ukarofi

12738 Posts
Uba ya ɗaure ɗansa shekaru biyar bisa zargin tafiya babu izininsa

Uba ya ɗaure ɗansa shekaru biyar bisa zargin tafiya babu izininsa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Rundunar ‘yan sanda a Anambra ta ƙaddamar da bincike kan rahoton wani matashi da ake zargin mahaifinsa ya ɗaure shi da sarƙa tsawon shekaru biyar a Igboukwu da ke ƙaramar hukumar Aguata. Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Tochukwu Ikenga, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Awka. Ikenga ya bayyana cewa wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ɗansa ya fita ƙasar waje ba tare da izini ba, wanda hakan ya sa ya tsare shi bayan ya dawo. A cewarsa, kwamishinan ‘yan sanda, Ikioye Orutugu, ya umurci jami’an da su gaggauta…
Read More
An bankaɗo mambobin mafi kuzari da marasa kataɓus a Nijeiya

An bankaɗo mambobin mafi kuzari da marasa kataɓus a Nijeiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Aƙalla ’yan Majalisar Wakilai 48 da Sanatoci biyar ne suka gaza bayar da gudummuwarsu wajen muhawara, ɗaukar nauyin ƙudirori ko gabatar da ƙudiri da koke a zauren majalisun na tsawon watanni 12, a cewar wani sabon tantance ayyukan da aka fitar a ƙarshen mako. Sakamakon binciken yana ƙunshe ne a cikin Rahoton Bayar da Muhimmanci da Manufofin Majalisa (NASS-DBPFR), wanda Cibiyar Erudite Growth and Advancement Foundation (ERGAF-Africa) ta wallafa, inda ya bi diddigin ayyukan majalisa tsakanin 14 ga Yuni, 2023, da 13 ga Yuni, 2024. A cewar rahoton, ’yan majalisar ba su yi wani…
Read More
Ba zan tsaya takarar kowane muƙami ba a 2027 – El-Rufai

Ba zan tsaya takarar kowane muƙami ba a 2027 – El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce ba zai tsaya takarar kowanne irin muƙami ba a zaɓen 2027, inda ya ce burinsa kawai ya samar wa jiharsa da Nijeriya nagartattun shugabanni. Ya bayyana hakan ne ranar Laraba a Kaduna, lokacin da ya karɓi wasu matasa ƙarƙashin jagorancin Aliyu Bello da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar haɗakar ’yan adawa ta ADC. El-Rufa’i ya kuma soki lamirin gwamnati mai ci, inda ya ce ’yan Nijeriya na ganin gazawarta ƙarara ba tare da wani ya musu ƙarin bayani ba. “Ba abin da wannan gwamnatin ke…
Read More
Ƙungiyoyi sun nemi gwamnatin Tinubu ta saki jagoran Falasɗinawa da guje wa zama karen farautar Yahudawa

Ƙungiyoyi sun nemi gwamnatin Tinubu ta saki jagoran Falasɗinawa da guje wa zama karen farautar Yahudawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Kungiyoyin fararen hula a Nijeriya sun nemi a gaggauta sakin shugaban Falasɗinawa Ramzy Abu Ibrahim da mambobinsa ba tare da gindaya wani sharaɗi ba. Sun yi gargaɗin cewa kama su da aka yi ya saɓa wa tanadin kare haƙƙin ɗan’adam kuma ka iya jefa Nijeriya cikin rikicin Gabas ta tsakiya. Wannan saƙo na cikin wata sanarwa ta haɗin guiwa da Omotaje Olawale Saint na ƙungiyar WorkBond International Network (WIN) da Kunle Ajayi na ƙungiyar Wizeman of United Action for Democracy (UAD), suka sa wa hannu tare da amincewar sauran ƙungiyoyi da dama, inda suka…
Read More
Ruftawar katanga ya yi ajalin uwa da ’ya’yanta biyu a Zariya

Ruftawar katanga ya yi ajalin uwa da ’ya’yanta biyu a Zariya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Musiba ta auka wa wani gida a Zariya da ke Jihar Kaduna, bayan da katangar wani kango da ke maƙwabtaka da su ta faɗa wa mazauna gidan suna tsaka da barci. Wakilinmu ya ruwaito cewa, ruftawar ginin wadda ta auku a safiyar wannan Larabar ta yi ajalin matar gidan, Habiba Nuhu da ’ya’yanta biyu, Hauwa’u da Aina’u Nuhu. Sai dai mijinta, wanda shi ma ya samu rauni a sakamakon faruwar lamarin, tuni an sallamo shi bayan duba lafiyarsa a asibiti. Wani maƙwabcinsu, Malam Ahmed, ya shaida wa Manhaja cewa lamarin ya faru ne da…
Read More
ADC ta zargi Gwamna Nasir da takardun karatu na bogi 

ADC ta zargi Gwamna Nasir da takardun karatu na bogi 

Daga JAMIL GULMA a Kebbi  Jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) reshen jihar Kebbi ta zargi gwamnan jihar Malam Nasir Idris da amfani da takardun bogi da ya ce ya yi karatu a waɗansu makarantu da ana tunanin ba gaskiya ba ne. Wannan yana ƙunshe ne a wata takarda mai ɗauke da sa hannun Engr Abubakar Atiku Musa sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar jiya Alhamis 28 ga Agusta, 2025. Takardar ta bayyana jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), reshen Jihar Kebbi, ta lura da damuwa game da rashin tabbas da ke tattare da bayanan karatun Gwamna Nasir Idris kamar yadda aka bayyana…
Read More
Laifina kaɗai shine gyara ɓangaren man Nijeriya, inji shugaban NNPC

Laifina kaɗai shine gyara ɓangaren man Nijeriya, inji shugaban NNPC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar Alhamis ne Babban Jami’in Rukunin Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL), Bayo Ojulari, ya nesanta kansa daga siyasantar da ɓangaren mai, inda ya ce ya mayar da hankali wajen yin garambawul da kuma farfaɗo da matatun man ƙasar. Ojulari ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karɓar tawagar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Nijeriya (PENGASSAN), ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Festus Osifo, a hedikwatar kamfanin da ke Abuja. "Ni ba na ɓoye wa kowa komai. Ni ba ɗan siyasa ba ne, amma na fahimci akwai buƙatar na ƙara koyon wasu dabaru na siyasa.…
Read More
Gwamnatin Kaduna ta ƙaryata saka jihar cikin jihohin da suka fi fama da garkuwa

Gwamnatin Kaduna ta ƙaryata saka jihar cikin jihohin da suka fi fama da garkuwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da wani rahoto da ta bayyana jihar a cikin jerin jihohin da aka fi satar mutane a faɗin ƙasar, inda ta bayyana hakan a matsayin "ƙarya, ɓarna da shaci-faɗi." Wata sanarwa da ma’aikatar yaɗa labaran ƙasar ta fitar a ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun kwamishinan yaɗa labarai, Malam Ahmed Maiyaki ta miƙa wa kamfanin dillancin labarai, ta yi Allah-wadai da wani rahoto da aka alaƙanta wa SB Morgen wanda ya yi zargin cewa an yi garkuwa da mutane 629 a Kaduna tsakanin Yuli 2024 zuwa Yuni…
Read More
Saudiyya za ta fara ɗaure maniyyatan da suka zo ta ɓarauniyar hanya

Saudiyya za ta fara ɗaure maniyyatan da suka zo ta ɓarauniyar hanya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Masarautar Saudiyya ta gargaɗi alhazai ‘yan Nijeriya da ke shirin zuwa Hajjin shekarar 2026 cewa duk wanda aka kama yana gudanar da ibadar Hajj ba tare da ingantacciyar Biza ta Hajj ba, zai fuskanci tara har Riyal 20,000 (kimanin Naira Miliyan 8.15) tare da ɗaurin gidan yari. Gargaɗin ya fito ne yayin taron tattaunawa ta yanar gizo tsakanin Hukumar Hajji ta ƙasa (NAHCON) da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya domin duba shirin hajjin na baɗi. Dr. Rania Adham daga Ma’aikatar Hajji ta Saudiyya ce ta jagoranci zaman. A wata sanarwa da NAHCON ta…
Read More
Gwamnan Imo ya ƙara mafi ƙarancin albashi daga N76,000 zuwa N104,000

Gwamnan Imo ya ƙara mafi ƙarancin albashi daga N76,000 zuwa N104,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya amince da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa Naira 104,000 ga ma’aikatan gwamnati a jihar. Uzodimma ya bayyana hakan ne a lokacin wata ganawa da shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago a daren Talata a fadar gwamnatin jihar da ke Owerri. A cewar jaridar Manhaja, kuma kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN) ya ruwaito, an ƙara mafi ƙarancin albashin daga Naira dubu 76  zuwa Naira dubu 104. Haka kuma, ya sanar da ƙarin mafi ƙarancin albashi na likitoci daga Naira dubu 215 zuwa Naira dubu 503,  yayin da na malamai…
Read More