31
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar kare haƙƙin yara ta ƙasa tare da tallafin ƙungiyoyin SOS, UNICEF da ma’aikatar kula da mata da ci gaban al’umma ta jihar Zamfara sun gudanar da taron kwanaki biyu na masu ruwa da tsaki kan nazari da tabbatar da ƙa’idojin tattaro bayanan ingantattu da za a kula da su don kula da yara musamman marasa galihu a jihar. Da take jawabi yayin taron bitar a ranar Lahadi, kwamishiniyar ma’aikatar mata da ci gaban jama’a ta jihar, Dakta Aisha MZ ta bayyana ƙudurin gwamnatin jihar na yin haɗin gwiwa da duk wata ƙungiya mai zaman…
