Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Zaɓaɓɓen Shugaban ƙaramar Hukumar Doguwa a Jihar Kano, Hon. Abdulrashid Rilwan ya bayyana cewa abinda suka sa a gaba a yanzu a shugabancin ƙaramar hukumar shine su tabbatar da haƙƙin al’ummar Doguwar yana zuwa gare su ana yi musu ayyukan bunƙasa cigabansu.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a Kano ya yi nuni da cewa akwai ƙalubale da yawa da suke fuskanta a Doguwa na rashin ayyukan cigaba da ake fama dasu a yankin sakamakon ana turo tarin haƙƙoƙinsu na ƙaramar hukumar amma saboda azzalumai da Allah ya ya haɗa su dasu sun mallake suna riƙewa a matsayin nasu ba sa ayyuka da za su inganta rayuwar al’umma.
Hon. Abdulraahid Rilwan ya ce a tsawon lokacin nan da aka dawo na mulkin Damakwaraɗiyya a ƙasar nan an turo da abubuwa na kason arziƙi masu ɗinbin yawa da yakamata a raya cigaban yankin amma waɗannan mutane da ke ci da gumin yan yankin basa hidimtawa al”umma dasu.
Ya ce zuwan su yanzu da yardar Allah gwargwadon hali da iko za su saka ɗan ba na kyautata cigaban yankin ta farawa da bunƙasa harkar ilmi da raya ƙasa suna kuma da yaƙinin na sanin zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf zai basu dukkan goyon baya da gudunmuwa da zasu tabbatar sun yi aiki na raya ƙasa da raya cigaban al’ummar karamar hukumar Doguwa domin duk mutumin da ka taimake shi ka raya shi da al’ummar sa shima akwai kyakkyawan zato zai rama alkhairi da alkhairi.
Hon. Abdulrashid Rilwan ya ce za su tabbatar dukkan tsare- tsare na kwankwasiyya sun yi aiki da tabbatar dasu domin in an bi tsarin al”ummar Doguwa za su ji daɗi da farin ciki.Duk da cewa sun zo sun sami tarin matsaloli a ƙaramar hukuma sakamakon Allah ya tara musu wasu da basa kishin al’umma da son cigaban su sakamakon ƙaramar hukumar ta yi nisa da cikin birni
Ya ce domin a da al”ummar Doguwa basa samun dama da za su bayyana ra’ayinsu domin a ɗauki mataki na gaggawa shi yasa mutane marasa kishin da suke kwace musu zaɓe in sun yi suka sami dama suke danne haƙƙin al’umma a Doguwa
Shugaban ƙaramar Hukumar Doguwa, Hon. Abdulrashid Rilwan ya godewe jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da ya girmama dan asalin yankin su Umar Haruna Doguwa na bashi dama yake hidimtawa a Gwamnatinsa
Hon. Abdulrashid Rilwan Doguwa ya ce wannan dama da ake basu amana ce tasa domin duk dan ƙaramar hukumar Doguwa in dai ba mara daraja ba zaka sane shi mai amana da halacci suna saka alkhairi da alkhairi , duk wanda ya yi musu babban burinsu su saka masa shi yasa suke jinjina ga jagoransu na kasa a siyasa Dakta Rabiu Musa Kwankwaso domin wannan irin tarbiyya da ya basu kenan suke nunawa a koyaushe.
