05
Sep
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hedikwatar tsaro (DHQ) ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙin da ake yi da ta'addanci, 'yan fashi da sauran matsalolin tsaro a faɗin Nijeriya, inda ta bayyana cewa sojoji sun kashe 'yan ta'adda da dama, tare da cafke mutane 85 da ake zargi, tare da ceto mutane 66 da aka yi garkuwa da su a cikin watan Agusta. Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Markus Kangye, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin da yake zantawa da manema labarai kan bitar ayyukan rundunar na wata-wata. Dakarun Operation Haɗin Kai…
