Rikici ya ɓarke a Majalisar Wakilai kan zargin karkatar da maƙudan kuɗaɗe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mambobin Majalisar Wakilai na shirin yin kaca-kaca da Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila bisa zargin karkatar da wasu maƙudan kuɗaɗe da suka kai dala miliyan 15 daga ɓangaren zartarwa na gwamnati.

’Yan majalisar da suka fusata sun yi zargin cewa Gbajabiamila ya ƙulla yarjejeniya da ɓangaren zartaslrwa a madadin majalisar na zartar da hanyoyin da za a bi wajen karɓo bashi daga babban bankin Nijeriya (CBN) na Naira tiriliyan 22.7, amma sai ya gajarce daga abokan aikinsa wajen raba dala miliyan 15 da aka bai wa Majalisar don jin daɗin yarjejeniyar.

Rikicin da ake fama da shi, kamar yadda aka gano, ya tilastawa Gbajabiamila ɗage ci gaba da zaman majalisar wanda tuni aka shirya ranar Talata domin a samu ƙarin lokaci da kuma kwantar da hankulan mambobin da ke cikin rikicin.

Kakakin majalisar ya ɗage zaman majalisar ne bisa fakewa da cewa an bayyana ranar ne bisa kuskure.

Magatakardar Majalisar, Yahaya Danzaria, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, ya ce, “Wannan na sanar da ɗaukacin ’yan majalisar da sauran jama’a cewa majalisar wakilai ba za ta dawo zamanta a ranar Talata 16 ga Mayu, 2023 kamar yadda aka sanar a baya ba. Ranar Laraba na gaba zai kasance Laraba 17 ga Mayu, 2023 da ƙarfe 11:00 na safe. Da fatan za a yi watsi da sanarwar farko da kwanan wata; an yi shi a cikin kuskure.”

Sai dai ba a sani ba ko hakan ka iya kwantar da rikicin da ke neman ɓullo kai.

Majalisar a ranar Talata, 31 ga watan Janairu, ta bai wa shugaban ƙasa izinin ciyo sabon bashin Naira tiriliyan 1 daga babban bankin Nijeriya (CBN) don ciyar da ƙarin kasafin kuɗin shekarar 2022. Yayin da majalisar ta amince da sake fasalin Naira tiriliyan 1, ’yan majalisar sun yi watsi da buƙatar Naira biliyan 22 daga CBN.

Bayan tattaunawa da yawa da mambobin kwamitocin majalisar da abin ya shafa da sauran masu ruwa da tsaki, Gbajabiamila ya amince majalisar ta amince da buƙatar a ranar Alhamis, 4 ga watan Mayu.