ukarofi

12738 Posts
Ƙaramar Hukumar Musawa ta yi sasanci da ‘yan bindiga a yankin

Ƙaramar Hukumar Musawa ta yi sasanci da ‘yan bindiga a yankin

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙoƙarin samar da zaman lafiya mai ɗorewa, a Jihar Katsina, ƙaramar hukumar Musawa tayi zaman sasanci da 'yan bindiga a yankin. Shugaban ƙaramar hukumar Musawa Hon. Aliyu Idris Gingin, Sarkin Musawan Hakimin Musawa Alhaji Sagir Inde, da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Musawa Hon. Lawal H. Yaro Away, da Alhaji Bala Abubakar Musawa da sauran shugabannin na ƙaramar hukumar Musawa suka jagoranci sasanciSu ka jagoranci sasanci da yan bindigar a dajin Tashar Mai Alewa dake cikin ƙaramar hukumar Ɗanmusa. Daga ɓangaren 'yanbindigan akwai Mannore, Kamilu Buzare, da Wada Yalo wanda shi ɗan asalin…
Read More
Matashi ya daddatsa matar ɗan uwansa a jihar Kwara

Matashi ya daddatsa matar ɗan uwansa a jihar Kwara

Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya, reshen jihar Kwara sun kama wani mutum mai suna Sylvester Enemo da zargin kashe wata mai ciki Esther Enemo a Ilorin babban birnin jihar. Rahotonni sun ce matashin mai shekara 29 ya daddatsa gawar matar mai shekara 39 ne, wadda kuma aka ce matar ɗan uwansa ce, bayan ya halaka ta a unguwar Temidire ranar Laraba. Mazauna yankin sun shaida wa manema labarai cewa mijin matar ya yi tafiya a lokacin da lamarin ya faru. "ƙarin bincike ya sa an gano sassan jikin matar da aka zuba a wani buhu kuma aka jefar a ƙarƙashin wata…
Read More
An kama dattijuwa da laifin safarar hodar iblis a juna biyu na ƙarya

An kama dattijuwa da laifin safarar hodar iblis a juna biyu na ƙarya

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) sun kama wata mai shekara 50 bisa zarginta da yunƙurin safarar hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1.3 ta hanyar amfani da ciki na ƙarya. An kama wacce ake zargin, Ifeoma Ezewuike a tashar mota da ke unguwar Jibowu, a unguwar Yaba kan hanyarta na safarar hodar zuwa Abuja. A nan gaba ne bayan an kammala bincike ne za a gurfanar da ita a gaban kotu.  Hukumar ta kuma bankaɗo fakiti 90 na wani nau'in tabar wiwi mai nauyin kilogiram 48.6 da aka ɓoye a cikin kwali uku na kwalayen…
Read More
Nana Asma’u da gudunmawarta wajen ci gaban addinin Musulunci a Nijeriya

Nana Asma’u da gudunmawarta wajen ci gaban addinin Musulunci a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rayuwa mai albarka. Kyawun ɗa, ya gaji mahaifinsa, in ji masu iya magana. Rayuwa tana da faɗi, saboda haka kowane mutum yana da irin gudunmawar da zai iya bayarwa bakin gwargwado. Madalla da rayuwar da ta yi kamanceceniya da ta ’yar Manzon Allah Nana Fatimatu a lokacin ƙuruciya da tasowa. Sannan kuma ta juya kamar rayuwar Nana A’isha matar Manzon Allah (dukkansu Allah ya ƙara musu yarda) a bayan aure da kuma rasuwar mahaifinta. Nana Asma’u, mace ce mai basira, himma, da kuma haziƙanci. Wannan baiwar Allah ta baiwa addininta na Musulunci gagarumar gudunmawa tun farkon…
Read More
Barka da zuwan maulidin bana

Barka da zuwan maulidin bana

Daga UNCLE LARABI “Mustapha manzona khatimul anbiya.” Wannan baitin amshin wata ƙasida ce da mu ke yi Lokacin Muna Yara a Makarantar Islamiyyarmu. Da yawan ’yan IzalaR yanzu duk mun yi Maulidi shekaru 30 da suka wuce.  Bayan Bikin Sallah Babba da Karama muna yara sai bikin Maulidi. Gaskiya an ci da rabon yaran yanzu. Idan watan Maulidi ya zo kusan kowanne gida sai an yanka kaji, wasu har raguna da shanu, ga soye-soyen su cincin da meat pie. Lokacin ba su pizza da doughnut. Sai dai su alkaki da dublan da algaragis da su bakilawa. Haka za a yi kunun…
Read More
Yadda NNPC ya kashe biliyan N235.6 a wata bakwai wajen neman mai a Arewa

Yadda NNPC ya kashe biliyan N235.6 a wata bakwai wajen neman mai a Arewa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin Fetur na Nijeriya (NNPC) ya cire zunzurutun kuɗi har Naira Biliyan 235.6 tsakanin watan Janairu zuwa Yulin 2025, don neman wuraren haƙo mai a arewacin Nijeriya, kamar yadda bayanan kuɗi na baya-bayan nan suka nuna. Jaridar News Point Nigeria ta bayar da rahoton cewa, an cire kuɗaɗen ne a ƙarƙashin Asusun Harkokin Man Fetur (FEF) kamar yadda dokar masana’antar man fetur (PIA) ta tanada, a ɓangaren karen kashi 30 cikin 100 na kuɗaɗen da aka ware don gano wuraren da mai yake. Wuraren da ake neman man sun haɗa da Basin Chadi, Tudun Binuwe, da…
Read More
Bunƙasa masana’antu: An sa dokar hana fita da wasu kayan amfanin gona daga Nijeriya

Bunƙasa masana’antu: An sa dokar hana fita da wasu kayan amfanin gona daga Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  A wani yunƙuri na bunƙasa masana’antun Nijeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da dokar hana fitar da ƙwallon kaɗanya wanda ake sarrafawa wajen samar da man kaɗe har na tsawon watanni shida.  Umurnin, wanda zai fara aiki nan take ya biyo bayan rahotannin tafka asara da Nijeriya ke yi sakamakon ficewa da ɗanyar kaɗanyar kafin sarrafawa, yin hakan a cewar gwamnatin zai daƙile kasuwanci mara riba da kƙarfafa masana’antun cikin gida. Mataimakin shugaban ƙasar, Kashim Shettima, wanda ya sanar da dakatarwar a yayin wani taron masu ruwa da tsaki, ya bayyana cewa matakin…
Read More
Nijeriya na buƙatar tiriliyan N1 duk shekara domin ɗorewar shirin ciyarwa a makarantu – Shettima

Nijeriya na buƙatar tiriliyan N1 duk shekara domin ɗorewar shirin ciyarwa a makarantu – Shettima

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa Nijeriya na iya buƙatar kimanin Naira Tiriliyan 1 a duk shekara don ci gaba da ɗaukar nauyin shirin ciyarwa a makarantu. Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne a Abuja a ƙarshen makon da ya gabata a yayin taron siyasa na ƙasa kan samar da tsari da aiwatar da shirin ciyar da yara ƙanana a gida da ƙungiyar ActionAid Nigeria ta shirya. Shettima wanda ya samu wakilcin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tattalin arziki, Dr. Tope Fasua, ya jadadda cewa, bai kamata a kalli shirin a…
Read More
Shirin ƙarin albashin ’yan siyasa na iya tada ƙura a Nijeriya – NLC

Shirin ƙarin albashin ’yan siyasa na iya tada ƙura a Nijeriya – NLC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Joe Ajaero, ya soki hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga da Raba Kuɗaɗen Shiga da kuma Kasafin Kuɗi (RMAFC) da nuna alamun ƙarin albashi ga masu riƙe da muƙaman siyasa. RMAFC ta bayyana cewa tana duba yiwuwar ƙarin albashi ta hanyar da za ta iya baiwa shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamnoni da sauran manyan jami’ai ƙarin albashi mai tsoka. A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Ajaero ya bayyana shirin a matsayin "rashin hankali da rashin adalci", yana mai gargaɗin cewa zai yi nasara ne kawai wajen ƙara zurfafa rashin…
Read More
Mutane 13 sun nutse a kogi, 22 sun ɓace yayin da suke tserewa daga farmakin ‘yan bindiga a Zamfara

Mutane 13 sun nutse a kogi, 22 sun ɓace yayin da suke tserewa daga farmakin ‘yan bindiga a Zamfara

Aƙalla mutane 13 ne suka mutu inda wasu 22 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ya kife a ƙaramar hukumar Gummi dake Zamfara ranar Juma’a da ta gabata. Rahotanni sun nuna cewar, Kwale-kwalen na ɗauke ne da mazauna ƙauyen Birnin Magaji a ƙaramar hukumar ta Gummi yayin da suke tserewa daga wani harin ‘yan bindiga da suka kai wa al’ummar garin da sanyin safiyar Juma’a. Malam Basiru Ibrahim da ke ƙauyen a wata hira da wakilin mu ta wayar tarho, ya bayyana cewar waɗanda lamarin ya rutsa da su, galibinsu mata ne da ƙananan yara daga Danmaga, Tungar Maigunya, da…
Read More