Aoun ya fusata da Isra’ila

Spread the love

Shugaban Lebanon Joesph Aoun na neman kai wa bango ga matakan da Isra’ila ke ɗauka kan ƙasar sa. Daga kalaman sa na kwanakin nan za a iya fahimtar Isra’ila ta fara kure haƙurin sa. Wannan na nuna zama a haka ba zai dore da diflomasiyya tsakanin ƙasashen ba. Haƙiƙa Isra’ila na yin gaban kan ta ko ma a ce yin abun da ta ga dama a yankin. Hare-hare da ta ke kai wa kan kudancin Lebanon hatta ma a kudancin babban birnin Lebanon din wato yankin Dahiyeh da sunan farautar ‘yan Hezbollah ba abu ne da za a iya amincewa da shi ba. Abun kamar zai dakata tun watan Oktobar bara amma har yanzu duk lokacin da sojojin Isra’ila su ka bushi iska sai su kai farmaki cikin Lebanon kai ka ce ba kasa ce mai ‘yanci ba. Isra’ila fa kasancewar ta ‘yar mowa a duniya ko shafaffa da mai ba kawai Lebanon ne ke fama da hare-haen ta ba; Sham da Yaman duk na cigaba da fuskantar waɗannan matakan da sunan farautar wasu dakarun Iran da ta ce su na ma ta kulle-kulle a ƙasashen. Kwanaki shi kan sa sabon shugaban Sham Ahmad Al-Sharaa ya nuna ɓacin rai kan hare-haren na Isra’ila kasancewar in ma tsama ce da tsohuwar gwamnatin Bashar Al-Asad ai an samu sauyi da hanyar mayakan da ya jagoranta su ka amshe madafun ikon birnin Damaskas. Al-Sharaa ya bukaci kasashen duniya su tsawatawa Isra’ila ta dakatar da hare-haren amma da alamu har yanzu da sauran rina a kaba. Duk lokacin da Isrta’ila ke hare-haen nan ba a jin magoya bayan ta na ja ma ta birki don gani su ke yi ai kare kan ta ta ke yi da matakan na zubar da jini da lalata dukiya. Gaza ma ba a magana don nan kullum na fudskantar hare-hare da kashe Falasɗinawa akasari mata da ƙananan yara da sunan farautar mayaƙan Hamas. Gaskiyar magana hari kan Lebanon da sunan hallaka ‘yan Hezbolla ba zai zama abun lamunta ga gwamnatin ƙasar bat un da a yanzu an samu sulhu. Hezbollah ne ginshiƙi ce a gwamnatin Lebanon don ita ce ke da hurumi ko ma dai a ce dan ta ne ke zama shugaban majalisar dokokin kasar. Ma’ana dai kasancewar ta ƙungiyar ‘yan Shi’a ko wacce Iran ke marawa baya, a tsarin gwamnatin Lebanon ɗan Shi’a ke zama shugaban majalisa da hakan ya sa Nabih Berry yake cigaba da jan zare a matsayin shugaban majalisar dokokin ƙasar. Majalisar ke da hurumin zaɓen shugaban ƙasa shi kuma ya naɗa Firaminista. Wato a taƙaice shugaban majalisa shi daga Shi’a, shugaban kasa mabiyin addinin Kirista inda Firaminista kan zama ɗan Ahlissunnah. Haka Lebanon ke gabatar da tsarin gwamnati don wakiltar rabe-raben addini da muradun sassan ƙasar. Don haka cigaba da kai farmaki kan Hezbollah a lokacin da ya ke waje da yaƙi ba zai zama abun lamunta ga mahukuntan Beirut ba. Kazalika an ma tura sojojin gwamnati don kula da kan iyakar kudancin Lebanon da ke iyaka da Isra’ila. Abu ne kuma na wuce gona da iri a ce lallai sai Hezbollah ta wargaza dukkan mayaƙan ta ko watsewa daga dukkan tungar da ta ke da ita a kudancin tun da a cikin kasar ta Lebanon ne ba ƙetaren iyaka ba. Wani abu ma ai Isra’ila ta kai mummunan hari kafin samun sulhun kan babbar sakatariyar Hezbollah da ke Dahiyeh ta ruguza babban bene da hakan ya yi sanadiyyar kashe jagororin Hezbollah ciki har da shugaban ta na tsawon zamani Hassan Nasrallah. Mun san cewa wannan karon Hezbollah ta yi tsama da Isra’ila ne kan hare-hare da da sojojin Isra’ila ke yi a Gaza.  Mara baya ga al’ummar Gaza ya jawo rasa ran jagororin Hezbollah da ma na Hamas ɗin kamar babban shugaba Isma’ila Haniyeh da Yahaya Sinwar da sauran su da dama. A wajen Isra’ila sai lallai ta wargaza waɗannan ƙungiyoyin biyu kafin ta tsagaita hare-hare. Abu ne mai kamar wuya a iya cewa an murƙushe HHezbollah ba tare da ɗaura ɗamarar yaƙi da Lebanon ba gaba ɗaya ta hanyar mamaye ƙasar. Hakanan nan Hamas sai an kashe dukkan al’ummar Gaza kafin kawo ƙarshen Hamas. Muradin na Isra’ila zai cimmu ne idan an cigaba da yakin kare dangi da bijirewa dokokin duniya da biris da ƙa’idojojin Majalisar ɗinkin Duniya da shashantar da hkunce-hukuncen kotun duniya ta birnin Haƙue.

Isra’ila ta cigaba da kai hare-hare kudancin Lebanon bayan neman gurgubncewar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Nuwambar bara.

Wannan ya sa shugaban Lebanon Joesph Aoun buƙatar masu shiga tsakani da su ka tsayawa Isra’ila wato Amurka da Faransa su tilasta dakatar da hare-haren.

An ga gini a inda Isra’ila ta kai sabon harin ya turnuƙe da hayaƙi.

Amma ofishin Firaministan Lebanon Benjamin Netanyahu ya ce harin ya shafi wani gini ne da Hezbollah ke tara makamai don haka ta kai harin don dakatar da nufin ƙungiyar mai samun goyon bayan Iran.

Isra’ila tun farko ma ta umurci mutane su kaucewa yankin Hadath na kudanci da ta kai harin ta na mai cewa sam ba za ta bar Hezbollah ta yi karfin da za ta zama ma ta barazana ba.

A nan dai shugaba Aoun ya yi Allah wadai da harin da zaiyana shi da karantsaye ga yarjejeniyar tsagaita wuta, ya na mai bukatar Amurka da Faransa su sanya jan birki ga hare-haren.

Idan mu ka leka Gaza kuma masu ceton rai sanadiyyar harin Isra’ila kan wani gida a Gaza sun bayyana cewa yawan mutuwar da a ka samu zuwa yanzu ta kai mutum 23.

Jami’an kare lafiyar farar hula sun ce harin a kan garin Jabalia ya kai mutum 23 don da farko an samu gawa 12 inda wanshekare a ka samu gawa 11.

Sojojin Isra’ila sun ce sun kai hari ne kan cibiyar shirya hari ta Hamas ne a Jabaliya ba ta ba da ƙarin bayani ba.

Harin a makon jiya a yankin Al-mawasi da ke garin Khan Younis na kudancin Gaza ya yi sanadiyyar mutuwar mata da miji da ‘ya’yan su 3 lokacin da a ka jefa mu su bom ya dira kan tantin su.

Tun wargajewar yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta tsakanin Hamas da Isra’ila a ranar 18 ga watan jiya adadin waɗanda Isra’ila ta kashe a Gaza sun kai mutum 1,978 inda ya zama jimillar mutanen da hare-haren Isra’ila su ka aika lahiradaga bayan 7 ga Oktobar 2023 ya kai mutum 51, 355.

Yanzu kisan mutane a gaza ya haura mutum 52,000:

Ma’aikatar lafiya ta Gaza da ke ƙarƙashin jagorancin Hamas ta baiyana cewa an samu ƙarin mutuwar mutum 51 a hare-haren da Isra’ila ke kai wa kan Gaza da zuwa yanzu adadin mutuwar mutane ta haura mutum 52,000.

Asibitoci a Gaza sun ba da labarin kawo gawawwaki 51 cikin sa’a 24 da su ka wuce da lissafin adadin mutuwa ya kai mutum 52, 243 a tsawon wata 18 na yakin na Isra’ila kan Gaza ko Hamas.

Cikin mutanen akwai gawawwaki kimanin 700 da a ka kammala tantancewa kuma sun haɗa da wadanda a ka tono ƙarƙashin gine-ginen da boma-bomai su ka ruguza.

Tun 18 a watan jiya da Isra’ila ta kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita ta ke kai hare-haren kusan kullum kan Gaza da ma zagaye garin Rafah na kuryar kudanci da mamaye kimanin kashi 50% na Zirin na Gaza.

Kungiyoyin agaji sun ce kusan kwana 60 Isra’ila ta ƙange al’ummar Gaza daga samun tallafin abinci da magani da nan ba da daɗewa ba kayan agajin za su kare inda tuni dubban yara su ka rasa sinadarai masu taimakon lafiyar jiki.

A nan za mu iya amincewa an dau ‘yan-adam da a ke zubar da jinin su a matsayin wasu halittu masu daraja kuwa? Kalmar Allah wadai kaɗai ta isa dakatar da wannan masifa da ta aukawa wannan yankin ta ke karewa kan waɗanda ba su yi wa kowa laifi ba? Ya nuna fa in mutum na son ya zauna da ran sa a yankin nan to sai dai ya zama ɗan amshin shatan Isra’ila ko mai hidima ga muradun Isra’ila. Mun sha ba da uzuri ga kasashen Larabawa don yanda su kan maida martani a kaikaice don yanda siyasar duniya ta ke da matuƙar shugabannin ƙasashen masu neman dauwama kan mulki ba su yi takatsantsan ba za su iya fuskantar tumɓukewa kan mulki ko ma rasa ran su. Ga misalin marigayi Sadamma Hussein a Iraki ga ma nan Afurka in mun tuna yanda a ka yi kisan gilla ga marigayi shugaba Moammar Gaddafi a Libya. Da zarar shugaba ya daga yatsa to nan take Isra’ilawa za su fille yatsar. Tsarin jagoranci a Masar da kuma na Falasɗinawa a birnin Ramallah ƙarƙashin Mahmud Abbas ne salo mafi sauƙi na daɗewa kan mulki.

Kammalawa;

Duk nisan jifa ƙasa zai faɗo kuma komai nisan dare gari zai waye. A nan ma’ana dai zalunci ba zai daumawa har abada ba. Ko ba jima ko ba dade wataran sauran Falasdinawa ko waɗanda a ke takewa haƙƙi a gabar ta tsakiya za su samu ‘yanci. Yanzu dai ‘yan mowa ke jan zaren su ko cin Karen su ba babbaka. Akalla dai taimakon da za a iya wanda a ke zalunta shi ne irin wannan rubutu, yin magana ta nuna ƙorafi ko kuma a tsaya ga addu’a da ta ke makamin bayin Allah.

By ukarofi