
Daga BELLO A. BABAJI
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Paris Saint Germain ta kai wasan ƙarshe a gasar zakarun Nahiyar Turai (Champions League) sakamakon doke Arsenal da jimillar ci 3-1 a wasan dab da na ƙarshe.
An buga wasan ne a gidan PSG da ke ƙasar Faransa, mako guda bayan doke ƙungiyar da ci 1-0 a filin wasa Emirates dake London.
A yanzu haka dai PSG za ta fafata da Inter Milan a wasan ƙarshe da za a yi a ranar 31 ga watan Mayu, 2025.
