Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Faruk Sayyadi na ɗaya daga cikin zaƙakurai a masanantar Kannywood; ƙwararre ne a fannin zane-zane da tasirin gani (ɓFɗ). Shi darakta ne, kuma marubucin fim ne kuma jarumi ne a masana’antar Kannywood. A wannan hira ta musamman da wakilinmu Ibrahim Hamisu ya yi da shi a Kano, za ku ji tarihinsa da ma wasu muhimman bayanai.
MANHAJA: Za mu so ka gabatar mana da kanka?
SAYYADI: Da fari dai, sunana Faruk Sayyadi. An haife ni a unguwar Dandago, kusa da ƴar Maishinkafi. Na yi makarantar firamare a Mawgan, sannan na tafi makarantar sakandare ta Kawaji, daga nan na kammala IJMB a CAS (Kwalejin Fasaha da Kimiyya da Karatun Gyara). Bayan haka, na tafi Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), inda na samu digiri a fannin Larabci da Darussan Addinin Musulunci.
Bayan kammala hidimar ƙasa (NYSC) a ƙaramar Hukumar Ibi, Jihar Taraba, na fara harkar fim tare da Ummi PRoduction a Sabon Titin Mandawari. Daga nan na samu aiki a Legas, inda na yi aiki na tsawon shekaru uku, sai dai daga bisani aka rage ma’aikata a lokacin gwamnatin Obasanjo, hakan ya sa na bar aikin. Sai na koma harkar fim a Legas, daga bisani kuma na dawo Kano, inda nake ci gaba da aiki har zuwa yau.
Ya aka yi ka shiga masanaartar fim ta Kannywood?
Da farko, ni mai son kallon finafinai ne. Wannan shi ne ya zaburar da ni shiga harkar fim bayan na kalla wani fim mai suna ‘Hard Target’ tare da ƙanina, Khalil Sayyadi. Bayan wani abu mai ban mamaki ya faru a fim ɗin, sai ya yi min bayani a lokacin yana karatun digiri akan aikin jarida a BUK. Wannan ne ya sa sha’awa ta ƙaru, kuma ya ƙarfafa min gwiwa da in fara karanta littattafai na makaranta.
Na samu shiga Kannywood ne bayan na dawo daga NYSC ba tare da aiki ba. Na kan je wajen abokina, Hon. Ahmad Rufa’i Nasidi, wanda aka fi sani da Baban Malam, wanda a lokacin yana farawa da harkar shirya fina-finai. Suna da wani ɗakin kallon finafinai da ke tsakanin ofishin Darakta Ishaƙ Sidi Ishaƙ da Ummi Production na Darakta Shariff Aminu.
Abin mamaki, ni da Darakta Shariff Aminu mun saba tun muna yara shi yana zuwa sakandare, ni kuma ina firamare, muna tafiya makaranta tare a mota ɗaya. Wannan ne ya sa muka ƙara kusanci. Wata rana ya tambaye ni ko zan iya fitowa a fim. Na ce e. Na fara fitowa a fim mai suna ‘Kaskanci’ tare da Kumurci da Momo a shekarar 2000. Wannan ne ya fara bayyana ni a fina-finan Kannywood. Bayan na dawo daga Legas a 2008, na ci gaba har zuwa yanzu.
A me ka fi ƙwarewa a Kannywood?
Tun kafin na fara firamare, ina zane-zane (art). Wannan ne ya sa da na je Legas, na shiga wata makarantar Indiyawa da ke da reshe a Legas, inda na koya zane-zane da motsi (motion cartoons), rubutun fim, shirya fim, ɗaukar fim, gyaran bidiyo, aikin sauti, da kuma abubuwan da suka shafi shirin kwamfuta da kafafen sadarwa na zamani.
Babban abin da na fi ƙwarewa a kai shi ne zane-zane, hoto mai motsi (motion cartoons), editing, mai kula da tsarin sauri da tasirin gani (ɓFɗ).
Wane fim ka fara yi a matsayin darakta?
Fim na farko da na fara a matsayin darakta shi ne ‘Candy’. Na shirya shi ne a Legas a shekarar 2007, kuma ya lashe lambar yabo a wani bikin fina-finai a Abuja a matsayin ‘Best Animated Film of 2007’.
Finafinai nawa ka yi ko ka jagoranta?
Na jagoranci finafinai guda shida: guda uku manya ne, uku kuma gajeru ne. Sun haɗa da: ‘Candy’, ‘Sandar Arziki’, ‘Balas’, ‘Laifin Wa’, ‘Zing Zong Zombies’, da ‘Zakariyus the Role Model’.
Na kuma yi aikin mataimakin darakta a fim guda uku – ‘Dan Adam’, ‘Princess of Gala’, da ‘Jamila Jammaje’.
Baya ga daraktanci wato bada umurni ko akwai wasu fannoni na fim da kake yi ne?
Eh tabbas! Ina bayar da gudunmawa a duk inda zan iya. Na yi aikin ƙawata wurin ɗaukar fim (set design) a Dan Marayan Zaki’ na Malam Saira; ‘Ashabul Kahfi’ na Malam Saira; ‘Ssai A Lahira’, da ‘ƙasa Ta’ na Yasin Auwal. Na kuma yi aiki a fannin ɓFɗ. Misali, a fim ɗin ‘ɗan Adam’ na Babangida Bangis; ‘Mutum da Aljan’ na Murtala Baharu; ‘ɗan Marayan Zaki’, da ‘As’habul Kahfi’ na Malam Saira, da sauransu.
Na kuma kasance mataimakin darakta a finafinai irin su ‘ɗan Adam’ na Bangis, ‘Princess of Galma’ na Muh’d Galadima, da ‘Jamila Jammaje’ na Nasir B. Muhd.
Na kuma yi rubuce-rubuce (scripts) na finafinai kamar ‘Hauren Mayu’, ‘Sandar Arziki’ da ‘Balas’. A halin yanzu kuma, ina aiki a kan wani rubutu da nake yi da harshen Turanci.
Abin da mutane suka fi sani na da shi, shi ne, rawar da nake taka wa a cikin shirin ‘Daɗin Kowa’ na Arewa24 wanda Adamu Trooper ya jagoranta, inda nake fitowa a matsayin Baban Rasaki ko Mustapha Manager. Kafin hakan, na fito a finafinai kamar ‘Jamilun Jidda’ na Kamal S. Alkali; ‘ɗan Marayan Zaki’ na Malam Saira; ‘As’habul Kahfi’ na Malam Saira; ‘Wani Gari’, ‘Farin Dare’, ‘Kara da Kiyashi’, da “Mai Jego’ duk na Yasin Auwal, da sauransu.
Yanzu haka kuma ina fitowa a cikin ‘Kishiyata’ na Hassan Giggs da ‘Alaƙa’ na Dr. Ali Nuhu, wanda na fara kwanan nan.
