Babu juyin mulki a Ƙasar Benin, gwamnati na nan daram, inji Ministan Cikin Gida

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Harkokin Cikin Gida na Ƙasar Jamhuriyar Benin, Alassane Seidou ya ce dakarun tsaron ƙasar sun yi nasarar daƙile yunƙurin kifar da gwamnati.

An tabbatar da cewa yunkurin kifar da gwamnatin ƙasar Benin da wasu sojoji suka yi a safiyar Asabar ya ci tura, bayan dakarun gwamnati sun sake karɓe ikon cibiyoyin gwamnati da gidan talabijin na ƙasa.

A safiyar ranar Asabar ne wani kwamanda, Pascal Tigri, tare da wasu runduna na sojoji, suka kutsa cikin gidan talabijin na ƙasar, inda suka gabatar da sanarwar cewa sun hambarar da Shugaba Patrice Talon, tare da rusa gwamnati da dakatar da kundin tsarin mulki.

Sai dai bayan lokaci kaɗan, gwamnatin Benin ta sanar cewa sojojin da suka yi yunkurin juyin mulkin an fatattakosu, kuma dakarun da suka tsaya tare da gwamnati sun maido da doka da oda.

Ministan ya bayyana cewa an yi nasarar hana juyin mulkin, kuma shugaban ƙasa Patrice Talon yana cikin tsaro babu wata barazana.

Rahotanni sun bayyana cewa, an kama wasu daga cikin sojojin da suka yi yunƙurin, yayin da ake cigaba da gudanar da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a baya.

Al’amarin ya tayar da hankula a yankin, musamman ganin yadda ƙasashen Afrika ta Yamma ke fama da lamuran juyin mulki a ƴan shekarun baya-bayan nan.

By Babaji