Ba takardar digiri kaɗai ake buƙata a jami’a ba – Shettima

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya ce lokaci ya yi da jami’o’in Nijeriya za su sauya salon aikinsu ta hanyar zama cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci da bunƙasa masana’antu, maimakon mayar da hankali kan fitar da masu takardun shaida kawai.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da cibiyar Manufacturing Technology Uniɓersity Innoɓation Pod (Manu-Tech UniPod) a Jami’ar Noma ta Michael Okpara da ke Umudike, ƙaramar hukumar Ikwuano a Jihar Abia. An kafa cibiyar ne domin haɓaka ƙirƙire-ƙirƙire a fannin fasaha da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci.

Shirin haɗin gwiwa ne tsakanin Shirin Raya ƙasashe na Majalisar ɗinkin Duniya (UNDP) da Gwamnatin Tarayya ta hannun Asusun Tallafa wa Manyan Makarantu (TETFund).

Da yake jawabi ta bakin Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, Shettima ya ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Sabuwar Fata, waɗanda suka fi mayar da hankali kan ilimi, ƙirƙire-ƙirƙire, bunƙasa masana’antu, ƙarfafa matasa da faɗaɗa tattalin arziki.

Ya bayyana cewa, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya na aiwatar da shirin farfaɗo da fannin ilimi domin ƙarfafa ilimin asali, koyar da sana’o’in zamani, fasahar dijital, bincike da samar da sabbin kasuwanci. A cewarsa, jami’o’in ƙarni na gaba dole ne su riƙa fitar da masu ƙirƙire-ƙirƙire, ‘yan kasuwa, masu ƙirƙirar kayayyaki, masana’antun cikin gida da masu samar da ayyukan yi. Ya ƙara da cewa, cibiyar za ta haɗa masu bincike, masana’antu da ‘yan kasuwa, tare da taimakawa burin gwamnatin tarayya na gina tattalin arzikin da darajarsa za ta kai dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Abia, Aleɗ Otti, ya ce haɗin gwiwar da aka kafa tsakanin jami’o’i da masana’antu zai sauya tsarin samar da kayayyaki da ci gaban tattalin arzikin jihar.

Ya ce, cibiyar za ta karkata binciken jami’o’i zuwa warware matsalolin rayuwa ta zahiri, samar da kayayyakin da za su iya shiga kasuwa tare da jawo sabbin masu zuba jari. Otti ya tabbatar da cikakken goyon bayan gwamnatinsa ga shirin, yana mai cewa ya yi daidai da manufofin bunƙasa tattalin arzikin jihar.

A nata ɓangaren, Mataimakiyar Sakatare Janar ta Majalisar ɗinkin Duniya kuma Daraktar UNDP ta Yankin Afirka, Ahunna Eziakonwa, ta ce cibiyar ba kawai aikin ci gaba ba ce, illa wata hanya ce ta sauya makomar matasan Afirka. Ta bayyana cewa shirin na cikin Timbuktoo Initiatiɓe, wanda ke da burin tara dala biliyan ɗaya domin tallafa wa sabbin kamfanoni 10,000 a Afirka, bunƙasa kamfanoni 1,000 da samar da ayyukan yi miliyan 10.

Ita ma Babbar Wakiliyar UNDP a Nijeriya, Elsie Attafuah, ta ce Manu-Tech UniPod na haɗa ilimi, bincike, kasuwanci da masana’antu domin sauya hazaƙar matasa zuwa masana’antu da ayyukan yi. Ta ce ana shirin faɗaɗa cibiyoyin daga bakwai zuwa 21 a faɗin ƙasar.

Shi kuma Babban Sakataren TETFund, Sonny Echono, wanda Dakta Suleiman Zangina ya wakilta, ya ce haɗin gwiwar zai mayar da manyan makarantu cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire tare da taimakawa bincike ya zama kayayyakin da za a iya fitarwa kasuwa.

Tun da farko, Mataimakiyar Shugabar Jami’ar Michael Okpara, Farfesa Ursula Akanwa, ta ce cibiyar za ta haɗa bincike da harkokin kasuwanci, ta yadda za a riƙa sauya sabbin dabarun jami’a zuwa masana’antu, kamfanoni da ayyukan yi, musamman a fannin sarrafa amfanin gona da bunƙasa masana’antu.

By ukarofi

Leave a Reply