31
Aug
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU A cikin makon da ya gabata ne aka gudanar da bikin Ranar Hausa a sassan duniya daban-daban, wanda aka shirya da nufin raya harshen Hausa da al'adun al'ummar Hausawa. An gudanar da wannan biki a jihohi da dama na arewacin ƙasar nan, har ma da maƙwaftan ƙasashe, inda ake da Hausawa masu yawa. Ana gudanar da wannan biki ne a kowacce ranar 26 ga watan Agusta, inda tsangayun ilimi a manyan makarantu da ƙungiyoyin Hausawa na raya harshe da al'adu, ke shirya bukukuwa daban-daban, da suka shafi raye-raye, waƙe-waƙe, baje-kolin abincin gargajiya da suturun Hausawa na…
