Bikin auren ‘yar jaruma Zulai Babeji: ‘Yan fim sun mata kara

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU

Fitacciyar jaruma a masana’antar finafinai ta Kannywood Hajiya Zulai Babeji ta yi bikin auren ‘yar autarta, wato Maryam M. Usman Nunu wadda aka fi sani da Maryam ‘Yar autar Mama. 

Bikin auren dai an fara gudanar da shi ne a ranar Asabar 5 ga Afrilun 2025 inda aka fara da taron liyafa a ɗakin taro na Gidauniyar Jihar Kano da ke kan titin BUK Kano da misalin ƙarfe biyar na yamma.

Taron bikin dai ya samu harkar ‘yan fim da dama da suka halarci wajen domin taya jaruma Zulai Babeji murna.

A wajen taron an sha shagali na gani na isa, domin kuwa fitattun jarumai da suke cikin masana’antar finafinai ta Kannywood da daman sun halarci wajen bikin.

Cikin ‘yan fim ɗin da suka halarci wajen sun haɗa da Asma’u Sani, Hadiza Kabara, Hajara Usman Hajara ‘yar Rano, Amir Iliyasu maiross da sauran jarumai musamman ma na cikin shirin ‘Daɗin Kowa’.

An dai shafe tsawon sa’o’i ana gudanar da shagalin bikin tare da gudanar da liyafar cin abinci.

A rana ta biyu ta bikin wato Lahadi 6 ga Afrilu. An ɗaura auren Maryam M Usman Nunu tare da angonta Muhammad Dahiru Abdul’aziz a Masallacin Juma’a na Tsohuwar Jama’ar Bayero da ke Kano, da misalin ƙarfe 11 na rana inda nan ma ɗumbun jama’a suka haɗu domin shaida ɗaurin auren.

Baya ga haka Hajiya Zulai Babeji, ta shirya taron wunin biki a gidanta da ke unguwar Chiranci layin Takumashi.

Da take miki godiyar ta ga mahalarta taron bikin, Hajiya Zulai Babeji, ta nuna farin cikin ta tare da miƙa godiyar ta ga Allah da ya nuna mata ranar bikin auren ‘yar autar ta wadda ta kasance rana ce ta tarihi a cikin rayuwarta.

Haka nan ta yi godiya ga dukkan jama’ar da suka bayar ga gudunmawar su ta lokaci dukiya da kuma jikin su tun daga farkon shirye shiryen bikin har zuwa kammaluwar sa.

Tare da fatan Allah ya saka wa kowa da alheri, duniya da lahira.

By ukarofi