Buɗaɗɗiyar wasiƙa zuwa ga San Turakin Dutse

Daga HARUNA BIRNIWA

Ranka shi daɗe, da fatan wasiƙata za ta riske ka cikin ƙoshin Lafiya.

Dalilin rubuto maka wannan wasiƙa tawa shi ne, Na ga ka ɗauko wani salon rubutu na siyasantar da lamarin ambaliyar ruwa a Jigawa. Duk da yake, ka san cewa wannan iftila’i saukakke ne daga Buwayi gagara misali, Ubangijin da yake gudanar da komai cikin ƙudurarSa da mulkinsa.

Ban san wacce irin riba kake son samu daga wannan jarrabar da aka sauke wa al’ummar Jigawa ba, amma ina da kyakkyawan sanin rubututtukanku ba za su taimaka wa jama’ar wannan jihar ba a halin yanzu. Mu ɗauki misali da qaramar hukumarka ta Birnin Kudu wacce tana ɗaya daga cikin ƙananun hukumomin da ruwa ya yi ɓarna.

Gdaje sun rushe, wanda hakan ya yi sanadiyyar salwantar rayuka da dukiyoyi, shin wanne hovvasa ka yi domin tallafa wa waɗanda wannan iftila’i ya shafa? Ko kana ganin fitowa kafar sada zumunta ka ce gwamnati ba ta iya ba ne kawai gudunmawar da za ka iya ba su a matsayinka na ɗan takarar gwamna kuma wanda kullum bakinsa ke cike da kalamai na nuna tausayin talakawa?

Dattawa na cewa, ‘ta yaro kyau take, ba ta ƙarko’, yanzu kam na fahimta. Mu jam’iyyarmu tana ta ƙoƙarin kai ɗauki a lungu da saƙo na wannan jihar tana daƙile wajajen da ruwa ya ɓulla tare da aike da kayan rage raɗaɗi. kai kuma da ire-irenka kuna zaune kuna jin daɗi saboda kun juya al’amarin dai-dai da yanda za ku yaqi gwamnati da jam’iyya mai mulki da shi.

Haƙiƙa, wannan salon siyasar ba ta dace da matashi mai ilimi kamarka ba. Ka duba ‘yan siyasa irin su Honarabul Abubakar Hassan Fulata da a cikin wannan ƙanƙanin lokacin ya aike wa da ƙananun hukumomin da da yake wakilta da kayan tallafi; kama daga kan fatun buhu da nau’ikan abinci da sauran ababen buƙata na gaugawa.

Har’ilayau, akwai babbar gudunmawar da za ka iya bayarwa a ɓangaren ilimin yara da kake ta ɓolon gwamnati ta kasa fito da wata hanyar da za ta maye gurbi sakamakon ruwa da ya mamaye hanyoyin da za su sada ɗaliban da makarantunsu.

A tawa fahimtar, ya kai ma fi iya gudanar da mulkin Duniya, shin idan ka ɗauki nauyin ilimintar da ɗaliban nan ta hanyar gidajen rediyo da muke da su a faɗin wannan jihar, ba zai fi amfani ba a kan kawar da hankalin gwamnati daga ƙoƙarin da take na daƙile ɓarnar da ruwan yake da lalata hanyoyin zuwa makarantar? Ko kana nufin iya siyasantar da al’amura kaɗai ne wajibi a gare ka?

Ya kai mai girma ɗan takarar gwamna, zan so ka yi duba da yanda gwamnatin wannan jiha take faɗi-tashi domin gyaran hanyoyin da ruwa ya cinye. A ranar 10 ga watan Satumba na wannan shekarar mai girma muƙaddashin gwamnan jiha kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC, Hon.

Umar Namadi ya kai ziyara domin duba aikin hanyar da ta fara daga Jahun zuwa Gujungu tare da ƙara wa ɗan kwangila ƙaimi domin a yi aiki mai kyau kuma cikin sauri, yanda al’umma za su samu damar ci gaba da gudanar da al’amuran rayuwarsu cikin nutsuwa.

Shi dambu idan ya yi yawa, bai cika jin mai ba. A jihar Jigawa babu wata ƙaramar hukuma wacce ba ta fuskanci barazanar ambaliyyar ruwa da rusau ba a wannan shekarar, hakan kuma ya samo asali ne ta yawaitar manya-manyan ruwa da aka samu a jere kuma a ƙasa da wata da biyu.

Sakamakon haka, gidajenmu da ma fi yawa na laka ne sun ɗauki ruwa, kuma sun yi nauyin da katangunsu ba za su iya ɗaukarsu ba. Don haka, babu mamaki don gidaje sun rushe a wannan yanayin.

Abu na ƙarshe, ina ƙalubalantarka a kan ka kawo mana jerin kayayyakin jin wai da ka tura a manyan garuruwa da ruwa ya shanye irin su: Dabi, Una, Baturiya, da sauransu. Sannan ina tsorace maka zama tamkar tsuntsuwar cakwaikwaiwa. Ma’ana, surutunka ya fi aikinka yawa. Domin na fahimci ka fi iya gudanar da al’amura a harshe fiye da yatsun hannunka. Babban Yaya a dage a gyara. Na bar ka lafiya.

Haruna Birniwa, marubuci ne, ɗan siyasa kuma mai sharhi a kan al’amuran mulkin jihar Jigawa.

Ya rubuto daga Birniwa, Jigawa.
07043759956
Imel: [email protected]