Ba ma zawarcin Jonathan a takarar 2027 – PDP

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Babbar jam’iyyar hamayya a Nijeriya, PDP, ta ce babu ƙanshin gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa cewa ta nemi tsohon shugaban ƙasar, Dokta Goodluck Ebele Jonathan da ya tsaya mata takarar kujerar shugabancin ƙasar a shekara ta 2027.

Jam’iyyar ta ce tana ta ganin ana yaɗa wannan batu, sai dai labarin babu gaskiya a ciki.

Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Ibrahim Abdullahi, shi ne ya musanta wannan labari a tattaunawarsa da BBC.

Kakakin ya ce: ”To abin da ke gaskiya shi ne ba rahoton gaskiya ba ne na cewa jam’iyyar PDP ta miƙa tiket ɗinta na takarar shugaban ƙasa zuwa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ko tana kira da ya zo ya yi takarar a 2027 mai zuwa.

Abdullahi ya ƙara da cewa: ”Abin da ya faru ni ne ɗin nan na yi hira da ɗan jarida, hirar da muke a kan wasu maganganu daban, sai a cikin hirar ya ambato tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan cewa mene ne tunaninmu a kansa?

”Ana kira kwanan nan na ya zo ya yi takarar shugaban ƙasa. ‘Yan Nijeriya na kira. Shi ne na amsa masa da cewa babu shakka ya cancanci ya yi ɗin tun da ɗan Nijeriya ne kuma yana da damar ya yi haka a fuskar doka kuma yana da wa’adi ɗaya na takarar shugaban ƙasa. So fitowarsa ya yi takara ba illa ba ne a zaman shi an Nijeriya kuma babu abin da ya hana shi yin haka a idon doka,”‘ inji kakakin.

Ya ƙara da cewa ta yaya ma za a ce sun yi zawarcin mutumin da daman shi dan jam’iyya ne – wanda jam’iyyar ce ya ce ta yi wa Jonathan din riga ta yi mishi wando.

Alhaji Abdullahi ya ce, su ko magana da Jonathan ɗin ba su yi ba a kan takara, kuma ba su karkata akalarsu cewa sai shi kaɗai zai iya yin takara a jam’iyyar ta PDP ba.

Ya ce suna da gwamnoni 12 a yanzu haka, sannan suna da waɗanda za su iya yin takarar ta shugaban ƙasa da dama, waɗanda kuma ‘yan siyasa ne fitattu.

Sai dai gamin yadda jam’iyyar take fama da rarrabuwar kai da matsaloli na cikin gida da kan bijiro a lokacin neman takara, wasu na ganin tsohon shugaban ƙasar ka iya zamar wa jam’iyyar dan takara na maslaha.

A kan haka, ya ce ba shakka tsohon shugaban ƙasar yana da ta shi fa’idar idan da zai yi.

To amma a cewarsa jam’iyya ba za ta zauna zaman jiran mutum ɗaya ba, wanda kuma mutumin nan ya ce idan ba a manta ba shi ne wanda jam’iyyar APC ta riƙa zaraci da karkata akalarta wajen ƙoƙarin ta kira shi ya yi mata takara lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya kare wa’adinsa.

”A gaskiyar magana inda zai yi takarar da kuma jam’iyyar za ta ba shi takarar lalle zai iya, to amma matsalar ba a ba mutum irin wannan matsayi a zaune za ka fito ne ka nuna ra’ayinka ka nuna kwaɗayinka a kanshi,” inji shi.

Mai magana da yawun jam’iyyar ta PDP ya ce, duk wadannan maganganu ma da ake yi shi kansa tsohon Jonathan ɗin bai nuna sha’awarsa da takarar ba.

”Idan ma ba a manta ba, ba da daɗewa ba, kwanan nan matarsa ta fito ta ce babu abin da zai sa shi ya dawo ya sake neman shugaban ƙasa, babu abin da ya manta a bila balle ma a yi tunanin ya dawo neman shugaban ƙasa,” inji shi.

Ya ce: ”To shikenan mu kuma jam’iyyar PDP don mun fi kowa maita sai mu ce sai shi.”

Kakakin ya yi tutiya da cewa, ita jam’iyyar PDP ko ka yarda a yi da kai ko ka yi tafiyarka za ka dawo ka ganta.

Ya ce, tun da aka kirkiro ta har yanzu ita kaɗai ce ba ta canza sheka, ba ta canza ka, ba ta canza yanayinta ko sunanta ko aƙidarta ba, a tsakanin jam’iyyun Nijeriya.

Har ma ya ƙara da cewa ita ce jam’iyyar da ta fi kowace jam’iyya daɗewa a tarihin Nijeriya.

By ukarofi