Ba a biya mu kuɗin aikin zaɓen 2023 ba, cewar wasu masu aikin wucin-gadi na INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wasu daga cikin ma’aikatan wucin-gadi da suka yi aikin zaɓen 2023 a Nijeriya sun koka kan rashin biyan su kuɗaɗen alawus-alawus na aikin da suka yi.

Ma’aikatan waɗanda suka ce suna da yawan gaske a faɗin ƙasar sun nemi Hukumar Zaven, INEC ta taimaka ta biya su haƙƙoƙinsu.

A watannin Fabarairu da kuma Maris ɗin shekarar 2023 ne aka gudanar da zaɓukan Shugaban Ƙasa da na ‘yan majalisu da kuma gwamnoni a Nijeriyar.

Ɗaya daga cikin irin waɗannan ma’aikatan na wucin-gadi daga jihar Kano ya shaida wa BBC cewa a jihar kaɗai akwai abokan aikinsa 80 waɗanda ba a biya su ba.

“Mun rasa gane abin da yake faruwa, daga cikinmu akwai waɗanda ba a biya alawus ɗin aikin zaɓen Shugaban Ƙasa ba akwai kuma wasu waɗanda na gwamnoni ne ba a biya su ba.

Wasu sun yi ƙoƙarin gano abin da ke faruwa amma sai aka faɗa musu wai matsalar ta shafi duk mutane da lambobin asusun ajiyarsu na banki ya fara da “0” ne suka samu matsalar;

To sai dai kuma wasu masu irin wannan asusun sun yi aikin zaɓen Shugaban Ƙasa kuma an biya su,” a cewar ma’aikacin wucin-gadin na INEC.

Ya ce ƙara da cewa ba su fahimci yadda wannan matsalar ta shafi biyansu haƙƙoƙinsu ba.

Shi ma wani ma’aikacin na wucin-gadi da har yanzu ya ce bai karɓi kuɗin aikinsa ba, ya ce a zaven 2019 ma akwai wasu da irin wannan matsalar ta shafa kuma har yanzu ba a biya su ba.

“Akwai wasu abokaina waɗanda na sani har yanzu ba su samu kuɗinsu ba tun zaɓen 2019 don haka mu ma muna fargaba kar kuɗaɗenmu su maƙale” inji matashin.

Ita ma wata matashiya da ta yi aikin zaɓen na wucin-gadi ta ce ko da kuɗin horo da ake bayarwa ma ba ta samu ba a aikin da ta yi na zaben gwamna da kuma na shugaban kasa.

BBC ta tuntuɓi shugaban hukumar INEC reshen jihar Kano Ambasada Abdul Zango kan wannan batun kuma ya ce mutane ƙalilan ne matsalar ta shafa.

“Mun biya kashi 96 cikin ɗari na kuɗaɗensu saura kashi 4 da ba a biya ba sun samu matsalar asusun ajiya ne.

Wasu ba su bada lambobin asusun ajiyarsu ba sai dai na abokai ko ‘yan uwansu, kuma da yake da na’ura ake biya, idan ta samu sunan jikin asusun ajiyar kuɗi bai tafi daidai da sunan mutumin da ya yi aikin zaɓen ba kuɗin ba za su shiga ba,” a cewar Ambasada Abdul.

Ya kuma ƙara da cewa hukumar zaɓe ba za ta ji daɗi ba ko da kuwa mutum ɗaya ne ba a biya shi kuɗin aikinsa ba.

“Duk wanda ba a biya ba ya shigar da ƙorafinsa zuwa ga hukumar zaɓe domin a shigar da sunansa cikin kundin bayanai da ake tattarawa domin mun kafa wani kwamiti da zai warware wannan matsalar zuwa ƙarshen watan Mayun shekarar nan ta 2023.

Dukkan waɗanda BBC ta yi magana da su sun buƙaci hukumar zaven ta INEC ta biya su haƙƙinsu saboda a cewarsu aiki suka yi na sayar da rayukansu.

Baya ga jihar Kano, akwai wasu ma’aikatan daga jihohin Nijeriya da dama waɗanda suka ce har yanzu su ma ba a biya su ba.