Shekaru 62 da samun ‘yancin kan Nijeriya: Nasarorin da ƙalubale

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Gobe Asabar ɗaya ga watan Oktoba Nijeriya ta ke cika shekaru 62 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka. Kuma tun daga shekarar 1960 da turawan Ingila suka miqa ragamar mulkin ƙasar nan ga shugabannin gwamnatin haɗaka ƙarƙashin jagorancin Firaminista Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, ‘yan ƙasa ke shirya bukukuwa don raya wannan rana, da bayyana farin cikin su da jin daɗi na samun ‘yanci da damar tafiyar da dukkan harkokin da suka shafi al’ummar Nijeriya, ba tare da neman amincewar Sarauniya ko Razdan ba.

Turawan mulkin mallaka sun shafe tsawon shekaru suna bautar da ‘yan Afrika, suna kwashe musu albarkatun ƙasa suna gina ƙasashen su, suna sarrafa kuɗaɗen haraji da tattalin arziki yadda suka ga dama bisa umarnin Sarauniya, kuma su ne ke tsara wa jama’a yadda za su rayu ko tafiyar da harkokin su na rayuwa, a wani ɓangaren ma hatta addini da al’ada sai da suka tsara yadda za a gudanar da su.

Sai dai duk da irin satar dukiyar ƙasa da Turawa suka riƙa yi, suna samar da ingantattun hanyoyin mota da na jiragen ƙasa, ko da kuwa domin samun sauƙin fitar da kayan albarkatun ƙasar da suka sace ne zuwa masana’antun ƙasashensu, sun kuma samar da makarantu da asibitoci masu inganci, waɗanda wasun su har yanzu ana cin moriyarsu, wasu kuma an yi musu kwaskwarima ana ci gaba da amfana da su.

‘Yan Nijeriya da dama a lokacin suna da ayyukan da suka dogara da su, da suka shafi kasuwanci, da ƙwadago, sai noma da kiwo, waɗanda suka riƙe iyalai da matasa wajen inganta rayuwarsu. A lokacin duk wanda aka samu yana zaman kashe wando to, shi ya ga dama, saboda akwai damarmaki iri-iri da mutum zai jingina da su.

Idan abin mutum ya waiwayi abubuwan da suka faru a wancan lokacin ne, kafin karɓar ‘yancin kai, duk da kasancewar wasun mu ba su ma zo duniyar ba, amma tarihi ya tabbatar da yadda Turawan mulkin mallaka suka bar ƙasar nan da abubuwan cigaba da suka samar, domin ‘yan qasa waɗanda suka karɓi mulki, su ɗora daga inda suka tsaya. Mutum zai yi takaicin yadda ake samun koma baya da lalacewar al’amura, waɗanda ake xora alhakin su kan rashin samun shugabanci nagari, da rashin kishin ƙasa daga gare mu.

Duk da kasancewar an samu damar da za a ninka irin ci gaban da aka gada daga hannun turawa, sakamakon gano arzikin man fetur da ya yi sanadiyyar kawo wa ƙasar kuɗaɗe masu yawa, amma wancan zargin da aka yi a baya, na rashin shugabanci na gari da rashin kishin ƙasa, ya sa aka riƙa almubazzaranci da dukiyar da take shigowa, da yi wa dokokin ƙasa hawan ƙawara.

Siyasar ƙabilanci da ɓangaranci ta ci gaba da haifar da rabuwar kai a tsakanin ‘yan Nijeriya, aka watsar da harkokin gona, aka koma rayuwar kura tsira da na bakin ki, abin da ya daxa jefa ƙasar cikin wani yanayi na daga ba gidana ba, sai gidan ‘ya’yana. Aka canja salon tafiyar da tsarin shugabanci daga salon mulki irin na Ingila mai Firaminista da Shugaban Gwamnati, zuwa tsarin siyasar ƙasar Amurka mai shugaba guda ɗaya tilo mai cikakken iko.

Waɗannan da wasu dalilai da ba zai yiwu na kawo su duka a nan ba, ko saboda ƙarancin ilimi da shekaru, ko saboda gudun kada rubutun ya gunduri mai karatu. Amma ko shakka babu, duk wani dattijo da ya ke da wayo kan abubuwan da suka kasance a baya, ya dubi yadda rayuwar ƙasar nan ta ke a halin yanzu zai bayyana maka takaici da yadda ƙasar take daɗa samun kanta.

Ko da ya ke ba za a nuna ɗan yatsa kan wani mutum ko ɓangare da za a xora wa alhakin lalacewar ƙasar nan ba, saboda yadda al’amura suka riƙa warware wa a hankali, har suka kawo halin da muke ciki na yanzu. Amma a duk rana irin ta yau, a kan samu wasu ‘yan ƙasa da ke ganin babu wani abin yi wa buki, don kuwa ‘yan ƙasa ba su ci moriyar ‘yancin da aka samu ba.

Tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da kwan gaba kwan baya, yau a ce an samu bunƙasa da nasara, wacce akasari a rubuce ne ba a zahirin rayuwar ‘yan ƙasa ba, gobe kuma a sake yin warwas, xa kwance uwa kwance. Talauci na cigaba da galabaitar da ‘yan Nijeriya, yayin da rashin ayyukan yi a tsakanin matasa ke daɗa jefa ƙasar cikin ƙalubalen tsaro. Shi ya sa idan kana hira da dattijai za ka ji ana tuna maka da karin maganar nan ta Bahaushe da ke cewa, kowa ya tuna bara bai ji daɗin bana ba.

Ko da ya ke kuma ba adalci ba ne a riqa auna bara da bana, musamman a yanayin zamantakewa ta Nijeriya, saboda canjin zamani da bunƙasar da ƙasar ta yi. An samu ƙaruwar yawan al’umma daga kimanin mutane miliyan 46 a lokacin samun ‘yancin kai a 1960, zuwa mutane kimanin mutane fiye da miliyan 200. An samu ƙaruwar marasa ayyukan yi, da yawaitar yaran da ke yawo a titi babu karatu, da ƙaruwar ƙungiyoyin ‘yan bindiga, masu ta da ƙayar baya da masu satar dukiya da mutane, don neman kuɗin fansa.

Duk da kasancewar Nijeriya da ake yi wa laƙabi da Giwar Afrika, ɗaya daga cikin manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin soja da damar faɗa a ji a Majalisar Ɗinkin Duniya, da yadda ƙasar ke da yawan ƙwararrun likitoci, ma’aikatan lafiya da sauran ƙwararru da a kowacce rana suke neman hanyar barin ƙasar, saboda samun kyakkyawar kulawa a wasu ƙasashen duniya, a yayin da harkokin lafiya da ilimi ke ƙara taɓarɓarewa, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnatoci ke cewa suna yi wajen daidaita al’amura.

Rayuwar ma’aikacin gwamnati ta tashi daga abin sha’awa zuwa abin takaici, saboda rashin ingancin albashi da kyautatuwar yanayin gudanar da aiki, inda har wasu ma ke gwammatar kasuwanci da ƙwadago, don ciyar da iyalinsu, a maimakon jiran albashin da bai wuce cikin cokali ba, wanda da ƙyar ke yi wa ƙaramin ma’aikaci sati guda.

Ba na goyon bayan masu ra’ayin bai kamata a yi wani murna don samun ‘yancin kai ba, ina ganin ko babu komai abin farin ciki ne, kasancewar mu ne muke mulkar kan mu, kuma har yanzu Nijeriya ta ci gaba da zama dunƙulalliyar ƙasa, duk kuwa da yunƙurin da wasu suke yi na ɓallewa ko kafa ƙasar kansu, domin tunanin za su fi kafa tsarin da zai samar musu da cigaba. Tsarin dimukraɗiyya da ƙasar nan ta samu kanta a ciki, ya ƙara kusantar da talakawa kusa da gwamnati, jama’a da dama sun amfana da mulkin siyasa.

Wasu tsare-tsare da gwamnati ke ƙirƙirowa lokaci-lokaci yana bai wa wasu ‘yan Nijeriya damar cin moriyar wani abu daga arzikin ƙasa, musamman a ƙarƙashin gwamnati mai ci. Tsare tsaren yaƙi da talauci da aka ɓullo da su sun taimakawa mutane da dama samun madogara da inganta sana’o’in su na neman abinci. A lokacin da a wani ɓangaren kuma ake zargin ‘yan siyasa da raba kan ‘yan ƙasa, haddasa matsalolin tsaro, da satar dukiyar ƙasa, da kuma karya tattalin arziki, da ya jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya cikin wani mawuyacin hali.

Lallai ne, a maimakon mu ci gaba da kokawa da bayyana takaici, da la’antar shugabanni, mu riqa amfani da wannan lokaci wajen duba hanyoyin da za mu gyara gaba, ta hanyar amfani da duk wata dama da ‘yancin kai ya ba mu, mu mutunta kan mu a matsayin mu na ‘yan Nijeriya, kuma mu mutunta ƙasarmu a matsayin ta na uwa, kuma gatan mu a duniya. Wacce in babu ita, babu wata ƙasa da za ta karve mu a matsayin ’ya’yanta, sai dai mu yi ta galantoyi a matsayin ‘yan gudun Hijira.

Tsohon Firaministan Nijeriya na farko, kuma wanda daga kansa babu wani, Sa Abubakar Tafawa Ɓalewa, cikin jawabin sa na bayan ‘yancin kai, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya mu yi amfani da wannan dama ta ‘yancin kai, mu ga mun tafiyar da al’amarin ƙasarmu da kyau. Kowanne ɗan Nijeriya, komai matsayinsa ko ɓangarensa, ko wanne addini ya ke bi, ya ba da gudunmawa ga cigaban ƙasar nan.

Wannan shi ne muhimmin saƙon da har yanzu ake isar wa ga ‘yan Nijeriya. Idan ba mu sanya kishin ƙasa da kishin al’ummarmu ba, son zuciya da mugunta ne zai halaka mu kuma ya cigaba da lalata ƙasarmu.

A rana mai kamar ta yau, ina kira ga ‘yan uwana matasa, a maimakon ɗauke ɗauken hotuna da sanya tufafi masu launin tutar Nijeriya, ana ɗorawa a zaurukan sada zumunta, ya kamata mu yi amfani da lokacin wajen tunatar da kawunan mu, nauyin da ke kan mu na nuna kishin ƙasa da jajircewa, don ganin Nijeriya ta samu sauyi mai ma’ana da zai kawo cigaba mai ɗore, a duk wata dama da suka samu. A maimakon neman damar da su ma za su wawuri arzikin ƙasa su kuɗance lokaci ɗaya, su da iyalansu.

Allah ya kawo mana sauyi a Nijeriya da cigaba mai ma’ana da kowa zai amfana da shi a matsayin mu na ‘yan ƙasa.