Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ranar Larabar da ta gabata ne aka ƙaddamar da shugabannin Jam’iyyar ADC a ƙaramar Hukumar mulki ta Argungu.
Da ya ke jawabi ga sababbin shugabannin, jagoran siyasar yankin gudummar mazaɓar Kebbi ta Arewa, Alhaji Ibrahim Muhammad Mera ya bayyana cewa wannan tafiyar fa ba an soma ta ba ne don a bari ba saboda haka idan aka yi la’akari yanayin da wannan ƙasar ta samu kan ta na tabɓrɓarewar al’amurra tun kama daga tattalin arziki zuwa tsaro an sami ci baya ba ɗan ƙarami ba.
Wannan aikin ya wuce siyasa ko wani abu mai kama da haka, wannan aikin jihadi ne na ceto kai daga halaka.
Wani abin ban haushi ga ma’abota hankali shi ne, idan kun lura da wannan yankin ne na arewa a ke neman a kassara saboda a wannan yankin ne a ke noma duk wani nau’i na abinci da a ke safarar sa zuwa sassan kudancin ƙasar nan, a nan ne a ke samar da dabbobi da a ke safarar su zuwa sassan kudancin ƙasar nan ana duk da haka nema a ke yi a wargaza wannan yankin.
Saboda haka kowa ya ja damara don fafutukar ƙwato yancin arewacin ƙasar nan.
Ya kuma bayyana cewa yanzu an soma sabunta katin zaɓe saboda haka wanda ta sa ta bata da matasa da suka kai shekaru goma sha takwas da su yi kokari su tafi cibiyoyin da aka tsara don bayar da sababbin katin su yanki katin jifar kuri’a.
Duk yadda ka ke son wani ɗan siyasa da ka ke yi wa kyakykyawan zato idan ba ka jefa masa ƙuri’a ba to tamkar ka goyi bayan ta’adanci ne saboda haka a ƙarfafa wa mutane gwiwa da su je su karɓi kati.
Da ya ke jawabi a madadin sababbin shugabannin shugaban Jam’iyyar ADC na ƙaramar hukumar mulki ta Argungu Alhaji Tukur JB ya gode wa Allah bisa ga wannan shugabancin da ya ba su, ya kuma yi alƙawarin kawo sauyi a fagen siyasa a ƙaramar hukumar mulki ta Argungu ta hanyar bai wa kowa damar aiwatar da aikin da ya rataya a wuyan sa kuma in sha Allahu za su yi aiki tare.
