Basaraken mawaƙi, Aminu Ala, ya aurar da ’ya’yansa uku rigis rana ɗaya

Spread the love

DAGA MUKHTAR YAKUBU a Kano

A karon farko fitaccen mawaƙi Sarkin ɗiyan Gobir, Alhaji Aminu Ladan Abubakar Ala, ya yi bikin auren ’ya’yansa mata har guda uku rigis lokaci guda.

A ranar Lahadin da ta gabata 28 ga Yuli, 2024, ne aka yi taron ɗaurin auren a gidansa da ke unguwar Maidile cikin ƙaramar Hukumar Kumbotso a cikin Birnin Kano da misalin ƙarfe 12 na rana.

Taron ɗaurin auren wanda ya samu halartar dubbun jama’a daga ciki da wajen ƙasar nan kama daga sarakuna malamai attajirai da manyan ma’aikatan gwamnati.

Ɗaurin auren dai na ‘ya’yan Aminu Ala ne guda uku da suka kasance su ne manyan ‘ya’yansa wato Fatima Aminu Ladan Abubakar Ala Aisha Aminu Ladan Abubakar Ala da Bilkisu Aminu Ladan Abubakar Ala. 

Shugaban Majalisar Malamai ta Arewa da kuma Majalisar Malamai ta Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil yana ɗaya daga cikin manyan malaman da suka jagoranci taron ɗaurin auren.

Tun kafin ranar ɗaurin auren dai aka fara shirya taron bikin, in da a ranar Juma’a 26 ga Yuli aka shirya bikin ƙauyawa, yayin da kuma a ranar Asabar aka yi taron yinin biki duk dai a gidan Aminu Ladan Abubakar Ala da ke Unguwar ta Medile.

Taro mafi ƙayatarwa da aka shirya shi ne a daren ranar ɗaurin auren, inda aka shirya taron Liyafar cin abinci a babban wajen taro na Meenah Event Center da ke Unguwar Nassarawa G R A tun daga misalin ƙarfe 8 na dare har zuwa 12 na dare. 

A wajen taron dai an gayyaci duk wani makusanci da abokai domin nuna ƙauna da kuma kara ga Aminu Ladan Abubakar Ala.

An dai yi shagalin biki, an ci abinci an yi nishaɗi a wajen har zuwa lokacin da aka tashi daga taron.

Muna fatan Allah ya sanya albarka a cikin auren ya ba da zaman lafiya.

Bayan kammala shagulgulan bikin auren ‘ya’yan Aminu Ladan Abubakar Ala wakilinmu ya nemi jin ta bakin uban amare uku, mawaƙi Aminu Ala don jin yadda ya samu kansa a karo na farko cikin aurar da ‘ya’yansa uku. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA Bayan taya ka murnar auren ‘ya’yanka da aka yi a Lahadin da ta gabata, masu karatunmu za su so jin yadda ka samu kanka a cikin hidimar bikin.

AMINU ALA: To muna yi wa Allah godiya da ya nuna mana wannan lokaci na aure wanda aka saka rana wata uku, kuma ga shi a yanzu muna tattaunawa bayan an kammala biki kowa ya watse bayan an yi hidimar bikin an gama lafiya, kuma duk waɗanda suka zo sun koma gidansu lafiya.

Da yake wannan shi ne karo na farko da ka aurar da ‘ya’yanka kuma har su uku. Ko a yaya hidimar bikin ta zo maka?

Ka san wani abu ne wanda yake ko ba ka da ƙwarewa a kansa, to yana faruwa a kan idonka na makwafta da abokan arziki, don haka an yi a gidanku da wasu da kake gani. Amma duk da haka sai ka samu wasu ɗan bambance-bambance idan aka ce kai ne za ka yi. Saboda haka akwai muhimman mutane na kurkusa waɗanda sai ka manta ba ka sanar da su ba waɗanda ka na ganin su a cikin hidimar ma suke.

Yanzu dai ka ga mafi kusa a cikin masarautun da nake kusa da su masarautar Gobir, saboda ni ɗan Sarkin Gobir ne. To ban kai katin gayyata can ba. Sannan dubi yadda muke da masarautar Dutse, ban kai katin gayyata can ba. To ka ga irin wannan, sai ka ga mutane na kurkusa sai ka ga ka yi kuskure a kansu. 

Haka kuma akwai amintattun mutane waɗanda tare kuke faɗi-tashi, amma sai ka ga ka manta da wani mafi kusa kuma ka gayyato wani na nesa. To irin wannan abubuwan su ne wanda aka rinƙa cin karo da su. Kuma ka san an canza lokaci, huɗu ga watan Agusta za a yi, sai ake ganin masu zanga-zanga sun ce babu fashi, kuma ba mu san da sigar da za ta zo ba, amma dai muna fatan Allah ya tabbatar mana da zaman lafiya a kasar mu. To wannan shi ne ya sa su masu neman auren suka ga dacewar a matso da shi baya zuwa 28 ga Yuli, to wannan ma ya dan daburta abubuwa da dama, amma dai muna murna don an yi taro an tashi lafiya kuma cikin nasara.

Tara jama’a irin wannan akwai darusa masu yawa, ko wanne darasi ka samu?

Akwai darussa sosan gaske har ma da wasu ilimummuka da za ka samu. Kamar yanzu ka ga a matsayinmu na ‘ya’yan sarki muna da al’adunmu da yawa wanda muka bari saboda nisa da kuma tsoron halin da ake ciki na rayuwa da kuma rashin tsaro da ake ciki musamman a Arewa maso gabas, to wannan ya sa muka haƙura. 

Amma idan za a wanke ‘ya’yan sarki ana kai su wajen Sarauniya ta Gobir saboda ita za ta yi musu wankan lalle, akwai wankan al’ada da kuma kayan al’ada da suke sakawa, akwai takalmi da sauran kayan al’ada, sannan za a je a gabatar da su a gaban sarki ya yi musu huɗuba da nasiha, sannan su yi bankwana da shi. Sannan mu dawo da su a fara hidimar bikin. Ka ga duk wannan ba mu yi ba. 

Sannan a nan masarautar Kano ta karve mu, wanda ka san Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero uba ne a gare mu kuma ya tsaya a matsayin uba, don haka sai muka tsaya muka yi al’amuran mu a ƙarƙashin wannan masarauta. Wanda bayan an kammala biki ya kamata a ce ranar da aka ɗaura auren za a kai amaren, to sai da muka kai su kashe gari don su je su yi sallama da sarki, suka je suka yi hotuna da darki suka yi sallama.

Kuma yin amfani da wannan dama wajen godiya ga wannan masarautu, musamman masarautar Kano da ya zama suka zo kamar ƙwansu da ƙwarƙwatarsu, don akwai Hakimai da yawa wanda suna ma ba zai yiwu ka kama sunan su ba saboda lokaci, waɗanda suka taho ƙarkashin masarautar Kano da fadawan sarki da masoya duk gabakiɗaya suka zo suka cika wajen, don in ka lura har da motar Sarki two dogarai aka zo don taya mu murna.

Haka kuma idan ka kalli masarautar Zazzau Ciroma ma aka taso wadda sarautar Ciroma ta nabban ɗan sarki ce to shi ne ya zo, kuma aminina ne kuma yayana ne maigidana ne kuma ina da kusanci da shi, don a Zazzau idan ka ɗauke Ban buran Barden kudu, to babu wanda nake zuwa gidansa sama da shi Ciroma. Ina zuwa gidansa mu yi hira mu ci abinci muna huddar arkizi da shi, amma na manta ban kai masa katin gayyata ba, sai kuma ya zama shi ne wakilin sarki. Kuma akwai Hakimai da suka zo, irin su Shattiman Yamman Zazzau da sauran Hakimai da yawa da suka zo daga Zazzau. Sannan akwai Hakiman Misau, kamar Mukaddam ya turo sako da wakili, sannan akwai Dujuman Misau. Sannan akwai Hakimai dawa Gombe, kamar Zannan Nafada wato Alhaji Ibrahim Jalo Sarkin Zangon Dukku, da kuma Hakimai da suka zo daga ƙasar Gumel wato Lautai, du kuma Hakimi da ya zo daga masarautar Lafiya wato Bulaman Lafiya.

Sannan kuma ga Salanken Gaya, Salanken ƙasar Hausa ta Daura kuma Salanken Mubi, du Sa’idu Gombe El-Mu’azu Burniwa da sauran mutanen da suka zo waɗanda ba za su misaltu ba, don ka ga akwai Sarkin Dawaki Babba, Ga Sheikh Ibrahim Khalil su ne waliyyai, ga Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, Sharif Muhammad Rijiyar Lemo wanda shi ne ya ɗaura auren ya yi huduba, saboda haka babu abin da zan ce wa mutane musamman waliyyan nan guda uku, Sheikh Ibrahim Khalil da Farfesa Sa’idu Muhammad Gusau da kuma Sharif Muhammad Rijiyar Lemo da suka yi walicci na waɗannan amare. Sai ‘yan Dangin juna abokan mu’amalar a cikin masu wasan Kwaikwayo da finafinai da rubutu akwai marubuta sun zo irin su Ado Ahmad Gidan Dabino, Kabiru Yusif Fagge, Sai tsohon Akanta na ƙasa.

Na ji daɗi na yi farin ciki, don Unguwar mu suka ce ba su taba ganin shigar manyan mutane cikin Unguwar ba kamar wannan rana da aka yi daurin auren ‘ya’yana saboda masu kanti a Unguwar har gajiya suka yi da tambayar ina ne gidan Ala. Babu shakka wannan aure ya ɗaga martaba ta, don martaba ce ta ‘ya’yan, amma ya daga martaba ta a matsayina na mahaifinsu a idon al’ummar unguwar.

 Sannan akwai mawaƙa irin su Fati Nijar, Fantimoti, Maryam A Baba, Ahmad Yariman Tiga, Shalelen waƙa da ya zo daga Zazzau tare da mahaifiyarsa. Don haka babu abin da za mu ce sai dai Allah ya saka wa kowa da alheri, kuma Allah ya maimaita mana irin wannan alherin. Yaran nan da aka aurar da su Allah ya ba su zaman lafiya da mazajensu, Allah ya azurta su, kuma Allah ya hore wa kowa, ƙasarmu Allah ya ba mu zaman lafiya.

By ukarofi