Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsare na Tattalin Arziki, Sanata Atiku Bagudu, ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke yi a cikin shekaru biyu da suka gabata, sun sanya tattalin arzikin Nijeriya ta kai inda ba a zata ba.
Sanata Bagudu ya yi wannan magana ne a daren ranar Asabar jim kaɗan bayan ziyarar ban girma ga shugaba Tinubu a gidansa da ke Legas.
Ya yaba da manufofin tattalin arziki na gwamnatin, inda ya ƙara da cewa Nijeriya ta fara ganin alfanun sauye-sauyen shugaban Tinubu, wanda aka daɗe ana jira.
Ya ce, “Ba mu kasance inda muke so ba, amma waɗannan matakan sun karkatar da tattalin arzikin ƙasar zuwa kan hanyar da ta dace.”
A cewar ministan, “Shekaru goma da rashin zuba jari ya kawo Nijeriya a matsayin da ko biyan albashi na neman gagara.
“Ta hanyar yanke waɗannan tallafin, mun fitar da albarkatu. A yau, ƙananan hukumomi da jihohi sun ruɓanya kuɗaɗen da suke da su a baya. Al’amura sun canja.”
Ya ce, ana karkatar da kuɗaɗen zuwa sassa masu muhimmanci kamar kayayyakin more rayuwa, noma, basussukan masu amfani, ƙirƙire-ƙirƙire na dijital, da bunƙasa jarin ɗan Adam.
Ministan ya ce: “Waɗannan ba alƙawura ba ne, muna ganin ainihin kason da aka ware don samar da tsaro, ilimi, da ƙarfafa tattalin arziki.”
Ya ce, “ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke banbance tsakanin ƙasashen da suka ci gaba da masu tasowa shi ne matakin zuba jari, na gwamnati da na masu zaman kansu, yanzu muna gyara koma-bayan da aka samu a shekaru.
“Akwai babban koma-baya na masu zaman kansu, na cikin gida da na waje, masu saka hannun jari sun sake ɗaukar Nijeriya da muhimmanci, suna ganin gwamnatin da ke ɗaukar tsauraran matakai.
Da yake tsokaci kan yadda ‘yan siyasar adawa ke ƙaruwa zuwa jam’iyyar APC, ya ce hakan ya faru ne sakamakon shugabancin Tinubu.
Ministan ya ce: “Sun bayyana a bainar jama’a dalilin da ya sa suka sauya sheƙa, saboda gaskiya da alƙiblar wannan shugabanci. Wannan ba siyasa ba ce. Wannan hanya ce da ake ginawa da jajircewa da hangen nesa.”
Ya kuma ba da tabbacin cewa, “sabuwar gwamnati na aiki, zuba jari na ƙaruwa, duk da ƙalubalen da ke addabar ƙasar.”
