Batun dawo da martabar noma a Nijeriya

Kamar dai yadda kowa ya sani ne cewa, akwai gayar muhimmanci ga gwamnati ta sake duba batun bunƙasa harkokin noma a ƙasar nan, duba da rawar da ɓangaren ke takawa wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasa da samar da wadataccen abinci. Ayyukan noma su ne ginshiki kuma babbar hanyar da za ta iya jure kowace irin kwaramniya ga ci gaban ƙasa tare da al’ummarta baki ɗaya.

Noma babbar abu ce a Nijeriya, ana ma kallon cewa ita ce sana’ar da ta fi kowace sana’a muhimmanci, wacce idan babu ita rayuwar ma sam-sam ba za ta yiwuwa ba.Haka zalika, kamar yadda ake yi wa noma kirari da cewa ‘Na duƙe tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya taras’, wannan ko shakka babu, ta duba da ɗimbin albarkatun da yake ƙunshe dasu kuma waɗanda ba su ƙarewa matuƙar akwai bil Adam a doron ƙasa, shi ne tushen duk wata hanya ko matakin ci gaban tattalin arzikin kowace ƙasar da ta shahara a duniya.

Wanda ya tuna bara bai ji daɗin bana ba, musamman ta la’akari da rawar da ayyukan noma su ka taka a Nijeriya a fannin ci gaban tattalin arziki, da tasirin noman gyada a arewacin Nijeriya ga tsarin tattalin arzikin ƙasar nan. Sananniyar tsibin dalar gyada a arewacin Nijeriya babbar alama ce kuma shaida ga kowa kan yadda mu ka tsaya tsayin daka, kuma abin alfahari a shekarun da su ka gabata. Lamarin da ya kai mu ne kan gaba a tsakanin ƙasashen Afrika ta yamma, inda Nijeriya ce ke noma kaso 41 cikin ɗari na gyadar da ake nomawa a ƙasashen, daga arewacin ƙasar nan.

Haka kuma, idan mun kalli shekarar 1880, Allah ya albarkace mu da gonakin ‘cocoa, a kudancin Nijeriya, musamman a Legas da Otta. Wanda har zuwa tsakanin 1950 zuwa 1970, Nijeriya ita ce ta biyu wajen noma cocoa a duk faɗin duniya. Sannan ga gonakin noma kwakwar man ja a yankin kudu maso gabashin ƙasar nan, yanki ne wanda Allah ya yi masa tagomashin kwakwar man ja, bila adadin.Bugu da ƙari kuma, baya ga arzikin albarkatun gyada, cocoa da kwakwar man ja, Allah ya sanya wa ƙasarmu albarkar noma itacen roba, auduga, ganyen taba da sauran kayan amfanin gona kala-kala. Waɗanda dukansu masu ƙima ne a fannin bunƙasar yanayin tattalin arziki, kuma waɗanda za su gina Nijeriya zuwa matsaukakin matsayi ga ’yan ƙasa.

A hannu guda kuma, waɗannan kayan amfanin gona da Nijeriya ke samar wa, a kan duga-dugan su ne tsarin tattalin arzikin mu ke gudana tare da kasancewa matsaukaka kuma aka san mu a tsakanin ƙasashen Afrika da ma duniya.

Wanda sai a shekarar 1956, Nijeriya ta buɗe sabon shafin nasarar ɗanyen man fetur, ta hanyar Oloibiri a jihar Bayelsa. Yayin da wannan shi ne soman taɓin canja alƙiblar inda ƙasar ta dosa a fannin tattalin arziki, kuma daga wannan lokacin ne fannin noma ya samu tazgaro da koma baya, gwamnatoci su ka karkata zuwa ga man fetur fiye da bayar da cikakkiyar kulawa ga ayyukan noma.Bisa ga karkata akalar tattalin arziki daga sashen noma zuwa ga man fetur, ya jawo gagarumin sauyi, yayin da a tsakanin shekarun 1960 da 1970, ayyukan noma su ne kan gaba a fannin ci gaba da bunƙasar yanayin tattalin arzikin Nijeriya- musamman gyada, wanda ake noma sama da tan miliyan 1.6. Amma a farkon shekarar 1980 adadin ya faɗo warwas, inda da jibin goshi ake iya noma gyadar da ta kai ton 700,000 kacal.

Al’amarin da bai ƙyale noman Cocoa da dangogin su ba.A wata ƙididdigar da hukumar kula da lafiyar dabbobi ta ƙasa (Federal Department of Livestock and Pest Control Serbice) ta bayar ya nuna yadda Nijeriya ke kan gaba a fannin kiwon dabbobi da tsuntsaye, wanda shi ne babban jigon bunƙasar tattalin arzikin kowace ƙasa a duniyar nan. Yayin da wani bincike ya gano cewa, a 1990 Allah ya horewa Nijeriya shanu kimanin miliyan 13,947,000.A cikin wannan adadin, jihar Barno ita ƙadai ta mallaki shanu kimanin miliyan uku, yayin da jihar Bauchi da tsohuwar jihar Gongola (Adamawa da Taraba yanzu), Kaduna, Nijar, Plateu da Sakkwato, kowanen su ya na da saniya (nagge) kimanin miliyan ɗaya.Haka zalika kuma, idan an koma gefen kiwon tumaki da awaki, jihohin Bauchi, Barno, da Kano, su na da tumaki da awaki sama da milyan biyu kowacen su, inda Katsina, Gongola, Sakkwato su na biye dasu da sama da miliyan ɗaya kowacen su.Jihohin Benuwai, Plateau su na kan gaba wajen kiwon aladai, inda a wancan lokacin kowacen su ta na da kimanin 500,000, sai Gongola da Kaduna na bin bayan su da 470,000 da 250,000.

Haka zalika kuma, jihar Benuwai ce ke kan gaba wajen kiwon kaji (a wancan lokacin), inda take da kaji sama miliyan 8, sai jihohin Ogun, Oyo, Ondo, Anambara da Bendel ke bin bayanta da kaji sama da miliyan huɗu kowacen su.Bugu da ƙari kuma, a albarkatun kiwon dabbobin da tsuntsaye, jihohin Bendel da Benuwai su na kan gaba wajen kiwon agwagi sama da miliyan ɗaya kowacen su, wanda Bauchi, Filato, Gongola da Sakkwato ke biye da su da agwagin da su ka doshi miliyan ɗaya kowacensu.

Har wala yau kuma, binciken ya nuna yadda jihohin Kano, Akwa-Ibom, da Filato su ka zarta sauran jihohin ƙasar nan wajen kiwon talo-talo. Haka kuma, jihar Bauchi ta na kiwata zomaye sama da 500,000, idan an kwatamta da jihohin Kano, Katsina da Kaduna ma su yawan zumayen; 217, 166,000, da 112,000 a takaice.Saboda haka, Jaridar Manhaja na ganin ya zama wajibi ga gwamnatocin Nijeriya su sake duba wannan lamarin wajen sake farfaɗo da harkokin noma, wanda ko shakka babu zai kasance kan-da-garki tare da zama babban jigon ci gaban tattalin arzikin Nijeriya, kamar yadda ya kasance a farko.