Babban Hafsan Sojan Nijeriya ya sha alwashin kawo ƙarshen Boko Haram a Yobe

Spread the love

Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu

Babban Hafsan Soja (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya sha alwashin shawo kan matsalar tsaro, inda ya ce za su yi dukan abin yi wajen inganta tsaron, duk da wasu hare-haren da aka kai kwanan nan, a Buni-Gari.

Olufemi ya bayyana haka ne yayin ziyarar ƙarfafa wa sojojin dake bakin daga a jihar gwiwa a Yobe, ya ce dangantakarsa da jihar ta musamman ce, wanda a baya ya kasance ya riƙe matsayin kwamandan Brigade da Sector 2 a jihar.

“Mun zo ne a yau musamman don ƙarfafa gwiwar al’ummar Jihar Yobe da sojojin mu da ke aikin samar da tsaro, duk da koma-bayan da muka samu, na sabbin hare-haren Boko Haram.

“Duk da ba zan yi cikakken bayani dangane da sabbin dabarun da muke ɗauka ba. Amma mutanen Yobe su kwantar da hankalinsu, kuma abubuwa za su inganta.”

Har wala yau, ya yi ƙarin haske dangane da wasu muhimman matakan da za a ɗauka don magance rashin tsaro a jihar, ciki har da tura ƙarin sojoji tare da kayan aikin tsaro.

A nashi ɓangaren, Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yaba wa babban hafsan soja kan ɗaukar matakan gaggawa wajen mayar da martani kan hare-haren kwanan nan, sannan ya yi wa sojojin da suka rasu addu’a.

Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin farar hula da sojoji, inda ya buƙaci ƙarfafa haɗin gwiwa wajen bayar da bayanan sirri don daƙile matsalolin tsaro.

Gwamna Buni ya ƙara da cewa, “Dole mu haɗa kai mu yi aiki tare, tsakanin jama’an hukumomin tsaro, wajen bayar da gudummawa tsakanin rundunonin tsaron Nijeriya.”

By ukarofi