Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
An bayyana cewa ba za a taɓa rufe tarihin Kano da Nijeriya da ma Afirka ta yamma ba, ba a sanya Sheikh Nasiru Kabara ba, dangane da gudunmawar da ya bai wa addinin Musulunci da ɓangarorin rayuwa.
Shugaban Tsangayar Fasaha da ilimin addinin Musulunci ta Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Ibrahim Garba Satatima ne ya bayyana haka a yayin taron kwana biyu, don tattaunawa rayuwa da gudunmawar da Sheikh Malam Nasiru Kabara ya bayar.
Taron, wanda ya guda a ɗakin taro na Musa Abdullahi da ke Jami’ar Bayero ta Kano a ranakun Talata da Laraba.
Farfesa Satatima ya ƙara da cewa mu da muke wannan lokaci ya kamata mu tuna baya, domin tuna baya shi ke sa a ga me aka yi don a yi koyi da shi.
“Sheikh Nasiru Kabara ya shekara 60 yana bada gudunmawa kuma ɗaya daga cikin ɗalibansa shi ne Sheikh Abukarar Gumi idan kuwa kana maganar Musulunci dole ka sanya Gimmi Nijeriya ashe ka ga kenan, Malam Nasiru ba ɗarika ya yi wa aiki ba addinin Musulunci ya yi wa aiki ko ka ce ɗan-Adam ya yi wa aiki.”
Shi ma a jawabinsa Limamin Kano Farfesa Sani Zaharadden ya bayyana cewa gunmawar sheikh Nasiru Kabara ba wai ta tsaya a ilimin addinin musulunci ba ne kadai har da harshen Hausa.
Ya ƙara da cewa, “Malam ya gina makarantu ya koyar da harshen Larabci sannan yana cikin waɗanda suka bunƙasa harshen Hausa sannan laburaren Malam zai yi wahala a samu kamarta a Kano,” inji Limamin Kano.
Tun da farko a jawabinsa shugaban ɗariƙar Kadiriyya, Sheikh Karibullahi Sheikh Nasiru Kabara ya bayyana cewa shirya taro irin wannan ga babban gwarzo irin wannan da ya tafiyar da rayuwarsa akan ilmantar da al’umma da fahimtar da su da kafa makarantu tun daga farko har zuwa na ƙololuwa.
Sannan ya yi kira ga al’umma da ayi koyi da halayyarsa da kuma ƙudirinsa na hadin kan al’umma Musulunci zuwa ga kalma ɗaya.
Sannan jinjina wa Jami’ar Bayaro da ta shinya wannan gagarumin taro mai cike da tarihi da anfanarwa.
A yayin taron an gabatar da takarda sama da 78, yin da ake sa ran zaa bibiye takardun a tace sannan a maida su littafi.
Taron dai ya samu halartar manyan malamai daga jami’oin da cibiyoyin ilimi a Nijeriya da ƙasashen waje irinsu Iraki da Libiya da sauransu.