Yarima Harry na Birtaniya da matarsa sun tsallake rijiya da baya

Yarima Harry da matarsa Meghan sun tsallake rijiya da baya a lokacin da motarsu ta kusa yin taho mu gama da wasu motocin, sa’ilin da masu ɗaukar hoto ke bin su a mota.

Lamarin ya faru ne a lokacin da yariman da matarsa suka bar wurin wani bikin bayar da kyatuka a birnin New York na Ƙasar Amurka.

Wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun yariman, ta ce masu faukar hoton sun rinƙa bin ma’auratan a guje cikin mota har tsawon kusan sa’a biyu.

Sanarwar ta ce, hakan ya sanya motar da suke ciki ta kusa kara wa wasu motocin, da kuma masu tafiya a ƙafa har ma da ƴan sanda.

Rundunar ƴan sanda ta birnin New York ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba tun farko.

Wannan al’amari ya faru ne a lokaci na farko da aka ga ma’auratan tun bayan bikin naɗin sarautar mahaifin Harry, Sarki Charles III na Ingila a farkon wannan wata.

Al’amarin ya faru ne a lokacin da Harry da Meghan suke tare da mahaifiyar Meghan, wadda ta raka su wurin bikin bayar da kyautuka na ‘Ms Foundation Women Vision.’

Mahaifiyar Yarima Harry, gimbiya Diana ita ma ta rasa ranta ne a haɗarin mota a shekarar 1997 a birnin Paris, lokacin da masu ɗaukan hoto ke bin ta a cikin mota.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *