03
Sep
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa ya amince da naɗa Tasi'u Dahiru PHD da Aminu Lawal Jibiya a matsayin masu bashi shawara kan ilimin almajiranci da na cigaban al'umma. Babban jami'in yaɗa labarai na gwamnan Muhammad kaula ya fitar da wannan sanarwa da aka rabawa manema labarai a Katsina. Tasi'u Dahiru wanda tsohon kwamishinan ayyuka ƙarƙashin gwamna Aminu Masari shine zai kasance mai ba gwamna shawara kan ilimin almajiranci da yaran da basa zuwa makaranta. Aminu Lawal Jibiya shine mai ba gwamna shawara kan cigaban al'umma,kafin nan ya taɓa riƙe muƙamin mai baiwa gwamna shawara…
