Ban naɗa Babban Magatakardan Kotu don kasanewar sa Kirista ba – Alƙalin Alƙalan Bauchi

*Ta gargaɗi sabbin kwamishinonin kotuna kan cin hanci

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi

Alƙalin Alƙalai a Jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar, ta nuna takaicin ta bisa yadda wasu ma’aikatan shari’a suke buga takardun bogi, rasitai, har ma da tambarin hukuma na kan su suna yin almundahanar karkata kuɗaɗen shiga ga gwamnati, domin arzurta kan su.

Babbar Mai Shari’ar ta jiha ta bayyana cewar, bisa ƙoƙarin kawar da wancan mummunar ɗabi’a ce na karkata kuɗaɗen shigowa wa gwamnati, a yanzu aka buga wasu sabbin makamantan waɗancan takardu da sauran kayayyakin aiki masu alamun tsaro da zummar daƙile duk wata almundahana ta rashawa da cin hanci, cikin sabon tsari na inganta tattalin arzikin jiha.

Mai shari’ la Rabi Umar tana jawabi ne a ranar Talata da ta gabata yayin zartar da rantsuwar kamun aiki wa sabbin kwamishinonin maƙala rantsuna, inda ta yi masu nasihar su guji duk wata hanya da za ta jefa su cikin nadama da halaka yayin gudanar da ayyukansu.

Ta yi tuni da cewar, babban magatakardan kotu da shugaban tara kuɗaɗen shiga na gwamnati sun yi zama da suka amince wa bai wa babbar kotu wani kaso cikin dari na kuɗaɗen shiga ta fuskar kotu, yayin da mafi yawan kason za ake zurara wa a lalitar gwamnatin jiha.

Alƙali Rabi Umar, wacce ita ce kuma shugabar hukumar kula da lamuran shari’a ta jihar, ta nuna takaicinta kan yadda wasu tambaɗaɗɗun ma’aikatan hukumar su ke zargin ta da bai wa wani mabiyin addinin Kirista matsayin Babban Magatakardan Kotu da zummar ƙasƙantar da addinin Musulunci.

Ta ce, “ni Musulma ce da na tsaurara bin ƙa’idojin addini na wanda ya fauwala mun kamanta gaskiya da yin adalci wa dukkan jinsin jama’a ba tare da nuna bambancin aƙida ko yare ba, kuma na yi rantsuwar biyayya ga kundin tsarin mulkin Nijeriya, don haka, ba zan sava wa addini na ko kundin tsarin mulkin ƙasa ba.”

Ta kuma bayyana cewar, ba wata ma’aikata ko hukuma ta gwamnati da aka maƙale ta a turken addini, kazalika  Babbar Kotun jihar Bauchi inda ake gane zurfin ruwa daga na gaba, tana mai jaddada cewar, ana naɗa babban magatakardan kotu ne daga cikin ma’aikatan hukumar shari’a, ba tare da yin kwatance da addini ba.

Mai Shari’a Rabi Umar ta kuma tuhumi yadda aka naɗa Misis Modupe O. Bello ‘yar asalin garin Ibadan ta jihar oyo, da Alƙali H.M Tsamani ɗan asalin jihar Bauchi dukkan su mabiya addinin Kirista a cikin tarihin shari’a ta jihar Bauchi, kuma suka yi aiki a matsayin manyan magatakarda na kotu, ba a yi ƙorafi ba sai yanzu?

Rabi ta bayyana cewar, abinda yake faruwa a halin yanzu shi ne, batu ne na zaunannen hukuncin biyan kuɗaɗe wanda Babbar Kotun jiha ta zartar a ranar 23th ga watan Yuni na shekara ta 2009, a ƙarƙashin jagorancin babban magatakardan babbar kotu na wancan lokaci, kuma kafin Alƙali Rabi Talatu Umar ta zama Alƙalin Alƙalai ta jiha, lamarin da ya haddasa hukuncin babbar kotun tarayyar Nijeriya bisa babbar kotun jiha, wanda ya daɗaɗa wa AMCON kan ƙara mai lamba FHC/BAU/CS/37/2017 da aka zartar a ranar  8 ga Disambar  2020, da ya mara wa AMCOM jinkirta tokare lalitar jihar Bauchi bisa doka ko hukunci kotu, lamarin da har yanzu yake jinkiri a ɗakin kotu.

“Ma’ikatan da suke haddasa wannan koma-baya, suna yi ne da goyon baya haɗi da tsoma hannun ubangidan su, waɗanda a yanzu yake karkato addini cikin lamarin domin haddasa rashin jituwa tsakanin Babbar Kotun Jiha da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a.”

Kamar yadda alƙalin alƙalan ta ce, wancan ubangida na waɗancan ma’aikata, yana ta kara-kainar dagula mutuncin tsari ko gungun sa da sunan addini domin ya yaudari jama’a su haƙiƙance da manufarsa, tana mai bayar da tabbacin hakan ba zai taɓa faruwa ba a ƙarƙashin jagorancinta.

Alƙalin Alƙalai Rabi Umar ta kuma yi tuni da cewar, umarnin bincike da ta bayar na kwanan nan, shi ne na waɗansu tsirarun ma’aikatan babbar kotun jiha, da suka ƙulla yarjejeniya da wasu mabambantan kamfanoni bisa jigar biliyoyin nairori ta hanyar amfani da takardun ofishin babban magatakardan kotu, haɗi da tambarin hukuma duka na bogi, ba tare da sani ko umarnin ta ba.