ukarofi

12738 Posts
Kotu ta ƙwace miliyan N246 daga hannun wani janar bisa zargin almundahana

Kotu ta ƙwace miliyan N246 daga hannun wani janar bisa zargin almundahana

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Ikoyi, Legas, ta bayar da umarnin kwace kuɗaɗen da suka haura Naira Miliyan 246 daga hannun wani Janar na Sojojin Nijeriya (mai ritaya), Manjo-Janar U.M. Mohammed, ga Gwamnatin Tarayya. Hukuncin, wanda aka zartar a ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025, daga Mai Shari'a Dehinde Dipeolu, ya biyo bayan ƙudirin sanarwa ne da ofishin shiyyar Legas 2 na Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Zagon ƙasa (EFCC) ya gabatar. Takardun kotun sun bayyana cewa kadarorin da aka kwace kuɗinsu ya kai N246,305,544, waɗanda aka gano a…
Read More
An ɗaure Sarkin Ipetumodu na Osun a Amurka kan karkatar da kuɗaɗen tallafin Korona

An ɗaure Sarkin Ipetumodu na Osun a Amurka kan karkatar da kuɗaɗen tallafin Korona

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kotun Amurka ta yanke wa Sarkin gargajiya daga Jihar Osun, Oba Joseph Oloyede, wanda ake kira Apetu na Ipetumodu, hukunci bayan kama shi da laifin karkatar da kuɗaɗen tallafin annobar cutar Korona. Hukuncin ya biyo bayan shigar da ƙarar da ofishin babban lauyan gwamnatin Amurka a Jihar Ohio ya yi, inda aka tabbatar da cewa, ya jagoranci aikace-aikacen bogi, domin karɓar tallafin da Gwamnatin Amurka ta ware, amma tallafin da ya karɓa ya karkatar ne ga ‘yan kasuwa da ƙungiyoyi a lokacin ɓarkewar annobar cutar ta Korona. Rahoton ofishin lauyan Amurka ya ce tsakanin Afrilun 2020…
Read More
TISNI ta tsara tallafa wa ɗaliban da suka kammala jami’a – Maryam Bichi

TISNI ta tsara tallafa wa ɗaliban da suka kammala jami’a – Maryam Bichi

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Kungiyar masu mallakar kamfanonin kasuwanci da kamfanonin fasahar sadarwa da makamantansu da ake kira Technology Innovation & Solution Network Initiative (TISNI) ta samar da tsari irinsa na farko ta yadda ɗaliban da suka kammala jami'a da manyan makarantu za su ci gajiyar rubutunsu na kammala karatunsu da ake kira project, wanda shi ne TISNI ta tsara horar da su da tallafa musu ta hanyar jagoranci da wannan rubutun na ɗalibai zai samawa waɗannan ɗalibai aiki na dogaro da kai, kamar dai yadda Hajiya Maryam Abbas Abdulƙadir Bichi, shugabar hulɗa da jama’a da kuma yaɗa labarai…
Read More
Ganduje shugaba ne da ba ya aikata cin hanci – Muhammad Garba

Ganduje shugaba ne da ba ya aikata cin hanci – Muhammad Garba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Muhammad Garba, babban hadimin tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ƙaryata zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa jagoransa. Ya bayyana wannan zargi a matsayin yarfe na siyasa don ruɗar da jama’a. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Garba wanda tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai ne a jihar, ya ce ba gaskiya ba ne cewa Ganduje ɗan siyasa ne mai cin hanci kamar yadda magajinsa ya yi iƙirari. A cewarsa, Ganduje ya shugabanci jihar cikin gaskiya, amana, da bin ƙa’ida tare da aiwatar da manyan ayyuka a…
Read More
Ya kamata a kyautata jin daɗin al’umma maimakon ƙara wa ‘yan siyasa albashi, inji Danpass

Ya kamata a kyautata jin daɗin al’umma maimakon ƙara wa ‘yan siyasa albashi, inji Danpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana batun ƙarawa zaɓaɓɓu masu riƙe da muƙaman siyasa albashi musamman daga kan shugaban ƙasa, gwamnoni da 'yan majalisu da na sauran matakai da cewa ba abin da ya kamata  ba ne a cikin wannan yanayi da al'ummar ƙasar nan talakawa ke cikin mawuyacin hali. ɗansaran Kano, Alhaji Gambo Muhammad ɗanpass ne ya bayyana hakan, yace mutane na cikin matsalolin yadda Gwamnatin Tarayya take tafiyar da su don haka hukumar da ke neman ƙara albashi ga 'yan siyasa ta sauya shawara. Ya ce da ana yin abin da ya dace kowa a ƙasar nan…
Read More
’Yar shara ta maida miliyan N4.8 da aka yi kuskuren sakawa a asusunta

’Yar shara ta maida miliyan N4.8 da aka yi kuskuren sakawa a asusunta

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wata baiwar Allah mai shara a cibiyar kiwon lafiya, Faiza Abdulkadir ta sake nuna wa duniya cewa har yanzu akwai sauran masu gaskiya. Fa'iza da ke karɓar albashin N30,000 a wata, ta mayar da miliyan N4.8 da aka tura cikin asusun bankinta da kuskure a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. Dan uwan matar, Ibrahim Muhammad AbdulRahman ne ya tabbatar da haka a shafinsa na Facebook, ya ce duk da ƙuncin rayuwa da ta ke fama da shi, ba ta riƙe kuɗin ba. Da take magana da manema labarai, Faiza ta bayyana cewa tsoron Allah ne ya…
Read More
ECOWAS na shirin kafa rundunar yaƙi da ta’addanci mai dakaru 260,000

ECOWAS na shirin kafa rundunar yaƙi da ta’addanci mai dakaru 260,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka ta ECOWAS ta bayyana shirinta na kafa rundunar yaƙi da ta’addanci mai ɗauke da sojoji 260,000 domin tunkarar barazanar tsaro da ke ƙara ta’azzara a yankin. Shugaban ECOWAS, Omar Alieu Touray, wanda wakilinsa Abdel-Fatau Musah ya gabatar da jawabi a taron shugabannin rundunonin tsaro na Afirka da aka gudanar a Abuja, ya ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin daƙile ayyukan ta’addanci da sauran matsalolin tsaro da suka addabi yankin. “Babu wani yanki a Afirka da ya tsira daga ta’addanci, rikice-rikicen cikin gida da kuma koma-baya ta fannin…
Read More
Rundunar sojin Nijeriya ta ceto yara da dama bayan ragargaza maɓoyar ‘yan ta’adda

Rundunar sojin Nijeriya ta ceto yara da dama bayan ragargaza maɓoyar ‘yan ta’adda

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar sojin Nijeriya a ranar Juma’a ta yi nasarar ceto mutane 76 kuma mafi yawancinsu yara ne bayan hare-hare da ta kai ta sama maɓoyar ‘yan bindiga da ke Katsina. Sai dai yaro ɗaya a cikinsu ya rasu. Rudunar sojin saman Nijeriya ce ta kai wani samame a ranar Juma’a da yamma kan maɓoyar gungun ɗan ta’adda Babaro da ke tsaunin Pauwa, a garin ƙanƙara. Wannan hare-hare martani ne na irin mummunan harin gungun ‘yan bindiga Gidan Mantau suka kai da sace mutane da dama. Kwamishinan tsaro na cikin gida, Nasir Mu’azu, ne ya…
Read More
Hukumomin Nijeriya sun kama shugaban al’ummar Falasɗinawa mazauna Nijeriya a Abuja

Hukumomin Nijeriya sun kama shugaban al’ummar Falasɗinawa mazauna Nijeriya a Abuja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Jami’an tsaron Nijeriya sun kama shugaban al’ummar Falasɗinawa a Nijeriya, Ramzy Abu Ibrahim a Abuja ranar Juma’a. Wani ɗan uwa ya shaida wa SaharaReporters cewa jami’an sun kama Abu Ibrahim daga gidansa da ke Babban Birnin Tarayya (FCT), kuma har yanzu ba a sanar da iyalan inda aka kaisu ko kuma dalilin tsarewarsa ba. Jami’an da suka bayyana kansu a matsayin na anti-terrorism sƙuad, a cewar ‘yan uwansa. Jami’i a ofishin jakadancin Falasɗinawa da ke Abuja ya tabbatar da cewa suna da masaniya kan lamarin, amma har yanzu suna ƙoƙarin samun cikakkun bayanai. “Eh,…
Read More
Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Nijeriya – Tinubu

Tun da na hau mulki cin hanci ya zama tarihi a Nijeriya – Tinubu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tabbatar wa masu saka hannun jari na ƙasar Brazil cewa gyare-gyaren tattalin arzikin da ake aiwatarwa a Nijeriya suna samar da ingantattun sakamako, inda ya yi iƙirarin cewa “ba a sake samun cin hanci da rashawa ba” tun bayan da ya hau kujerar shugaban ƙasa. Jaridar Tribune ta rawaito cewa Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin wani taro da aka gudanar a ranar Litinin tare da ministoci daga ƙasashen biyu da kuma mambobin ƙungiyar kasuwanci ta Brazil, inda ya sake jaddada shirye-shiryen Nijeriya na ƙarfafa haɗin gwiwa…
Read More