan majalisar wakilai, Abdulmumin Jibrin, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, bai rufe ƙofar shiga jam’iyyar APC ba gabanin zaɓen 2027. Jibrin, jigo a jam’iyyar NNPP, ya ce Kwankwaso har yanzu ya bar  kofar tattaunawa a buɗe da Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC, duk da kasancewarsa ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023. Ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels  inda ya ƙara da cewa ƙungiyar Kwankwasiyya ƙarfin siyasa ce da ba za a iya watsi da ita ba. Sai dai ya nuna…
Read More
Gwamna Inuwa ya samar da ababen more rayuwa a Jihar Gombe – Dr. Jatau

Gwamna Inuwa ya samar da ababen more rayuwa a Jihar Gombe – Dr. Jatau

Daga GAMBO ISA a Abuja Shugaban ƙaramar Hukumar Balanga a Jihar Gombe Honorabul Dr. Ibrahim Jatau Salihu ya yabawa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya bisa gagarumin ci gaban da yake samarwa a faɗin jihar. A cikin wata sanarwar manema labarai da ya raba wa jaridar Blueprint a Abuja, Dokta Jatau ya bayyana nasarorin da gwamnan ya samu a muhimman sassa da suka haɗa da bunƙasa jarin ɗan Adam, samar da ababen more rayuwa, noma, kiwo, ilimi, kiwon lafiya, da kuma tsaro. A cewarsa, ƙoƙarin gwamnan ya bayyana a fili wajen samar da ƙarin kansiloli 13 na raya kasa, gyaran sakatarorin ƙananan…
Read More
An kama wata uwa kan binne jaririyarta a Kebbi

An kama wata uwa kan binne jaririyarta a Kebbi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ’Yan sanda a Jihar Kebbi sun kama wata matashiya mai shekara 20, Maryam Atiku, bisa zargin binne jaririyar da ta haifa da ranta a unguwar Nasarawa da ke Kamba a ƙaramar Hukumar Dandi. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, CSP Nafi’u Abubakar, ya fitar a wannan Larabar. Ya ce matashiyar bayan ta haifi jaririyar, ta naɗe ta a cikin wasu zannuwan atamfa guda uku, sannan ta kai ta wani daji da ake kira Malam Yaro a yankin Nasarawa, inda ta tono rami ta binne ta…
Read More
Yadda ‘yan daba suka tarwatsa taro kan rashin tsaro a Katsina

Yadda ‘yan daba suka tarwatsa taro kan rashin tsaro a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Wani taron tsaro da aka shirya a Katsina ƙarƙashin Katsina Security Community Initiative ya rikide zuwa tarzoma bayan wasu ‘yan daba da ake zargin masu goyon bayan siyasa ne suka tarwatsa shi. Taron, wanda ya haɗa kwararru daga bangarorin tsaro, tsoffin jami’an soji da ’yan sanda, masana da shugabannin al’umma, an shirya shi ne domin tattauna hanyoyin magance matsalar tsaro da ta addabi jihar. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa rikicin ya fara ne lokacin da mai shirya taron, Dr. Bashir Kurfi, yake bayyana matsalolin tsaro a jihar, inda wani ya katse shi da zargin cewa…
Read More
Kuɗaɗen da ake warewa ‘yan majalisu domin yi wa mazaɓu aiki tamkar na sata ne – Obasanjo

Kuɗaɗen da ake warewa ‘yan majalisu domin yi wa mazaɓu aiki tamkar na sata ne – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon Shugaban Nijeriya, Olusegun Obasanjo, ya sake caccakar 'yan majalisun dokokin ƙasar wanɗanda ya bayyana su a matsayin mafi munin da aka taba gani, bayan Jamhuriyar ta ɗaya da biyu da kuma ta uku. Obasanjo ya bayyana kuɗaɗen da 'yan majalisun na jihohi da na tarayya ke karɓa da sunan ayyukan mazaɓu a matsayin fashi da kuma yunƙurin su na tattara kuɗaɗen da ba na halal ba. Blueprint Manhaja ta ruwaito Obasanjon a littafin da ya wallafa yana cewar, sau biyu ya na karo gaba da gaba da 'yan majalisun a matakin ƙasa, kuma…
Read More
Tinubu ya kawar da matsalar rashin biyan albashi a jihohi 27 — Idris

Tinubu ya kawar da matsalar rashin biyan albashi a jihohi 27 — Idris

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar sun kawo ƙarshen matsalar biyan albashi a jihohi 27. Ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin da kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohi 36 suka kai masa ziyara. Idris ya ce manufofin shugaban suna tafiya ne don amfanin ƙasa baki ɗaya, ba siyasa ba, tare da tabbatar da cewa ayyuka suna gudana a dukkan jihohi ba tare da nuna bambanci ba. Ministan ya ce cire tallafin man fetur ya buɗe sabbin hanyoyin samun kuɗaɗe ga jihohi, wanda ya…
Read More
Kebbi: An ƙaddamar da shugabannin jam’iyyar ADC a ƙaramar Hukumar Argungu 

Kebbi: An ƙaddamar da shugabannin jam’iyyar ADC a ƙaramar Hukumar Argungu 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Ranar Larabar da ta gabata ne aka ƙaddamar da shugabannin Jam'iyyar ADC a ƙaramar Hukumar mulki ta Argungu. Da ya ke jawabi ga sababbin shugabannin, jagoran siyasar yankin gudummar mazaɓar Kebbi ta Arewa, Alhaji Ibrahim Muhammad Mera ya bayyana cewa wannan tafiyar fa ba an soma ta ba ne don a bari ba saboda haka idan aka yi la'akari yanayin da wannan ƙasar ta samu kan ta na tabɓrɓarewar al'amurra tun kama daga tattalin arziki zuwa tsaro an sami ci baya ba ɗan ƙarami ba. Wannan aikin ya wuce siyasa ko wani abu mai kama…
Read More
Harajin da ba na man fetur ba a Nijeriya ya kai tiriliyan N20.6, ya ƙaru da kashi 40 cikin 100 – Fadar Shugaban ƙasa

Harajin da ba na man fetur ba a Nijeriya ya kai tiriliyan N20.6, ya ƙaru da kashi 40 cikin 100 – Fadar Shugaban ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Fadar Shugaban ƙasa ta sanar da cewa kuɗaɗen shiga na Nijeriya da ba na mai ba ya ƙaru da kashi 40.5 cikin ɗari zuwa tiriliyan N20.59 tsakanin watan Janairu zuwa Agustan 2025, wanda ya nuna abin da ta bayyana a matsayin kasafin kuɗi mafi ƙarfi a tarihi. Wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Larabar da ta gabata, ta bayyana cewa an samu ƙaruwar kuɗaɗen da aka samu daga Naira tiriliyan 14.6 da aka samu a daidai wannan lokacin na shekarar…
Read More
Kebbi: An kama ɗan Jamhuriyar Nijar da shanun da Lakurawa suka sace

Kebbi: An kama ɗan Jamhuriyar Nijar da shanun da Lakurawa suka sace

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan sandan Tarayyar Nijeriya a garin Bachaka da ke kan iyakar Nijeriya da Jamhuriyar Nijar a yankin ƙaramar Hukumar mulki ta Arewa da ke Jihar Kebbi sun cika hannu da wani mutum mai suna Salihu Umar ɗan asalin Dogon Dutsi da ke Jamhuriyar Nijar a kasuwar Bachaka da shanu 10 da Lakurawa suka sace daga garin Zogirma da ke ƙaramar Hukumar mulki ta Bunza kimanin sati biyu da suka wuce. Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kebbi ta bakin jami'in hulɗa da jama'a, Sufurtanda Nafi'u Abubakar ya ce, yanzu haka dai 'yan sanda suna nan sun…
Read More
Ni ne na ba Nafisa kyautar N200,000, ba daga Gwamnatin Tarayya ba – Ministan Ilimi

Ni ne na ba Nafisa kyautar N200,000, ba daga Gwamnatin Tarayya ba – Ministan Ilimi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ma’aikatar Ilimi ta Tarayyar Nijeriya ta yi ƙarin haske kan cece-kuce dangane da kyautar kuɗi da aka baiwa ɗaliban Nujeriya da suka yi nasara a gasar duniya ta TeenEagle 2024/2025 da aka gudanar a ƙasar Birtaniya. Bayanin ya biyo bayan rahotannin da ake yaɗawa a shafukan sada zumunta da wasu kafafen yaɗa labarai na yanar gizo da ke nuni da cewa Gwamnatin Tarayya ta bada Naira Miliyan 1.7 a matsayin kyautar kuɗi ga haziƙan matasan. A watan Agusta 2025, an ba da N200,000 ga Nafisa Abdullahi, wacce ta lashe gasar Turanci ta duniya ta TeenEagle. Jim…
Read More