Ba a sauya wa Jihar Kaduna suna ba – Gwamnatin Jihar

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi watsi da rahoton da ya ce ta sauya wa jihar suna zuwa Jihar Zazzau.

Mai ba da Shawara na Musamman ga Gwamnan Kaduna kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, shi ne ya yi watsi da rahoton a madadin Gwamnatin Jihar cikin wata sanarwa da ya fitar ran Talata, yana mai cewa labarin ba gaskiya ba ne.

Adeleke ya bayyana rahoton a matsayin na bogi, tare da kira ga al’ummar jihar da su yi watsi da labarin.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito wasu kafafen yaɗa labarai a intanet sun ce, wai Majalisar Tarayya ta Ƙasa ta amince da dokar sauya wa Jihar Kaduna suna wanda har ta tura Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan ga Shugaba Buhari don sanya wa dokar hannu.

Kazalika, rahoton ya nuna
Sanata Suleiman Abdu Kwari da takwaransa Sanata Uba Sani mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya ne suka mara wa ƙudurin baya, tare cewa sun samu amincewar ‘yan majalisa 13 daga cikin 15 da suka fito daga sassan Kaduna kan batun sauya wa jihar suna.

Da yake maida martani kan batun, Sanata Uba Sani, ya shaida wa NAN cewa rahoton ba komai ba ne face tsagwaron ƙarya.

Ya ƙara da cewa, dokar da aka ce shi da Sanata Sulaiman Abdu Kwari sun mara wa baya, ba gaskiya ba ne.

Sanata Sani ya bayyana mamakinsa dangane da yadda wasu mutane za su zauna sannan su tsara abin da zai haifar wa jiharsu tashin-tashina da kuma tsananta matsalar tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *