Tallafin taki da Sanata Barau ya raba a Kano zai taimaka wajen bunƙasa noma – Hon. Yaƙub Takai

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana irin tallafin taki ga manoma kyauta da mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanatan Kano ta Arewa Dakta Barau I Jibrin yake bayarwa ga dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar Kano da cewa zai mutuƙar taimakawa wajen bunƙasa noma a daminar bana.

Hon. Yaƙub Husaini Takai ɗaya daga cikin manyan mataimaka na musamman ga mataimakin shugaban majalisar dattijai na ƙasa Sanata Barau I jibrin ne ya bayyana hakan da yake zantawa da ‘yan jarida.

Ya ƙara da cewa tsarin bayar da takin da Sanatan Kano ta Arewa ya kawo jihar Kano da aka ƙaddamar da rabon takin da ya samar ƙarƙashin jagorancin shugban ma’aikatansa Farfesa Muhammad Ibn Abdallah ana rabawa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na  jihar Kano.

Ya ce wannan rabon takin da duk ƙasar nan ba a taɓa yin irinsa ba, rabo ne da ya ake yi ba a iya mazaɓar Sanatan Kano ta Arewa ba da yake wakilta ba, a dukkan  faɗin jihar Kano baki ɗaya ya ke.

Hon. Yaƙub Husaini  Takai ya yi nuni da cewa kowace ƙaramar hukuma ta samu takin ne daidai  da irin yawan mazaɓunda take da su kuma tsarin rabon ana yi ne ta baiwa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a matakin ƙaramar hukuma da na mazaɓu da ‘yan jam’iyya da na ‘yan dangwale masu zaɓe.

Ya ƙara da cewa a tsarin da mataimakin shugaban majalisar dattijai na ƙasa ya yi babu wanda ya samu ƙasa da buhun taki  ɗaya a wannan  yanayi na hali da ake ciki, a ce talaka ya sami buhun taki daga hannun ɗan siyasa mai kishin ci gaban al’umma sai godiya ga Allah.

Takai ya ce ko shi a yankinsu na ƙaramar hukumar Takai duk da  a  yankin Sanatan Kano ta Kudu suke, Sanata Barau I Jibrin ya ba su taki buhu sama da 220 a rabawa al’umma, wannan mataki ba ƙaramin taimako ne ga manoma ba sosai.

Ya ƙara jaddada cewa rabon takin da mataimakin shugaban majalisar dattijai na ƙasa yake, ba  kawai ‘yan mazaɓarsa yake baiwa ba kaɗai  gaba ɗaya faɗin Jihar Kano yake taimakawa.

Hon. Yaƙub Husaini Takai ya ce duk da cewa jam’iyyar su ta APC Sanatan su ɗaya a Jihar Kano amma ba sa wani da na sani, in dai ta samun abin amfani ne na Gina al’umma ,suna amfana daga  Sanatan  Kano ta Arewa Dakta Barau I Jibrin a kowace mazaɓa suna alfahari da shi.

Ya ƙara da cewa ba taki kawai yake rabawa ba, domin da azumi ya raba shinkafa tun daga mazaɓu da shugabanin jam’iyya da sakatarori da shugabanni na ƙananan hukumomi da  duk masu ruwa da tsaki sun samu.

Ya ce irin waɗannan ayyuka da Sanata Dakta  Barau  I Jibrin yake zai bashi dama ya zama Gwamnan Jihar Kano nan gaba domin ko a jam’iyyar su ta APC babu wanda ma suke tunanin zai fito ya ce zai nemi Gwamnan Kano idan ga Barau idan ma  wani  ya fito ba za a zaɓe shi ba, babu  wanda za su sa a gaba a takarar  Gwamna a jam’iyyar APC sai shi da yardar Allah.

Hon. Yaƙub Husaini Takai ya ce suna fatan Allah ya ba su dama na tsadar da  Sanata Dakta   Barau I Jibrin a Gwamna da nasara su kada wannan Gwamnati ta Kano mai ci ta Abba ta  Kwankwasiyya ,maƙaryaciya da babu abinda tasa a gaba sai ƙungiyanci da komai cancantarka da dacewa da ƙoƙarinka ba za su yi da kai ba.

By ukarofi